• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Manyan hanyoyi huɗu da gwamnatin Tinubu ke ginawa za su sauya tattalin arzikin Nijeriya – Idris

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
July 1, 2026
in Labarai
A A
0
Manyan hanyoyi huɗu da gwamnatin Tinubu ke ginawa za su sauya tattalin arzikin Nijeriya – Idris
Jami'an gwamnati da 'yan kwangila a lokacin ƙaddamar da gadar ƙasa mai tsawon mita 600 (Underpass) da ke Zagayen Akwanga a ranar Laraba, 1 ga Yuli, 2026, a garin Akwanga, Jihar Nasarawa. Hoto daga: Khalid Ahmed/FMINO.

Jami'an gwamnati da 'yan kwangila a lokacin ƙaddamar da gadar ƙasa mai tsawon mita 600 (Underpass) da ke Zagayen Akwanga a ranar Laraba, 1 ga Yuli, 2026, a garin Akwanga, Jihar Nasarawa. Hoto daga: Khalid Ahmed/FMINO.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa manyan ayyukan gina hanyoyi guda huɗu na Shugaba Bola Ahmed Tinubu zuba jari ne masu matuƙar muhimmanci da za su sauya tattalin arzikin Nijeriya, su ƙara haɗin kan al’umma tare da samar da ɗorewar wadata ga miliyoyin jama’ar ƙasa.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da aikin gina Sashe na Farko (Akwanga zuwa Jos mai tsawon kilomita 125) na babbar hanyar Akwanga–Jos–Bauchi–Gombe, a garin Akwanga na Jihar Nasarawa a ranar Laraba, Idris ya ce wannan wani babban cigaba ne ƙarƙashin Ajandar Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda) ta Shugaba Tinubu.

Ya ce, “Shugaba Tinubu ba hanyoyi kawai yake ginawa ba; yana gina hanyoyin tattalin arziki da za su sauƙaƙa kasuwanci, samar da ayyukan yi, haɗa al’ummomi da kuma bunƙasa cigaban ƙasa wanda kowa zai amfana da shi. Wannan shi ne ainihin aiwatar da Ajandar Sabuwar Fata.”

Ministan ya bayyana cewa babbar hanyar Akwanga–Jos–Bauchi–Gombe tana daga cikin manyan ayyukan hanyoyi guda huɗu na Shugaba Tinubu, waɗanda suka haɗa da Babbar Hanyar Bakin Teku ta Legas–Kalaba, da Babbar Hanyar Sakkwato zuwa Badagiri, da kuma Hanyar da ta Ratsa Sahara, waɗanda aka tsara domin bunƙasa kasuwanci, inganta haɗin kai tsakanin sassan ƙasa da kuma buɗe sababbin damarmakin tattalin arzikin Nijeriya.

Har ila yau, Idris ya jero wasu muhimman nasarorin gwamnatin Tinubu, ciki har da sauye-sauyen tattalin arziki da suka ƙara wa masu zuba jari ƙwarin gwiwa, faɗaɗa damar samun ilimi mai zurfi ta hannun Asusun Lamunin Ilimin Nijeriya (NELFUND), ƙarfafa masana’antun cikin gida da kuma inganta hasashen tattalin arzikin ƙasar nan.

Da yake ba da misali da wasan ƙwallon ƙafa, Ministan ya buƙaci ‘yan Nijeriya su ci gaba da bai wa gwamnati goyon baya, yana faɗin, “Idan ƙungiyar ku tana samun nasara, ba za ku maye gurbin ta da tawagar masu jiran gado ba. Nijeriya ta cancanci mafi kyawun shugabanci, kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana ba da irin wannan jagorancin domin gina ƙasa mai ƙarfi da wadata.”

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Ministan ya yi watsi da zargin cewa Gwamnatin Tarayya tana nuna wariya wajen raba ayyukan gine-ginen more rayuwa tsakanin yankuna. Ya jaddada cewa ayyukan hanyoyi na Shugaba Tinubu sun bazu a sassa daban-daban na ƙasar nan, abin da ke nuna jajircewar gwamnatin wajen tabbatar da cigaba mai adalci da ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

A madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce wannan aiki wata alama ce ta ƙudirin gwamnati na amfani da gine-ginen more rayuwa a matsayin ginshiƙin sauya tattalin arzikin Nijeriya.

Tun da farko, sai da Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya ƙaddamar da aikin gina sashen kilomita 125 na hanyar Akwanga–Jos, wadda ke cikin babbar hanyar kilomita 700 daga Akwanga–Jos–Bauchi–Gombe–Yobe–Maiduguri.

Ya ce za a aiwatar da aikin a matakai daban-daban domin inganta sufuri, bunƙasa harkokin tattalin arziki da kuma hanzarta cigaba a yankunan Arewa-ta-Tsakiya da Arewa maso Gabas.

Umahi ya bayyana cewa a halin yanzu yankin Arewa-ta-Tsakiya yana da manyan ayyukan hanyoyin Gwamnatin Tarayya guda 35, da kuma ayyukan gaggawa guda 61.

Ya kuma buƙaci kamfanonin da ke gudanar da ayyukan su bai wa matasan yankunan aikin yi tare da ba su horon ƙwarewa, sannan ya yi kira ga al’ummomin da abin ya shafa da su kare waɗannan muhimman kayayyakin more rayuwa.

Manyan baƙi da suka halarci bikin sun haɗa da Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu; Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule; Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya; Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang; Ministar Harkokin Mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim; Ƙaramin Ministan Ayyuka, Barrista Bello M. Goronyo; mambobin Majalisar Dokoki ta Tarayya, sarakunan gargajiya da sauran manyan jami’an gwamnati.

—

HOTO:
Hagu zuwa dama: Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa, Dakta Emmanuel Akabe; Ministar Harkokin Mata, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim; Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris; Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule; wakilin kamfanin BAUHAUS Global Investment Nigeria Ltd.; wakilin Shugaban Ƙasa kuma Shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, a lokacin ƙaddamar da gadar ƙasa mai tsawon mita 600 (Underpass) da ke Zagayen Akwanga a ranar Laraba, 1 ga Yuli, 2026, a garin Akwanga, Jihar Nasarawa. Hoto daga: Khalid Ahmed/FMINO.

Previous Post

CBN ba da wasa yake ba: Jerin sunayen ƙananan bankuna 46 da aka soke wa lasisi saboda rashin ɗaukar tsarin hadahadar kuɗi da muhimmanci

Next Post

Sojojin mu sun kashe ’yan ta’adda 1,597, sun ceto mutane 1,516 – Hedikwatar Tsaro

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Sojojin mu sun kashe ’yan ta’adda 1,597, sun ceto mutane 1,516 – Hedikwatar Tsaro

Sojojin mu sun kashe ’yan ta’adda 1,597, sun ceto mutane 1,516 - Hedikwatar Tsaro

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!