• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Saƙon Sallah ga ’yan Nijeriya: Ku yi wa ƙasa addu’ar zaman lafiya, kwanciyar hankali, da cigaba – Minista Idris

ALI KANO by ALI KANO
May 27, 2026
in Labarai
A A
0
Ba da yawu na Sa’idu Enagi ya yi rubutu kan siyasar Neja ba, kuma na dakatar da shi – Ministan Yaɗa Labarai
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da yi wa ƙasar nan addu’ar samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, da cigaba a daidai wannan lokaci da suke shagulgulan Babbar Sallah.

Ministan ya yi kiran ne a ranar wannan Larabar cikin saƙon sa na taya ‘yan Nijeriya murnar shagulgulan Sallah.

Idris ya ce: “A madadin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayya, ina miƙa gaisuwar taya murna ga dukkan al’ummar Musulmi a Nijeriya da ma faɗin duniya baki ɗaya a wannan lokaci na Eid al-Adha.

“Wannan biki mai alfarma yana tunatar da mu kyawawan darussa marasa gushewa na imani, sadaukarwa, biyayya, tausayi, da miƙa wuya ga nufin Allah Maɗaukakin Sarki, kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) ya nuna.

“Wannan lokaci ne da ke kira a gare mu da mu yi tunani, mu ƙarfafa haɗin kai, haƙuri da juna, da sabunta ƙudirin mu na rungumar kyawawan ɗabi’u da ke haɗa mu a matsayin ƙasa ɗaya.

“Yayin da ’yan Nijeriya suke bikin tare da iyalan su da masoyan su, ina kira ga jama’a da su ci gaba da yi wa ƙasar mu addu’ar samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, da cigaba.”

Ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tana ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da manufofin Ƙudirin Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda) tare da gina Nijeriya mafi tsaro da wadata, wadda ta rungumi kowa.

Haka kuma, ya shawarci jama’a da su yi amfani da wannan lokaci wajen nuna ƙauna da tallafi ga marasa galihu, inganta zaman lafiya da zaman tare cikin fahimtar juna, da ƙarfafa ruhin haɗin kan ƙasa ba tare da la’akari da bambancin ƙabila, addini, ko ra’ayin siyasa ba.

Ya kuma yi addu’a da cewa: “Allah Ya sa albarkar wannan bikin Sallah ta kawo zaman lafiya, farin ciki, da yalwar arziki ga kowane gida, kuma Allah Ya karɓi addu’o’in mu da hadayar mu. Barka da Sallah.”

Tags: addu'aBabbar SallahEid al-AdhaMohammed Idris
Previous Post

Ziyarar Aminci da Sadaukarwa: Tsokaci kan Gaisuwar Sallah da Matawalle Ya Kai wa Shugaba Tinubu a Legas

Next Post

‘Yar takarar ADC ta Majalisar Wakilai a Kaduna ta kai ƙara kan hana ta shiga zaɓen fidda gwani

Related Posts

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
Next Post
‘Yar takarar ADC ta Majalisar Wakilai a Kaduna ta kai ƙara kan hana ta shiga zaɓen fidda gwani

'Yar takarar ADC ta Majalisar Wakilai a Kaduna ta kai ƙara kan hana ta shiga zaɓen fidda gwani

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!