• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, May 13, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Kotun KAROTA ta hukunta mutum 87 da suka karya dokar zirga-zirga a Kano

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
October 17, 2025
in Labarai
A A
0
Kotun KAROTA ta hukunta mutum 87 da suka karya dokar zirga-zirga a Kano
'Yan KAROTA a bakin aiki

'Yan KAROTA a bakin aiki

Hukumar Kula da Hanyoyi da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ta samu nasarar hukunta mutane 87 da suka karya dokokin zirga-zirga a birnin Kano, ta hanyar Kotun Tafi-da-Gidan-ka da aka kafa domin rage yawaitar take dokokin hanya a cikin birnin.

Bayanin yana ƙunshe cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na Hukumar KAROTA, Yusuf Ibrahim Sharaɗa, ya fitar a ranar Juma’a, a Kano.

Ya ce a cikin kwanaki biyu da suka gabata, kotunan da ke gudanar da zama a wurare daban-daban na cikin birnin sun saurari shari’u tare da yanke hukunci kan masu laifin da aka kama suna karya dokokin zirga-zirga, musamman masu wucewa lokacin da alamar hasken ja ya tsarar da su a mahaɗar da danja ke bada hannu.

Sai kuma waɗanda suka aikata wasu laifuka da suka shafi keta dokokin hanya.

Ɗaya daga cikin kotunan da ta gudanar da zama a kusa da Magwan Junction a kan State Road, ta hukunta mutane 41 ƙarƙashin jagorancin Alƙalin Babbar Kotu, Halima Wali.

Haka kuma wani zama da aka gudanar a kan BUK Road kusa da Ƙofar Famfo Junction, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Hauwa Abba, ta hukunta mutane 46 da suka haɗa da direbobi da masu tuƙin A Daidaita Sahu, saboda irin wannan laifi.

Da yake jawabi kan wannan cigaba, Manajan Darakta na KAROTA, Faisal Mahmud Kabir, ya jaddada ƙudirin hukumar na ci gaba da gudanar da zaman kotunan mai tafiya a sassa daban-daban na birnin Kano, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin rage take dokokin hanya da tabbatar da bin doka a tituna.

Ya bayyana cewa wannan mataki ba don tsoratar da direbobi ko masu tuƙa

A Daidaita Sahu ba ne, sai dai domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da tabbatar da tsari, bisa manufofin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya kuma yaba da ƙwazon alƙalai, jami’an tsaro da jami’an KAROTA da ke aiki tare wajen aiwatar da wannan aiki, inda ya bayyana cewa jajircewa da kishin aiki ne suka taimaka wajen samun wannan nasara.

Tags: Jihar KanoKAROTA
Previous Post

Jos 2025 NUGA: Atiku ya zama uban gasa

Next Post

Gwamnati ta yi kira a riƙa amfani da ilimin hulɗa da jama’a wajen ƙaryata zargin ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Nijeriya

Related Posts

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500
Labarai

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

May 13, 2026
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Next Post
Gwamnati ta yi kira a riƙa amfani da ilimin hulɗa da jama’a wajen ƙaryata zargin ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Nijeriya

Gwamnati ta yi kira a riƙa amfani da ilimin hulɗa da jama’a wajen ƙaryata zargin ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Nijeriya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!