• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Sunday, November 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

ADC ta yi da zanga-zanga kan ƙin amincewar da INEC ta yi da shugabancin Mark

New Citizen Hausa by New Citizen Hausa
April 8, 2026
in Siyasa
A A
0
ADC ta yi da zanga-zanga kan ƙin amincewar da INEC ta yi da shugabancin Mark
Shugabannin ADC a wajen zanga-zangar

Shugabannin ADC a wajen zanga-zangar

Jam’iyyar ADC a yau Laraba a Abuja ta gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin amincewa da matakin da Hukumar Zaɓe mai Zaman kan ta ta Ƙasa (INEC) ta ɗauka na ƙin amincewa da shugabancin Sanata David Mark.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa zanga-zangar ta fara ne daga Randabawul na Maitama zuwa hedikwatar INEC a Babban Birnin Tarayya (FCT).

Zanga-zangar, wadda Mark – shugaban jam’iyyar na ƙasa – ya jagoranta, ta samu halartar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabi’u Kwankwaso, Rotimi Amaechi, Aminu Tambuwal da Dino Melaye.

Da yake jawabi a wurin zanga-zangar, Mark ya ce fassarar hukuncin kotu aiki ne na ɓangaren shari’a kaɗai, ba na shugaban INEC ba.

Ya ce yunƙurin karɓar aikin ɓangaren shari’a na nufin keta kundin tsarin mulki mai tsanani tare da take ƙa’idar rabuwar iko tsakanin ɓangarori.

Ya ce: “Wasiƙar da INEC ta aike wa ADC kwanan nan tana ƙara tabbatar da zargin cewa hukumar ta daina tsayawa tsaka-tsaki, maimakon haka ta karkata zuwa ga ɓangarorin cikin jam’iyya.

“Wannan ba kawai ba daidai ba ne, har ma yana da haɗari ga amincin tsarin zaɓen mu.”

Jagororin masu adawar

Mark ya ce a rubuce yake cewa mutumin da ake magana a kan sa ya halarci taron NEC na ADC, inda aka rushe NWC da Shugaba Ralph Nwosu yake jagoranta, wanda kuma Nafi’u Bala ke cikin sa.

“Da yake ya shiga wannan shawara, duk wani dogaro daga baya da tsohon matsayin sa ko sa hannun sa ba shi da tushe, ya saɓa wa juna, kuma ba shi da inganci a doka.”

A cikin wata wasiƙar ƙin amincewa wadda Mark da Rauf Aregbesola suka sanya wa hannu kuma aka miƙa wa INEC yayin zanga-zangar, ADC ta buƙaci:

1. Murabus nan take na shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan

2. Janye nan take wasiƙar INEC da suka kira “mai ɓata rai” da aka aike wa ADC

3. Neman gafara a hukumance ga jam’iyyar

Masu zanga-zangar sun kuma bukaci INEC ta yi alƙawarin daina tsoma baki a harkokin cikin gida na jam’iyyun siyasa.

ADC ta ce za ta yi amfani da duk hanyoyin doka da kundin tsarin mulki domin tabbatar da an ɗauki mataki, ciki har da shigar da ƙara a kotu da kuma haɗa gwiwar matakan farar hula, idan INEC ta gaza bin buƙatun su.

Dandazon ‘yan zanga-zangar a hanyar zuwa ofishin INEC

Wani ɓangare na jam’iyyar a ƙarƙashin jagorancin Nafi’u Bala dai yana cikin rikicin shari’a da ɓangaren Mark kan ikon tafiyar da jam’iyyar.

Har ila yau, INEC ta dakatar da amincewa da ɓangarorin biyu, bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da kuma shari’ar da ke gudana a Babbar Kotun Tarayya kan shugabancin jam’iyyar.

Tags: adawaADCDavid MarkINECNafi'u Balashari'azanga-zanga
Previous Post

Yadda CBN ya kori tsoffin shugabannin Bankin Union, bayan gano badaƙala, gidoga da harƙallar wasoson maƙudan kuɗaɗen masu ajiya a bankin

Next Post

Amurka ta fara kwashe ma’aikatan ofishin jakadancin ta na Abuja

Related Posts

Tinubu ya ƙudiri aniyar ba manoma lamunin kuɗi ba tare da ruwa ba
Siyasa

Tinubu ya ƙudiri aniyar ba manoma lamunin kuɗi ba tare da ruwa ba

November 28, 2026
Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC
Siyasa

Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC

November 24, 2026
Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf
Siyasa

Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf

November 23, 2026
Next Post
Tsaro: Nijeriya da Amurka sun ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa don kare ’yancin addini da rayukan jama’a

Amurka ta fara kwashe ma’aikatan ofishin jakadancin ta na Abuja

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!