• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shirin ƙarfafa tattalin arzikin Nijeriya zuwa dala tiriliyan ɗaya: Bankuna 21 da suka cika ƙa’idojin CBN

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
January 20, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Shirin ƙarfafa tattalin arzikin Nijeriya zuwa dala tiriliyan ɗaya: Bankuna 21 da suka cika ƙa’idojin CBN
Bankunan Nijeriya

Bankunan Nijeriya

Bankunan Nijeriya 21 sun cika sababbin ƙa’idojin mafi ƙanƙantar jarin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya gindaya, yayin da ɓangaren bankuna ke hanzarta bin shirin sake ƙarfafa jari da aka fara a 2024.

Wannan shiri na da nufin ƙara ƙarfin bankuna wajen jure girgizar tattalin arziki da kuma ba su damar ba da gudunmawa mai ma’ana ga bunƙasar tattalin arzikin ƙasa.

Sabbin ƙa’idojin sun tanadi Naira biliyan 500 ga bankunan kasuwanci masu lasisin ƙasa da ƙasa, naira biliyan 200 ga bankunan masu lasin kasuwanci a faɗin ƙasar nan, da naira biliyan 50 ga bankunan cikin yankuna da shiyya.

Ga bankunan da ke aiki hadahada bisa tsarin da babu kuɗin ruwa, an sa naira biliyan 20 mafi ƙanƙantar jarin su. Sai Naira biliyan 10 ƙa’idar bankunan yanki.

An ba bankuna wa’adin watanni 24 domin cika wannan sharaɗi, wanda zai ƙare a ranar 31 ga Maris, 2026. Wannan ya haifar da yawaitar fitar da hannun jari, tattaunawar haɗewar bankuna, da sake tsara ma’aunin kuɗaɗe.

Wannan shiri ya yi kama da na shekarar 2004 a lokacin tsohon gwamnan CBN, Charles Soludo, wanda ya tilasta bankuna su ƙara jarin su daga naira biliyan 2 zuwa naira biliyan 25. Wannan mataki ya rage adadin bankuna daga 89 zuwa 25, tare da samar da manyan bankuna masu ƙarfi a lokacin.

Zuwa 8 ga Janairu, bankuna 21 sun riga sun cika sabbin ƙa’idojin, inda Access Bank ya zama bankin farko da ya kai matakin naira biliyan 500.

Bankunan da Suka Cika Sabbin Ƙa’idojin Jarin CBN

Bankunan Kasuwanci Masu Lasisin Ƙasa da Ƙasa (₦500bn):

  • Access Bank – Jarin sa ya kai naira biliyan 602.8.
  • Zenith Bank – Jarin sa ya kai naira biliyan 614.
  • First HoldCo (First Bank) – Ya cika sharaɗin CBN ta hanyar sayar da wani reshen kasuwanci.
  • GTCO (GTBank) – Sama da Naira biliyan 504 bayan shirye-shiryen tara jari a matakai daban-daban.
  • United Bank for Africa (UBA) – Ya ya zarce Naira biliyan 500 bayan tara jari a 2024 da 2025.
  • Fidelity Bank – Jarin sa ya kai naira biliyan 564.5.

Bankuna Masu Lasin Cikin Ƙasa:

(naira biliyan)

  • Wema Bank – Ya kammala tara naira biliyan 150; yana jiran tabbatarwar ƙarshe daga CBN
  • Citibank Nigeria – Ya cika sharadin (ba a bayyana yadda aka tara jari ba)
  • Standard Chartered Bank Nigeria ( Shi wannan banki ya samu taimakon jari daga babbar cibiyar kamfanin a Birtaniya)
  • Ecobank Nigeria – Ya wuce matakin Naira biliyan 200.
  • Globus Bank – Ya haura naira biliyan 200, bayan tara jari a 2024–2025.
  • Stanbic IBTC – Ya tara naira biliyan 200.
  • PremiumTrust Bank – Ya wuce wuce naira biliyan 200.
  • Providus Bank – Ya cika sharaɗin ta hanyar haɗewa da Unity Bank.

Bankunan Merchant:

  • FSDH Merchant Bank,
  • Greenwich Merchant Bank,
  • Nova Bank da
  • Rand Merchant Bank.

Bankunan Da Babu Kuɗin Ruwa:

  • Jaiz Bank
  • Lotus Bank
  • TAJBank
Tags: bankunaCBNMohammedIdris
Previous Post

Duk za a fice daga ADC idan Atiku ya zama ɗan takarar jam’iyyar, inji Hakeem Baba-Ahmed

Next Post

Hotuna: Sarkin Kano Sanusi a aji a matsayin ɗalibi

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Hotuna: Sarkin Kano Sanusi a aji a matsayin ɗalibi

Hotuna: Sarkin Kano Sanusi a aji a matsayin ɗalibi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!