• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Za mu girka cibiyar kyamarori masu amfani da AI don yaƙar rashin tsaro a Filato — Tinubu

Admin-content by Admin-content
April 2, 2026
in Tsaro
A A
0
Za mu girka cibiyar kyamarori masu amfani da AI don yaƙar rashin tsaro a Filato — Tinubu
Shugaban Ƙasa Tinubu yana yi wa jama'ar Filato jaje a lokacin da ya kai ziyara a Jos yau Alhamis

Shugaban Ƙasa Tinubu yana yi wa jama'ar Filato jaje a lokacin da ya kai ziyara a Jos yau Alhamis

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya jajanta wa waɗanda rikicin addini ya shafa yayin ziyarar sa a Jos a yau.

Shugaban ya tabbatar wa da al’ummar Jihar Filato cewa Gwamnatin Tarayya za ta girka wata hanyar sadarwar kyamarori na zamani sama da 5,000 masu amfani da fasahar basirar na’ura (AI) domin taimaka wa jami’an tsaro wajen yaƙar rashin tsaro a jihar.

Shugaban ya yi wannan alƙawari ne a jawabin da ya gabatar yayin ziyarar sa a Jos a yau.

Ya kuma jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar kan hare-haren bindiga na ranar 29 ga Maris da suka yi sanadiyyar mutuwar fararen hula waɗanda ba su ji ba su gani ba a yankin Angwan Rukuba da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.

Ya ce: “Na yi maku alƙawarin cewa wannan lamari ba zai sake faruwa ba.”

Tinubu ya umurci Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Janar Waidi Shaibu, da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Disu, da su “tono tare da gano masu kashe ‘yan Nijeriya waɗanda ba su ji ba su gani ba.”

Ya bayyana cewa Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Bosun Tijjani, zai jagoranci aikin girka kyamarorin tsaro nan take tare da haɗin gwiwa da gwamnatin Jihar Filato da hukumomin tsaro.

Za a fara girka su a garin Jos kafin a faɗaɗa aikin zuwa sauran sassan Jihar Filato, bisa tsarin da aka riga aka samu nasarar aiwatarwa a jihohin Legas da Inugu.

Yayin da yake nuna damuwar sa kan raɗaɗin da sabon tashin hankalin ya haifar, Tinubu ya bayyana takaicin sa da ya kalli bidiyoyin tashin hankali daga Jos.

Ya ce wa iyalan da abin ya shafa a taron da aka yi a filin jirgin sama na Yakubu Gowon: “Allah ne kaɗai zai iya ba ku farin ciki da kwanciyar hankali.”

Ya ƙara da cewa: “Babu wani kuɗi da zai iya maye gurbin rayukan da aka rasa.”

Shugaban ya yi alƙawarin cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da an yi adalci tare da taimaka wa iyalan waɗanda suka rasu.

Ya kuma umurci Ministan Harkokin Jinƙai, Bernard Doro, da ya tattara cikakkun bayanai kan waɗanda tashin hankalin ya shafa domin tabbatar da cewa tallafin gwamnati ya kai ga kowa cikin adalci.

Da yake jawabi ga shugabanni da masu ruwa da tsaki, Tinubu ya jaddada buƙatar ɗaukar matakan kariya domin hana sake aukuwar irin waɗannan hare-hare a nan gaba.

Ya ce: “Me ya sa abubuwan da suka faru a baya ba su zama darasi gare mu ba? Na saurari Jonah Jang, Wase, Lalong, Nentawe da Gwamna Mutfwang.

“Gwamna, kai da ni an zaɓe mu ne domin samar da zaman lafiya da tsaro, ba domin ta’aziyya ko ƙirƙirar zawarawa da marayu ba. An zaɓe mu ne domin kawo ci gaba da haɗin kai, da raba bege da buri ga kowa, tare da jagorantar matasa.”

Ya ƙara da cewa: “Ina tabbatar wa da matasan mu da ke nan cewa ba na son in riƙa zuwa nan domin ta’aziyya—ina son in zo ne domin tabbatar da zaman lafiya.”

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya ce jihar ta dade tana more zaman lafiya kafin wannan mummunan lamari na ranar 29 ga Maris, yana mai bayyana shi a matsayin koma-baya na ɗan lokaci.

