• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

FATI ABDUL by FATI ABDUL
November 25, 2026
in Tsaro
A A
0
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Malam Nasir El-Rufai a kotu

Malam Nasir El-Rufai a kotu

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna da ke tsare, Malam Nasir El-Rufai, ya janye iƙirarin sa na cewa shi da wasu ‘yan adawa sun yi satar sauraron wayar Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu.

Yayin da yake bayar da shaida a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a yau Laraba, ya ce kalamin da ya yi ba gaskiya ba ne, ya yi shi ne don tayar wa gwamnati da hankali.

El-Rufai ya tsaya a kotu ne a matsayin shaida na farko na kare kan sa a shari’ar da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ke yi masa, wadda take zargin sa da satar sauraron tattaunawar wayar Ribaɗu, da wasu laifuka.

Sai dai ya dage cewa yana da masaniyar cewa gwamnati ta sanya manyan ‘yan adawa, tsofaffin shugabannin ƙasa da manyan alƙalai a ƙarƙashin sa ido, kuma shi ko abokan hulɗar sa ba su saci sauraron wayar NSA ba.

Lauyan sa, Paul Erokoro (SAN), ya kunna wani ɓangare na hirar da El-Rufai ya yi da gidan talbijin na Arise a ranar 13 ga Fabrairu, inda ya ce sun saci sauraron wayar Ribaɗu. Da aka nemi ya yi bayani, sai El-Rufai ya amince cewa ya faɗi cewa suna sauraron tattaunawar NSA, kuma wani ya saci sauraron wayar Ribaɗu ya riƙa isar musu da tattaunawar sa.

Ya ce ba da niyyar a fahimci maganar a zahiri ba ne, yana mai kiran ta da “salon magana ta kwalliya da kwatance,” kuma ya ce irin wannan magana halal ce a sadarwar siyasa.

“Abin da nake so in faɗa shi ne gwamnati na sa ido kan ‘yan adawa, kuma mun san abin da suke yi.

“Na yi amfani da kalmar ‘tap’ a matsayin kalamin siyasa don su ji ba daɗi. Magana ce ta kwatance, ba ta zahiri ba. Salon harshe ne kawai, don gwamnati ta ji ba daɗi,” inji shi a gaban kotu.

Erokoro ya tunatar da shi cewa ɗan jaridar da suka yi hirar da shi ya nuna masa cewa satar sauraron wayar wani haramun ne. El-Rufai ya ce manufar sa ita ce ta fallasa abin da ya kira ɓoyayyen sa ido da gwamnati ke yi kan tattaunawar ‘yan adawa ba tare da umurnin kotu ba.

“Ina magana ne a kan gwamnati da ke keta doka, ba wani daban ba,” inji shi.

Dangane da wanda yake nufi da “mu” lokacin da ya ce “muna sauraron tattaunawar su,” ya ce yana nufin shi kan sa ne da sauran manyan ‘yan adawa. Ya ce ba su saci sauraron kiran Ribaɗu ba, sai dai sun samu labarin wani shiri na sace shi a tsare shi ne ta hannun wani aboki na bai-ɗaya, wanda ya ƙi bayyana ko wanene don kare majiyar sa.

A cewar El-Rufai, abokin ya ziyarce shi bayan hirar ya yi masa bayanin cewa ba a saci sauraron wayar NSA ba a zahiri.

El-Rufai ya ce ya amsa masa da cewa ya riga ya san hakan, kuma ya yi iƙirarin ne da gangan don masu mulki su ji ba daɗi.

Ya musanta cewa da hannun sa a satar sauraron wayar, yana mai cewa ba shi da ilimi ko kayan aikin yin hakan.

A farkon shaidar sa, El-Rufai ya ce ya san Ribaɗu tun 2003, lokacin da yake shugaban Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE), ya taimaka masa wajen kafa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Laifukan Kuɗi (EFCC) ta hanyar ba shi wurin aiki da kuɗi. Ya ce dangantakar su ta lalace ne lokacin da Ribaɗu ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2011, domin ya yi imanin cewa tsohon Shugaba Muhammadu Buhari shi ne ya fi cancanta a lokacin. Ya kuma ce NSA ɗin yana gaba da shi ne saboda adawar sa da neman sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu.

A lokacin da lauyan masu gabatar da ƙara, Oluwole Aladedoye (SAN), ke yi masa tambayoyi, El-Rufai, wanda ya ce yana da digiri a fannin shari’a daga Jami’ar London, ya sake ƙin bayyana waɗanda yake nufi da “mu.” Ya kuma ƙi bayyana mutumin da ake zargin ya faɗa masa cewa Ribaɗu, Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani da Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC sun yi taro kuma sun amince a kama shi.

Ya ce ya samu labarin shirin ne kafin dawowar sa daga Alƙahira a ranar 12 ga Fabrairu, kuma ya ƙi yarda jami’an DSS su kama shi a filin jirgin sama saboda ba su nuna sahihin sammaci ba.

El-Rufai ya dage cewa sauran iƙirarin da ya yi a hirar gaskiya ne, ciki har da cewa bai taɓa satar kuɗin gwamnati ba kuma ba shi da masaniya kan ɓacewar ɗan gwagwarmayar nan Dadiyata lokacin da yake gwamnan Kaduna.

Ya ce iƙirarin satar sauraron waya kaɗai ne bai yi daidai ba.

Ya kuma amince cewa ƙararrakin take haƙƙin ɗan’adam da ya shigar kan binciken gidan sa da aka yi da abin da ya kira takardar izini mai lahani, Babbar Kotun Birnin Tarayya da Babbar Kotun Tarayya duk sun yi watsi da su.

A ƙarshen tambayoyin, Aladedoye ya shaida wa kotu cewa Erokoro ya nemi taimakon sa kafin fara zaman, game da shirin kare wanda ake ƙara na gayyatar Ribaɗu da Shugaban ICPC a matsayin shaidu.

Ya ce ya ƙi taimakawa ne saboda lamarin ba a hannun sa yake ba.

Erokoro ya ce zai shigar da buƙatun da suka dace don tilasta bayyanar su.

Mai Shari’a Joyce Abdulmalik dai ta ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranakun 15 da 16 ga Fabrairu, 2027 don El-Rufai ya ci gaba da kare kan sa.

Tags: DSSkotuNasir El-Rufa'iNuhu Ribaɗushari'a
Previous Post

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

Next Post

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

Related Posts

EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano
Tsaro

EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano

November 17, 2026
Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi
Tsaro

Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi

November 6, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci bincike kan bidiyon atisayen muzaharar Izala
Tsaro

’Yan sanda sun kama matashin Izala kan bidiyon da ke tunzura rikicin addini

October 27, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

’Yan sanda a Katsina sun tabbatar da kashe Sheikh Yahaya Masussuka da abokin sa

October 26, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka

October 26, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci bincike kan bidiyon atisayen muzaharar Izala
Tsaro

Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci bincike kan bidiyon atisayen muzaharar Izala

October 26, 2026
Next Post
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!