• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Wani mutum ya arce yayin da ’yan sanda suka kama matar sa da agolar sa kan damfarar soyayya ta naira miliyan 18

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
June 4, 2026
in Tsaro
A A
0
Wani mutum ya arce yayin da ’yan sanda suka kama matar sa da agolar sa kan damfarar soyayya ta naira miliyan 18
Diana Urowhe (a hagu) tare da ’yar ta, Rokibat Oluwasheyi Imoru, bayan an kama su

Diana Urowhe (a hagu) tare da ’yar ta, Rokibat Oluwasheyi Imoru, bayan an kama su

Cibiyar Yaƙi da Laifukan Yanar Gizo ta Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya (NCCC) ta ce tana gudanar da bincike kan wani lamari da ya shafi damfara ta hanyar amfani da kwamfuta, satar bayanan sirri da kuma halasta kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya, wanda ya haɗa da wani mutum, matar sa da kuma agolar sa.

Ta ce binciken ya biyo bayan wani rahoton sirri da ta samu daga Hukumar Leƙen Asirin Kuɗi ta Nijeriya (NFIU).

Muƙaddashin Jami’in Hulɗa da Jama’a na NPF-NCCC da ke Abuja, DSP Unwana Imah, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa binciken farko ya nuna cewa ana zargin wani Emmanuel Amanfo, mazaunin Jihar Legas wanda a halin yanzu ya gudu, da haɗa baki da agolar sa mai shekaru 22, Rokibat Oluwasheyi Imoru, wajen buɗe da kuma sarrafa asusun banki da dama domin gudanar da ayyukan damfara. Ɗaya daga cikin waɗanda suka yi wa damfarar ita ce wata mazauniyar ƙasar Malta (an ɓoye sunan ta).

Ƙarin bincike ya nuna cewa ana tura kuɗaɗe ta hannun kamfanonin tura kuɗi da kuma ta hanyar ajiya kai-tsaye zuwa wasu asusun banki daban-daban a Nijeriya, waɗanda duk mallakin Rokibat Imoru ne.

Bayan karɓar kuɗaɗen, sai a mayar da su zuwa wani asusun Ecobank mallakin mahaifiyar ta mai shekaru 39, Diana Urowhe, inda ake zargin an kashe kuɗaɗen da aka samu.

Imah ya ce bayan gudanar da binciken fasaha kan yawon waɗanda ake zargin a intanet, sai aka kama matar da ’yar ta saboda rawar da suka taka a wata damfarar soyayya ta intanet.

Ya ce: “Ana ci gaba da ƙoƙarin cafke Emmanuel Amanfo, wanda ya tsere. Shi ne mijin Urowhe Diana kuma uban ga Rokibat Oluwasheyi Imoru wadda bai haifa ba.”

Ya ƙara da cewa: “Har yanzu bincike na ci gaba da gudana kan lamarin, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala binciken.”

Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce: “Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, IGP Olatunji Rilwan Disu, psc(+), NPM, tana ci gaba da jajircewa wajen kare kayayyakin fasahar dijital na Nijeriya da kuma tabbatar da tsaron sararin yanar gizon ƙasar.

“A ci gaba da wannan ƙoƙari, Daraktan NPF-NCCC yana kira ga jama’a da su riƙa kai rahoton duk wasu ayyukan da ake zargin laifukan yanar gizo ne ta hanyar shafin mu na hukuma na kai rahoto ko kuma ta adireshin imel ɗin mu: nationalcybercrimecenter@nccc.gov.ng.”

Tags: 'yan sandabincikedamfaraDiana UrowheIGP Olatunji Rilwan DisuNCCCRokibat Oluwasheyi Imoru
Previous Post

Sojoji sun kuɓutar da wasu da aka sace a Kogi, sun ƙara zafafa farautar ’yan ta’adda

Next Post

Gwamnatin Tinubu ta sha alwashin ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Oyo da Borno.

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Gwamnatin Tinubu ta sha alwashin ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Oyo da Borno.

Gwamnatin Tinubu ta sha alwashin ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Oyo da Borno.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!