Ya yaba wa jami’an tsaro kan ƙoƙarin su, tare da nuna ƙwarin gwiwa cewa matakan da suke ɗauka za su ƙara ƙarfafa tsaro.

Ya ce: “Za mu yi nasara a wannan yaƙi da rashin tsaro,” yana ƙara da cewa gwamnatin yanzu ta gaji waɗannan ƙalubale ne kuma tana ɗaukar dukkan matakan da za ta iya don magance su.

Mutfwang ya kuma gode wa Shugaba Tinubu bisa amincewa da ɗaukar ma’aikatan tsaron daji 1,000 domin ƙara ƙarfafa tsaro a jihar.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya gode wa Shugaba Tinubu bisa tsayawa tare da al’ummar Filato, yana mai cewa rikicin ya daɗe yana ci gaba.

Ya bayyana fatan cewa ziyarar Shugaban za ta ƙarfafa jami’an tsaro, ta rage hare-hare, tare da ba iyalan da abin ya shafa kwanciyar hankali.

Ya ce: “Za mu ci gaba da zama tare da jama’ar mu domin nemo mafita mai ɗorewa ga wannan matsala.”

Tsohon gwamnan jihar, Jonah David Jang, ya goyi bayan buƙatar da aka gabatar ta gudanar da taro na musamman a Abuja domin nemo mafita mai ɗorewa ga rikicin Filato.

Manyan baƙi suna sauraren jawabin Shugaban Ƙasa Tinubu a taron da ya yi da su a Filin Jirgin Sama na Yakubu Gowong da ke Jos a yau Alhamis

Ya ce: “Ni na yi fama da shi, Joshua Dariye ya ya yi fama da shi, Simon Lalong ya yi fama da shi. Yanzu da tashin hankalin ke fita daga ƙauyuka zuwa cikin birane, wannan wani sabon salo ne da ba ma son gani.”

Ya zargi wasu mutane da ƙoƙarin kawo cikas ga zaɓe mai zuwa da kuma nasarorin da Tinubu ke samu ga ƙasa.

Ya ce: “Kana yin aiki mai kyau ga ƙasa, amma wasu na son su lalata shi ta wannan hanya.”

Sanata Simon Lalong ya tuna yadda jihar ta taɓa shiga yanayin dokar ta-ɓaci a baya.

Ya ce: “Mun yi tunanin komai ya wuce, amma sai ga shi yana sake dawowa. Filato na da gata. Idan aka haɗa Jonah Jang, Joshua Dariye, Simon Lalong da Mutfwang tare da sarakunan gargajiya, za a samu mafita ga matsalolin jihar.

“Na faɗi haka ne domin dukkan mu mun fuskanci wannan lamari. Mafita tana hannun mutanen Filato. Idan muka shirya, za mu ba ku mafita, Mai Girma Shugaban Ƙasa. Shi ya sa muke buƙatar taron sirri a Abuja domin mu faɗi gaskiya.”

Ya ƙara da cewa: “Ba jami’an tsaro ba ne za su kawo zaman lafiya—mutanen Filato ne za su kawo shi.”

Tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Ahmed Idris Wase, ya ce har yanzu akwai aiki mai yawa da ya rage domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Filato.

Ya yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin Rundunar Sojin Sama da sojojin ƙasa, musamman yayin da damina take tafe.

Ya ce: “A Wase da Kanke kaɗai, a makon da ya gabata mun rasa sama da mutane 14, ciki har da wani Kyaftin na rundunar sojin Nijeriya.”

Tags: Filatorashin tsaroTinubu
Previous Post

Cikar FRCN shekara 75: Tinubu yana zamanantar da kafafen yaɗa labarai – Ministan Yaɗa Labarai

Next Post

Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista

Related Posts

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano
Tsaro

EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano

November 17, 2026
Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi
Tsaro

Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi

November 6, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci bincike kan bidiyon atisayen muzaharar Izala
Tsaro

’Yan sanda sun kama matashin Izala kan bidiyon da ke tunzura rikicin addini

October 27, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

’Yan sanda a Katsina sun tabbatar da kashe Sheikh Yahaya Masussuka da abokin sa

October 26, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka

October 26, 2026
Next Post
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista

Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!