Wata mai neman tikitin takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar ADC mai wakiltar Mazaɓar Tarayya ta Chikun/Kajuru a Jihar Kaduna, Malama Hawwah Abdullahi Gambo, ta shigar da ƙorafi gaban Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen jam’iyyar dangane da yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani a ranar Litinin.
A cikin takardar ƙorafin mai kwanan wata 27 ga Mayu, 2026, wadda ta aika wa Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa tare da aika kwafe ga Daraktan Harkokin Siyasa, da Shugabar Mata ta Ƙasa da kuma Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓe na jam’iyyar, Hawwah ta bayyana cewa ita kaɗai ce mace cikin mutum huɗu da suka nemi takarar kujerar, amma an cire sunan ta da gangan daga jerin ‘yan takara. Ta ce an kuma gaya wa magoya bayan ta cewa wai “babu wata mace cikin masu neman takarar,” ko kuma cewa ta janye daga takarar ko kuma ba ta tsallake tantancewa ba.
A cewar ta, zaɓen fidda gwani na ADC, wanda aka ɗage sau uku kafin daga bisani a gudanar da shi a ranar 25 ga Mayu, 2026, ya kasance ne kawai a rubuce ba a aikace ba.
Ta ce: “Da farko, an samu jinkiri wajen isar da kayan zaɓe. Mutane sun jira tun daga ƙarfe 8:00 na safe har zuwa ƙarfe 4:00 na yamma kafin kayan su iso cibiyoyi daban-daban sannan a rarraba su zuwa gundumomi.”
Ta ƙara da cewa an sauya wuraren gudanar da zaɓe a wasu gundumomi na Ƙaramar Hukumar Chikun ba tare da wani dalili, sanarwa ko cikakken bayani kan inda za a gudanar da zaɓen ba.
Ta ce: “Mutane sun je wuraren da aka nuna musu kuma suka jira na dogon lokaci, alhali kuwa ana gudanar da zaɓen a wasu wurare da ba a bayyana ba.
“A Ƙaramar Hukumar Kajuru inda aka samu wani abu mai kama da zaɓe, an sayi ƙuri’u a fili, an tsoratar da masu kaɗa ƙuri’a, an muzguna wa masu zaɓe da kuma sauran ayyukan maguɗi.
“A taƙaice, babu wani sahihin zaɓe da aka gudanar a Mazaɓar Tarayya ta Chikun/Kajuru, musamman ma na kujerar Majalisar Wakilai. Abin da ya faru wata hanya ce ta maguɗi da aka aiwatar da ita tare da take muradin jama’a da ‘yancin su na zaɓe.
“An gaya wa magoya baya na a Ƙaramar Hukumar Chikun da suka samu damar gano cibiyoyin da ake gudanar da zaɓen fidda gwanin cewa wai na janye daga takara, ko kuma ban tsallake tantancewa ba, ko ma cewa ni ba ‘yar takara ba ce kwata-kwata.
“Ni, Hawwah Abdullahi Gambo, ina ƙalubalantar sakamakon zaɓen kujerar Majalisar Wakilai ta Mazaɓar Tarayya ta Chikun/Kajuru.
“Ina kira ga wannan kotu mai daraja da ta gudanar da cikakken bincike kan abin da ya faru a ranar Litinin, 25 ga Mayu, 2026, a zaɓen Mazaɓar Tarayya ta Chikun/Kajuru, musamman a Ƙaramar Hukumar Chikun.
“Ina kira ga wannan kotu mai daraja da ta gano gaskiya tare da tabbatar da bin ƙa’ida da kuma mutunta ra’ayin jama’a.”
Hawwah Gambo ta gabatar da sunayen shaidu 11 a cikin ƙorafin nata, ciki har da ita kan ta, tare da roƙon kotun da ta gudanar da cikakken bincike kan abubuwan da suka faru domin tabbatar da an yi mata da kuma al’ummar mazaɓar adalci.
Ta jaddada cewa ADC “jam’iyya ce da aka gina bisa ƙa’idodin haɗa mata da maza cikin harkokin siyasa, daidaiton dama da kuma adalci,” tana mai cewa, “Waɗannan muhimman ƙimomi ne da ya kamata a kiyaye idan ADC na son ci gaba da ɗorewa a nan gaba.”
Ya zuwa yanzu dai jam’iyyar ADC ba ta fitar da wani bayani ba kan al’amarin.







