• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnati Ta Dakatar Da Kafa Manyan Makarantu Tsawon Shekaru 7 Don Inganta Waɗanda Ake Da Su .

WAKILIN MU by WAKILIN MU
August 14, 2025
in Labarai
A A
0

 

Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da sanya takunkumin shekaru bakwai kan kafa sababbin makarantun gaba da sakandare na tarayya a faɗin ƙasar nan.

Wannan ya haɗa da jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana cewa matsalar da ake fuskanta a fannin ilimi yanzu ba ta samun damar shiga makarantu ba ce, sai dai yawan maimaita kafa sababbin makarantu ba tare da isasshen kayan aiki da ma’aikata ba, wanda ke rage ingancin ilimi da lalata darajar da ɗaliban Nijeriya suke da ita a idon duniya.

Alausa ya ce akwai jami’o’i na tarayya 72, na jihohi 108, da masu zaman kan su 159, haka kuma akwai irin wannan yawaitar a kwalejojin fasaha da na ilimi, gami da wasu cibiyoyi kamar “monotechnics”, kwalejojin noma, na kiwon lafiya da makamantan su.

Ya bayyana cewa a wasu makarantu adadin ɗaliban da ke nema ya ragu ƙwarai. Haka ma a kwalejojin fasaha 295 da kwalejojin ilimi 219, inda wasu daga ciki ba su samu ɗalibi ko ɗaya ba, lamarin da ke nuna asarar kuɗaɗe da rashin inganci.

Ya ce akwai misali daga arewacin ƙasar inda wata jami’ar tarayya ke da ƙasa da ɗalibai 800 amma tana da ma’aikata fiye da 1,200, wanda ya kira da abin da ba zai ɗore ba.

Bisa haka, gwamnati ta ɗauki matakin taƙaita kafa sababbin makarantu domin mayar da hankali wajen inganta waɗanda ake da su, ta hanyar ƙara ƙarfin su, gyara kayan aiki da samar da ƙwararrun malamai.

Ya ce manufar ita ce a ƙara ingancin ilimi, don tabbatar da cewa ƙasashen duniya na ci gaba da girmama digirorin Nijeriya.

Sai dai duk da takunkumin, FEC ta amince da kafa sababbin jami’o’i masu zaman kan su guda tara wanda suka daɗe a Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) kimanin shekaru shida.

An kammala gina makarantun tuni da saka jarin biliyoyin naira.

Alausa ya kuma ce an yi garambawul ga ka’idoji guda 350 ba sa aiki aiki a baya, kuma daga yanzu duk makarantar da za a kafa, ko ta gwamnati ko mai zaman kan ta, ba za ta samu amincewa ba sai ta cika sababbin sharuɗɗan.

Ya gargaɗi cewa idan ba a ɗauki mataki ba, yawan rashin aikin yi ga matasa zai ƙaru, kuma hakan zai rage tasirin digirin Nijeriya a duniya.

Previous Post

Cire Tallafin Mai Ya Taimaka Mana Wajen Aiwatar da Ayyuka, Inji Gwamna

Next Post

Babban Titin ‘Trans-Sahara’ Zai Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Da Ƙarin Damar Tattalin Arziki – Minista Idris

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post

Babban Titin 'Trans-Sahara' Zai Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Da Ƙarin Damar Tattalin Arziki – Minista Idris

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!