Kamfanin sada zumunta na TikTok ya bayyana cewa ya dakatar da fasalin kai-tsaye wato “LIVE” na hirar dare a Nijeriya na ɗan lokaci, sakamakon yawaitar watsa shirye-shirye da ke ɗauke da aikace-aikacen batsa da sauran manyan abubuwan fasiƙanci.
Masu amfani da TikTok a Nijeriya ba za su iya yin ko kallon LIVE tsakanin ƙarfe 11 na dare zuwa 5 na safe ba — waɗannan su ne lokutan da ake samun mafi yawan hotunan batsa.
Dandalin na soshiyal midiya ya ce manufar ɗaukar wannan matakin ita ce kare masu amfani da kuma ƙarfafa tsaron abun ciki.
A baya, TikTok sun cire fiye da zaman LIVE 49,000 a Nijeriya da suka ƙunshi abubuwan batsa, kuma ba su bayyana tsawon lokacin da wannan taƙaitawar zai ɗauka ba.







