Ana sa ran Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai halarci tarukan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a jihohi 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja, bayan faɗaɗa jadawalin wuraren da zai ziyarta daga jihohi 12 da aka tsara tun farko gabanin zaɓen 2027.
Sabon jadawalin tarukan kamfen ɗin, wanda sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, ya bai wa manema labarai, ya ƙunshi wurare 20 da ake sa ran shugaban ƙasar zai ziyarta tsakanin ranar 24 ga Oktoba da 13 ga Janairu, 2027.
Sabon jadawalin ya ƙara da jihohin Katsina da Taraba, da kuma Abuja, Zamfara, Imo da Kwara, waɗanda ba su cikin jadawalin farko na wuraren da shugaban ƙasar zai kai ziyara.
Tun da farko, an tsara cewa Tinubu zai halarci tarukan kamfen a jihohi 12, yayin da shugabannin jam’iyyar za su wakilce shi a sauran jihohin.
Sai dai shugaban ƙasar ya riga ya halarci wasu tarukan kamfen a jihohin da ba su cikin jadawalin farko.
A ranar 6 ga Nuwamba, Tinubu ya ziyarci Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom, inda ya halarci taron yaƙin neman zaɓen APC tare da ƙaddamar da wasu ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Gwamna Umo Eno ta gudanar.
Bayan haka, a ranar 7 ga Nuwamba, ya tafi Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas, domin halartar wani taron kamfen na jam’iyyar.
Ziyarar Uyo ta kasance abin lura musamman saboda a jadawalin farko, an ware ranar 18 ga Nuwamba domin gudanar da taron kamfen a jihar, ba tare da bayyana cewa Tinubu zai halarta ba.
Haka kuma, shugaban ƙasar ya halarci taron kamfen na APC a Dutse, Jihar Jigawa, a ranar 10 ga Nuwamba, da kuma taron jam’iyyar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, a ranar 17 ga Nuwamba, duk da cewa ba a saka jihohin cikin jadawalin ziyarar kamfen ɗin sa na farko ba.
Sabon jadawalin ya ƙara da Akwa Ibom, Jigawa da Kebbi cikin jihohin da Tinubu zai halarci tarukan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da kan sa.
Bisa sabon jadawalin, ana sa ran Tinubu zai halarci taron kamfen a Katsina a ranar 2 ga Disamba, Kano a ranar 17 ga Disamba, Jalingo a ranar 19 ga Disamba, Abuja a ranar 21 ga Disamba, Gusau a ranar 28 ga Disamba, sannan Owerri a ranar 30 ga Disamba.
Haka kuma, an tsara shugaban ƙasar zai halarci tarukan kamfen a Yola, Jihar Adamawa, a ranar 4 ga Janairu; Sakkwato a ranar 5 ga Janairu; Ilorin, Jihar Kwara, a ranar 8 ga Janairu; Asaba, Jihar Delta, a ranar 11 ga Janairu; da Legas a ranar 13 ga Janairu.
Sauran jihohin da Tinubu zai halarci tarukan kamfen sun haɗa da Kaduna, Oyo, Borno da Inugu. Sabon jadawalin ya kuma sauya wasu ranakun da aka tsara gudanar da tarukan tun farko.
An sauya taron kamfen na Bauchi, wanda tun farko aka tsara gudanarwa a ranar 29 ga Nuwamba tare da halartar Tinubu, zuwa ranar 1 ga Disamba. Sai dai sabon jadawalin bai nuna cewa shugaban ƙasar zai halarci taron ba.
Haka kuma, an sauya ranar taron kamfen na Sakkwato daga 5 ga Disamba zuwa 5 ga Janairu, 2027, yayin da aka mayar da taron Asaba daga 12 ga Disamba zuwa 11 ga Janairu.
Taron kamfen na Legas, wanda shi ne babban taron rufe yaƙin neman zaɓen, wanda tun farko aka tsara gudanarwa a ranar 9 ga Janairu, yanzu an mayar da shi zuwa ranar 13 ga Janairu.
A jimlace, sabon jadawalin ya ƙunshi tarukan kamfen guda 37 a faɗin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja, inda ake sa ran Tinubu zai halarci guda 20.

Arewa maso Yamma ce kan gaba a jadawalin kamfen ɗin Tinubu
Yankin Arewa maso Yamma ne ke da mafi yawan jihohin da Tinubu zai ziyarta a yayin yaƙin neman zaɓen sa na shugaban ƙasa, inda yake da jihohi bakwai: Kaduna, Jigawa, Kebbi, Katsina, Kano, Zamfara da Sakkwato.
Yankunan Arewa maso Gabas da Kudu maso Kudu ne ke biye da jihohi uku kowannen su.
Arewa maso Gabas na da Borno, Taraba da Adamawa, yayin da Kudu maso Kudu ke da Akwa Ibom, Ribas da Delta.
Yankunan Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas kuwa suna da jihohi biyu kowannen su.
Arewa ta Tsakiya na da Filato da Kwara; Kudu maso Yamma na da Oyo da Legas; yayin da Kudu maso Gabas ke da Inugu da Imo.
A jimlace, jihohi 19 ne aka lissafa a cikin jadawalin kamfen ɗin na Tinubu, baya ga Babban Birnin Tarayya, Abuja.
A lokacin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Abuja, Tinubu ya bayyana cewa ba zai halarci dukkan tarukan kamfen ɗin ba, yana mai cewa akwai buƙatar daidaita harkokin siyasa da ayyukan gudanar da gwamnati.
Shugaban ƙasar ya yi alƙawarin ware lokaci domin tattaunawa kai-tsaye da ‘yan Nijeriya, yayin da shugabannin jam’iyyar za su jagoranci yaƙin neman zaɓen zuwa jihohi da ƙananan hukumomi.







