Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana ƙudirin gwamnatin sa na ci gaba da gina ƙasa mai haɗin kai da cigaba ta hanyar tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar da ƙasa baki ɗaya.
Gwamnan ya yi wannan bayani ne a yayin wani taro da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida ta jiha ta shirya a yau.
An shirya taron ne a ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Yaɗa Labarai, Ibrahim Abdullahi Wayya, a Kano, a wani ɓangare na bikin ranar samun ‘yancin Nijeriya shekara 65 daga Turawan mulkin mallaka.
Za a gudanar da taron ne a jibi Laraba, 1 ga Oktoba.
Gwamnan, wanda Shugaban Ma’aikata na Fadar Gwamnati, Dakta Sulaiman Wali Sani, ya wakilta, ya ce tsaro shi ne ginshiƙin duk wani cigaba, domin babu abin da za a iya cimma wa ba tare da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba.
“Ya kamata kowa ya ɗauki tsaron ƙasa a matsayin haƙƙin kowa da kowa, ba wai na gwamnati kawai ba,” inji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnatin sa na aiki tare da hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya da na al’umma domin ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai.
Ya ce shirye-shiryen ƙarfafa wa matasa gwiwa ta hanyar koyar da su sana’o’i da haɓaka ilimi yana daga cikin muhimman matakan da ake ɗauka wajen magance tushen matsalolin tsaro.
“Ta hanyar waɗannan shirye-shirye, muna rage dalilan da ke jawo rashin tsaro tare da samar da damarmaki ga matasan mu, domin su taka muhimmiyar rawa a cikin al’umma,” inji shi.
Haka kuma ya yaba wa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida saboda shirya wannan lacca da kuma fito da muhimmancin shirin ‘Save Corridor’ na daƙile shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya a jihar.
Yusuf ya ƙara da cewa wannan shiri, wanda ya mayar da hankali kan gyara da sake shigar da waɗanda suka tuba cikin al’umma, ya dace da manufar gwamnatin sa ta inganta sulhu, haɗin kai da cigaban jama’a.
A nasa jawabin, Kwamishinan Yaɗa Labarai ta Jihar Kano, Ibrahim Wayya, ya gode wa mahalarta taron tare da shaida masu cewa an shirya shi ne domin zaburar da matasa muhimmacin ƙaunar jihar su da kishin ƙasa.
Ya ce taron wata hanya ce ta jan matasa a jika da kuma nuna muhimmacin riƙo da al’adun yankin da mutum ya fito.







