Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Ƙaramin Ministan Gidaje da Cigaban Birane, Alhaji Abdullahi Tijjani Gwarzo, murnar cikar sa shekaru 65.
A sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya yaba da kishin ƙasa da kuma jajircewar Alhaji Gwarzo a harkokin siyasa, musamman a ɓangaren manufofin cigaban al’umma.
Shugaban ya ce ƙaunar da jama’a ke nuna wa Gwarzo ya samo asali ne daga siyasar gaskiya da riƙon amana da ya yi, tun daga lokacin da ya yi shugabancin ƙaramar hukuma har zuwa lokacin da ya zama mataimakin gwamnan Jihar Kano tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011.
Ya ƙara da cewa a shekarar 2011, lokacin da Gwarzo ya tsaya takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN), ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa dangantakar siyasa wadda daga bisani ta samar da APC a cikin 2013.
Tinubu ya yi masa fatan alheri da kuma ƙarfafa masa gwiwa kan ya ci gaba da sadaukarwar sa wajen bautar ƙasa.







