• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Cardoso ya yi fatali da masu kirayen CBN ya koma tsohon tsarin bayar da tallafin lamuni

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
May 29, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Cardoso ya yi fatali da masu kirayen CBN ya koma tsohon tsarin bayar da tallafin lamuni
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya kare matakin da bankin ya ɗauka na komawa tsarin gudanar da manufofin kuɗi na ƙeƙe-da-ƙeƙe, tare da gargaɗin cewa sake komawa tsohon tsarin shiga tsakani ta hanyar bada lamunin tallafi ga ƙanana da matsakaitan masana’antu, a baya ya janyo matsaloli ga ma’aunin kuɗaɗen CBN, tare da rage ingancin manufofin kuɗi.

Cardoso ya bayyana hakan ne yayin zaman buɗe taron bitar Kwamitin Manufofin Kuɗi (MPC) da aka gudanar ranar 21 ga Mayu, 2026, kamar yadda wata sanarwa da CBN ya fitar ranar Lahadi ta bayyana.

Sanarwar ta ce Cardoso ya sake jaddada ƙudurin bankin na bin tsarin manufofin kuɗi na gargajiya, gaskiya da kuma yanke shawara bisa hujjoji da bayanai, yana mai bayyana cewa sauye-sauyen da ake aiwatarwa suna da muhimmanci wajen dawo da ƙwarin gwiwa ga tattalin arzikin Nijeriya da kuma ƙarfafa daidaiton tattalin arziki.

Daga cikin tallafin lamunin gaggawa da CBN ya riƙa bayarwa kafin wannan gwamnati, akwai har da shirin bada lamuni ga manoma da aka fi sani da ‘anchor borrowers’, wanda biyan kuɗin ya zama alaƙaƙai daga baya.

Taron bitar mai taken, “Ƙarfafa Ingancin Manufofin Kuɗi Domin Samun Ɗorewar Daidaiton Tattalin Arziki”, ya haɗa mambobin Kwamitin Manufofin Kuɗi (MPC), Mataimakan Gwamnan CBN, daraktoci da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna hanyoyin inganta tasirin manufofin kuɗi a cikin yanayin tattalin arzikin gida da na duniya da ke ci gaba da sauyawa.

Cardoso ya waiwayi tarihin manufofin kuɗi na baya-bayan nan a Nijeriya tare da bayyana ƙalubalen da bankin ya tarar lokacin da gwamnati ta yanzu ta hau mulki. Ya ce daga cikin matsalolin akwai raunin ‘yancin cin gashin kai ga CBN, raguwar amincewa da manufofin sa da kuma dogaro da hanyoyin da ba na gargajiya ba wajen tafiyar da manufofin kuɗi.

“Ya bayyana cewa waɗannan ƙalubalen sun rikita bambanci tsakanin ayyukan gwamnati da na manufofin kuɗi, sun rage gaskiya da bayyana bayanai, tare da taƙaitai tasirin manufofin da ake aiwatarwa. Haka kuma ya lura cewa kasuwar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje ba ta ta aiki yadda ya kamata, yayin da rashin daidaituwar haɗin gwiwa tsakanin manufofin gwamnati da na kuɗi ya ƙara taƙaita sakamakon tattalin arziki.”

CBN ya ce waɗannan matsalolin tsarin sun taimaka wajen hauhawar farashi, rikice-rikicen farashin canjin kuɗi da kuma raguwar amincewar masu zuba jari da jama’a.
Sai dai sanarwar ta ce sauye-sauyen da shugabancin yanzu ya kawo sun fara sauya wannan yanayi.

Ya bayyana cewa bankin ya dawo da tsarin gudanar da manufofin kuɗi na gargajiya a ƙarƙashin tsarin MPC na yanzu, inda aka sake mayar da hankali kan amfani da tsarin gamegari da kuma amfani da ƙimar kuɗin ruwa na MPR a matsayin babbar hanyar isar da saƙon manufofi.

Sanarwar ta ƙara da cewa inganta tsarin sarrafa kuɗaɗen shiga da fita, bayar da hasashen manufofi da kuma sadarwa kan manufofin sun ƙara gaskiya tare da taimakawa wajen daidaita hasashen jama’a, ‘yan kasuwa da masu zuba jari.

“A sakamakon haka, sai Cardoso ya ce duk da cewa har yanzu ba a kakkaɓe hauhawar farashi baki ɗaya ba, amma dai ya fara raguwa, yayin da daidaiton farashin canjin kuɗi ya inganta.

Previous Post

Cika shekara uku a mulki: Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki sun fara haifar da ɗa mai ido

Next Post

Karo na farko tun 1999: Gwamna Uba Sani ya ziyarci alhazan Kaduna, ya ba kowannen su riyal 300

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Karo na farko tun 1999: Gwamna Uba Sani ya ziyarci alhazan Kaduna, ya ba kowannen su riyal 300

Karo na farko tun 1999: Gwamna Uba Sani ya ziyarci alhazan Kaduna, ya ba kowannen su riyal 300

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!