• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Kotu ta ba El-Rufai beli da tsauraran sharuɗɗa

ALI KANO by ALI KANO
May 18, 2026
in Labarai
A A
0
Mun samu damar sauraron kiran wayar Ribaɗu, mun ji yadda ya ba da umurnin a kama ni, inji El-Rufai
Malam Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Jihar Kaduna

Malam Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Jihar Kaduna

Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, beli bisa tsauraran sharuɗɗa da suka haɗa da kuɗi har Naira miliyan 100 tare da mutum guda da zai tsaya masa da irin wannan adadi.

Yayin da take yanke hukuncin, Mai Shari’a Abdulmalik ta gindaya wasu tsauraran sharuɗɗa da wanda ake ƙara dole ya cika kafin a kammala batun belin.

Kotun ta ce dole ne mutumin da zai tsaya masa ya kasance mazaunin yankin Maitama ko Asokoro a Abuja, sannan ya ajiye ainihin takardar mallakar fili ko gida (Certificate of Occupancy) a ma’ajiyar kotu.

Haka kuma, dole ne wanda zai tsaya masa ya kasance ma’aikacin Gwamnatin Tarayya wanda matsayin sa bai gaza mataki na 17 (Grade Level 17) ba, sannan ya gabatar da shaidar biyan albashi na aƙalla watanni uku, tare da wasiƙa daga manajan banki da ke ƙarƙashin ikon kotun da ke tabbatar da hakan.

Kotun ta kuma umurci wanda zai tsaya masa da ya rantse a gaban kotu kan ƙarfin sa na kuɗi, ya rattaba hannu kan takardar belin, sannan ya gabatar da sabon hoton fasfo zuwa ma’ajiyar kotu.

A matsayin wani ɓangare na sharuɗɗan belin, an umurci El-Rufai da ya miƙa duk wasu ingantattun fasfo ɗin sa na ƙasa da kasa zuwa ma’ajiyar kotu.

Kotun ta kuma buƙaci a gabatar da wasiƙar tantancewa daga sashen aikin wanda zai tsaya masa, tare da takardar shaidar biyan haraji na watanni shida da suka gabata.

Mai Shari’a Abdulmalik ta kuma umurci wanda ake ƙara da ya riƙa zuwa hedikwatar Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) a kowace Juma’ar ƙarshe ta wata da ƙarfe 10 na safe domin sanya hannu a rajistar halarta har sai an yanke hukunci a shari’ar.

Alƙalin ta gargaɗi cewa rashin cika waɗannan sharuɗɗa zai sa a soke belin kai-tsaye.

Bugu da ƙari, kotun ta umurci wanda ake ƙara da ya gabatar da wasiƙar shaidar gaskiya daga Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Kaduna.

Tags: Babbar Kotun Tarayya AbujabeliMai Shari’a Joyce AbdulmalikNasir El-Rufa'i
Previous Post

Nijeriya da Jamus sun ƙulla yarjejeniyar zuba jari ta dala miliyan 428

Next Post

Nijeriya ta jaddada ƙudirin kare ’yancin addini da haɗin gwiwar addinai

Related Posts

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
Next Post
Nijeriya ta jaddada ƙudirin kare ’yancin addini da haɗin gwiwar addinai

Nijeriya ta jaddada ƙudirin kare ’yancin addini da haɗin gwiwar addinai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!