Shugaban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC), Injiniya Bayo Ojulari, ya bayyana cewa an kammala kashi 72 cikin ɗari na aikin bututun gas daga Ajakuta zuwa Kano.
Ya ƙara da cewa aikin gina bututun iskar gas ɗin na AKK da ya kai darajar dala biliyan $2.8 yana dab da kammaluwa inda yanzu aka cimma kashi 72 cikin 100 na aikin a watanni huɗu na farko na shekarar 2025.
Cigaban aikin bututun wani babban tabbaci ne cewa nan ba da jimawa ba iskar gas mai tsafta ta CNG za ta karaɗe Arewacin Nijeriya, abin da ka iya janyo karyewar farashin man fetur da kuma ƙarfafa wa masana’antu da sufuri gwiwa a yankin.
Haka zalika aikin wani babban cigaba ne da ke nuna yadda Gwamnatin Tarayya ke jajircewa wajen ciyar da Arewacin Nijeriya gaba ta hanyar muhimman ayyukan raya ƙasa.






