• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar ƙarfafa wa matasa gwiwa – Minista

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
November 10, 2025
in Labarai
A A
0
Roƙon gwamnati ga ‘yan Nijeriya kan rikicin diflomasiyya da Amurka: Ku kwantar da hankalin ku
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, a wurin taron shekara na matasan Arewa-maso-yamma na 2025

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, a wurin taron shekara na matasan Arewa-maso-yamma na 2025

GWAMNATIN Tarayya ta sake tabbatar da ƙudirin ta na ƙarfafa wa matasan Nijeriya gwiwa ta hanyar shirye-shiryen sauya rayuwa da ke bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da ƙirƙira.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a Dutse, Jihar Jigawa, yayin da yake jawabi a matsayin Baƙo na Musamman a Taron Matasan Arewa-maso-yamma na APC, inda matasa suka taru don murnar nasarorin da aka samu cikin shekaru biyu na Shirin Sabunta Fata na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Idris ya ce Shugaban Ƙasa Tinubu ya nuna cikakken amincewa da ƙwarewar matasa ta hanyar ba su muhimman damarmaki da jagoranci a manyan muƙamai.

A cewar sa, “Daga naɗin ministoci zuwa cigaban fasaha da sauye-sauyen tsarin ilimi, matasan Nijeriya ba kawai suna cikin labarin ba ne, su ne ke jagorantar shi.”

Ministan ya jero wasu daga cikin manyan nasarorin gwamnati da suka shafi matasa, ciki har da Asusun Lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFUND) inda aka riga aka raba naira biliyan 116 ga ɗalibai sama da 620,000, da kuma shirin 3MTT wanda ya jawo kusan matasa miliyan biyu cikin yunƙurin samar da ayyukan fasaha da na’ura har miliyan uku a faɗin ƙasa.

Haka kuma ya bayyana Shirin Horon Fasaha da Sana’o’i (TVET) wanda ya bada takardar shaidar ƙwarewa ga ‘yan Nijeriya miliyan ɗaya a fannoni 25, inda kashi ɗaya bisa huɗu daga cikin su ke ci gaba da karatu a cibiyoyin koyarwa.

A cewar sa, “Waɗannan ba shiri ba ne kawai, sakamako ne da ake gani a makarantu, cibiyoyin koyarwa, da al’ummomi a faɗin ƙasar nan.”

Ministan ya ƙara da cewa Shirin Samar da Wutar Lantarki ga Makarantu na Hukumar Wutar Lantarki ta Ƙauyuka (REA) yana samar da wutar lantarki mai ɗorewa ga jami’o’in tarayya da asibitocin koyarwa kamar Jami’ar Bayero ta Kano da Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo ta Sakkwato, don bai wa ɗalibai damar yin karatu da bincike ba tare da katsewar wuta ba.

Game da gyaran tsarin tattalin arziki, Idris ya bayyana cewa sabuwar Dokar Haraji ta Nijeriya, wadda za ta fara aiki a watan Janairu 2026, za ta keɓe ƙananan kamfanoni masu samun ƙasa da naira miliyan 100 daga biyan harajin kamfani da na ribar jarin kasuwanci — matakin da ya ce zai “ba dubban matasa ‘yan kasuwa damar zuba jari a burin su da bunƙasa kasuwancin su.”

Ya kuma ambaci wasu shirye-shiryen da ake ci gaba da aiwatarwa, kamar MSME Clinics, shirin iDICE — haɗin gwiwar dala miliyan 517 don bunƙasa tattalin arzikin fasaha da ƙirƙira — da kuma samun nasarar Eurobond na Nijeriya da aka saye sama da kashi 400, wanda ya bayyana a matsayin “shaida ta ƙaruwar amincewar duniya ga tsarin tattalin arzikin Nijeriya.”

Ministan ya ƙara da cewa cire sunan Nijeriya daga FATF Grey List ya ƙara tabbatar da sahihancin gwamnatin da kuma ingantacciyar matsayin ƙasar a idon ƙasashen duniya.

Ya yi kira ga matasa da su guji yaɗa labaran ƙarya da kalaman rarrabuwar kai, yana jaddada cewa makomar ƙasar tana hannun su.

A cewar sa, “Mu yi amfani da muryoyin mu da dandamalin mu wajen gina ƙasa, ba rusa ta ba.”

Ya ƙara da cewa, “Jagorancin Tinubu yana nufin bai wa kowane ɗan Nijeriya, ko daga ina yake, daidaitacciyar dama ta yin nasara.”

Idris ya sake tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da gina Nijeriya wadda ƙwazon matasa da ƙirƙirar su ke tafiyar da cigaban da sabuntawar ƙasa.

Taron ya samu halartar Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi; Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Jigawa, Rt. Hon. Haruna Aliyu; Ministan Cigaban Matasa, Mista Ayodele Olawande; Ƙaramin Ministan Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmed; Shugaban Matasa na Ƙasa na jam’iyyar APC, Dakta Dayo Israel; Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Matasa, Sanata Iya Abbas; Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin ‘Yan Sanda, Sanata Ahmed Abdullahi; da Manajan Daraktan NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr, tare da sauran manyan baƙi da wakilai daga Arewa-maso yamma.

Tags: Arewa-maso-yammaDutsematasaMohammed Idris
Previous Post

Roƙon gwamnati ga ‘yan Nijeriya kan rikicin diflomasiyya da Amurka: Ku kwantar da hankalin ku

Next Post

Gwamnatin Tinubu ta rage kuɗin zuwa aikin Hajji

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Gwamnatin Tinubu ta rage kuɗin zuwa aikin Hajji

Gwamnatin Tinubu ta rage kuɗin zuwa aikin Hajji

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!