
HUKUMAR Aikin ‘Yan Sanda (PSC) ta amince da ƙara wa Kwamishinonin ‘Yan Sanda (CPs) guda 12 zuwa muƙamin Mataimakan Sufeto Janar (AIG), kuma ta ƙara wa wasu manyan jami’an ‘yan sandan su 226 girma.
A cikin wata sanarwa da ya bayar a Abuja ranar Litinin, jami’in yaɗa labarai na hukumar, Mista Ikechukwu Ani, ya ce waɗanda aka yi wa ƙarin sun haɗa da Mataimakan Kwamishinan ‘Yan Sanda (DCOs) mutum 16 da aka ɗaga zuwa muƙamin CP, da ACP su 27 da suka koma DCP, da Manyan Suferitendan ‘Yan Sanda (CSP) su 145 da suka koma ACP.
Ya ce amma akwai wani ACP, wanda bai halarci zaman ƙarin girman ba, shi sai aka tsallake shi, ba a yi masa ƙarin ba.
Haka kuma, hukumar ta ƙara wa Suferitendan ‘Yan Sanda (SP) guda 29 girma zuwa muƙamin CSP, da DSP guda 38 da suka zama SP.
Mista Ani ya bayyana cewa waɗannan da aka ƙara wa girma sun haɗa da ‘yan sanda masu aikin gama-gari (wato General Duty) da kuma ma’aikatan musamman kamar waɗanda suke ɓangaren jiragen sama, likitoci, masanan haƙori, masu bada magani, ma’aikatan ɗakin gwajin jini, nas-nas, injiniyoyin jirgin sama, da sauran su.
Kwamishinoni 12 da suka zama AIG su ne: Johnson Adenola, Ako Gabriel, Ahmadu Abdullahi, Emmanuel Aina, Omolara Oloruntola, Hassan Yababet, Bretet Simon, Enyinnaya Adiogu, Aminu Raji, Mohammed Usman, Festus Oko, da Ronke Okunade.
Su kuma DCP 16 da aka tura gaba zuwa muƙamin CP su ne: Uduak Ita, Sheikh Danko, Charles Dike, Nnana Ama, Gabriel Eliagwu, Abiola Olutunde, Yakubu Dankaro, Michael Falade, Aina Adesola, Umar Chuso, Emefile Osifo, Innocent Anagbado, Musa Sani, Victor Erivwode, Omoikhudu Philip da Sylvester Edogbanya.
Ani ya ce waɗanda suka yi nasara a wannan ƙarin girma sai da suka yi zaman jarabawa da intabiyu da hukumar ta gudanar a wani ɓangare na tsarin ƙarin girman.
Shi dai aikin ƙarin girman, Mista Taiwo Lakanu, wato Ciyaman na Tsayayyen Kwamitin Al’amuran ‘Yan Sanda, shi ne ya jagoranci yin sa, kuma ya gabatar da rahoton sa ga hukumar a wani zama na musamman da ta yi domin amincewa.






