• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tinubu Ta Tallafa Wa Sama Da Gidajen Talakawa 226,000 A Nasarawa

Wakilin Mu by Wakilin Mu
September 7, 2025
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tinubu Ta Tallafa Wa Sama Da Gidajen Talakawa 226,000 A Nasarawa
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Gwamnatin Tarayya ta ce kimanin gidaje 226,760 da ke cikin mawuyacin hali a Jihar Nasarawa sun amfana daga shirin “Household Prosperity and Empowerment” (HOPE), wato shirin ƙarfafa gidaje da rage talauci.

Mai kula da shirin HOPE a jihar, Rhoda Agbawu, ce ta bayyana haka a yayin taron kwana ɗaya da aka gudanar a Lafia domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan yadda shirin yake tafiya.

Ta ce taron ya samu halartar hukumomi daban-daban, ƙungiyoyin farar hula da na addinai domin tabbatar da shirin ya ci gaba da ɗorewa.

“Mun yi wannan taro ne domin tabbatar da shigar kowa cikin aikin aiwatar da shirin. Za mu haɗa kai da hukumar saka jari ta jihar Nasarawa domin tabbatar da cewa wannan shiri ya dore,” inji ta.

Ta kuma gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa ƙirƙirar shirin tare da yin godiya ga Gwamna Abdullahi Sule bisa nuna kulawa da marasa galihu a jihar.

A nasa jawabin, Darakta-Janar na Hukumar Tallafin Jama’a ta jihar Nasarawa (NSSIA), Malam Imran Jibrin, wanda shi ne mai magana sa yawun HOPE a jihar, ya ce shirin na da nufi shafar gidaje miliyan 15 da ke cikin talauci a faɗin ƙasar nan ta hanyar bai wa mutane kuɗi kai tsaye.

Ya ce a halin yanzu sama da gidaje miliyan biyu ne suka amfana a duk fadin Najeriya, inda aka kashe fiye da Naira biliyan 300.

“Gidaje da a da suke fama da ƙalubalen rayuwa yanzu sun samu sauƙi. Mata na iya ciyar da ’ya’yansu cikin kwanciyar hankali, gidaje kuma suna samun tallafi. Wannan ya dawo da martaba da fata mai kyau a zukatan mutane,” inji Jibrin.

Ya ƙara da cewa tun daga 2021, gwamnatin jihar ta yi amfani da shirin tura kudi kai tsaye na conditional cash transfer wajen tallafa wa gidaje fiye da 10,000 a cikin ƙananan hukumomi 13 na jihar.

Ita ma Kwamishinar Harkokin Mata da Cigaban Al’umma ta jihar, Hajiya Hauwa Jugbo, ta gode wa Tinubu da Gwamna Sule bisa jajircewa wajen tallafa wa marasa galihu.

Tags: Bola Ahmed TinubugidajeHOPENasarawaRhoda Agbawutallafi
Previous Post

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Jajen Rasuwar Mutane A Nutsewar Jirgin Ruwa A Borgu, Ta Umurci NEMA Ta Kai Agaji 

Next Post

Bashin Da Ake Bin Najeriya Abin Tsoro Ne – Kakakin Majalisa

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Bashin Da Ake Bin Najeriya Abin Tsoro Ne – Kakakin Majalisa

Bashin Da Ake Bin Najeriya Abin Tsoro Ne - Kakakin Majalisa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!