Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya tafi Bauchi tare da tawagar da Shugaban Ƙasa ya naɗa don halartar jana’izar babban malami, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, wanda Allah ya yi wa rasuwa jiya.
Tawagar ta ƙunshi manyan ƙusoshin gwamnati da suka haɗa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu, da Sanata Abdul’aziz Yari, Sanata Shehu Buba Umar, da ministoci irin su Sanata Abubakar Kyari (Aikin Gona), Jakada Yusuf Maitama Tuggar (Harkokin Waje), Farfesa Muhammad Ali Pate (Kiwon Lafiya da Walwalar Jama’a), Alhaji Mohammed Idris (Yaɗa Labarai), da Hon. Uba Maigari Ahmadu (Cigaban Yankuna).
Akwai kuma ƙarin manyan jami’an gwamnati irin su Dakta Aliyu Modibbo Umar, Malam Abdul’aziz Abdulaziz da tsohon Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa, Barr. Abdullahi Mukhtar.







