• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Nijeriya ta shirya karɓar baƙuncin Taron Hulɗar Jama’a na Duniya – Minista

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
November 11, 2026
in Labarai
A A
0
Nijeriya ta shirya karɓar baƙuncin Taron Hulɗar Jama’a na Duniya – Minista
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Alhaji Mohammed Idris, yana jawabi a yayin taron manema labarai kan  karɓar baƙuncin Taron Hulɗar Jama’a na Duniya na shekarar 2026 (WPRF), a Abuja ranar Laraba

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Alhaji Mohammed Idris, yana jawabi a yayin taron manema labarai kan  karɓar baƙuncin Taron Hulɗar Jama’a na Duniya na shekarar 2026 (WPRF), a Abuja ranar Laraba

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin ta na karɓar baƙuncin Taron Hulɗar Jama’a na Duniya na shekarar 2026 (WPRF), wanda ake sa ran wakilai daga ƙasashe sama da 126 za su halarta daga ranar 15 zuwa 22 ga Nuwamba a Abuja.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin wani taron manema labarai a Abuja, inda ya ce taron zai ba Nijeriya damar nuna ƙwarewar ta da kuma ƙarfafa matsayin ta a fagen sadarwa na duniya.

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, shi ne zai zama babban mai masaukin baƙi a taron, wanda zai gudana tare da babban taron Ƙungiyar Hulɗar Jama’a ta Afrika karo na 37 (APRA).

Idris ya ce Nijeriya ce ƙasa ta farko a Yammacin Afrika, kuma ta biyu a nahiyar, da za ta karɓi baƙuncin WPRF.

Ya bayyana taron a matsayin wata dama ta ƙarfafa dangantakar ƙasar nan da sauran ƙasashe, tare da ba da gudunmawa ga tattaunawar duniya kan harkokin sadarwa.

Mahalartan taron suna sauraren jawabin Minista Idris

Da yake tsokaci kan taken taron mai cewa, “Sadarwa Mai Haƙƙi: Muryar Duniya”, ministan ya buƙaci ƙwararrun masu hulɗar jama’a da su riƙa kiyaye gaskiya, sahihancin bayanai, bayyana gaskiya da ƙa’idojin sana’a, musamman a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan yaɗuwar bayanan ƙarya da raguwar amincewar jama’a.

Ya ce: “Dole ne ƙwararrun masu hulɗar jama’a su fahimci cewa nauyin da ke kan su ya wuce kula da martabar mutane ko inganta muradun cibiyoyi. Suna da haƙƙin tabbatar da gaskiya, sahihancin bayanai, bayyana gaskiya, bin ƙa’idojin sana’a da kuma kare muradun jama’a.”

Ministan ya bayyana goyon bayan Gwamnatin Tarayya ga yunƙurin kafa Cibiyar Ƙasa da Ƙasa ta UNESCO mai mataki na biyu kan Ilimin Kafafen Yaɗa Labarai da Bayanai (wato IMILI) a Abuja, yana mai cewa cibiyar za ta taimaka wa ’yan ƙasa, musamman matasa, wajen gane bayanan da za su iya yaudarar su da kuma amfani da kafafen zamani yadda ya kamata.

Idris ya ƙara da cewa ya kamata sadarwar gwamnati ta ƙunshi sauraron jama’a, magance matsalolin su da kuma samar musu da sahihan bayanai domin su yanke shawara bisa cikakken sani.

Shugaban Cibiyar Hulɗar Jama’a ta Nijeriya (NIPR), Dakta Ike Neliaku, ya yaba wa Idris bisa goyon bayan da ya bayar wajen neman damar karɓar baƙuncin taron a Nijeriya.

Shi kuwa Sakatare-Janar na Ƙungiyar Hulɗar Jama’a ta Afrika (APRA), Dakta Omoniyi P. Ibietan, ya bayyana haɗa taron WPRF da babban taron APRA karo na 37 a matsayin wata dama ga Afrika ta ƙarfafa muryar ta da tasirin ta a fagen sadarwa na duniya.

Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Ƙungiyar Hulɗar Jama’a da Sadarwa ta Duniya, Farfesa Justin Green, ya bayyana cewa ana sa ran wakilan Majalisar Ɗinkin Duniya, Bankin Duniya, Tarayyar Afrika da Hukumar Tarayyar Turai za su halarci taron.

Idris tare da manyan jami’ai a taron
Previous Post

Tinubu ya sha alwashin kawo ƙarshen matsalar tsaro, ya gode wa al’ummar Jigawa kan goyon baya

Next Post

Neja za ta ba Tinubu da Bago babbar nasara a zaɓen 2027 – Idris

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Neja za ta ba Tinubu da Bago babbar nasara a zaɓen 2027 – Idris

Neja za ta ba Tinubu da Bago babbar nasara a zaɓen 2027 - Idris

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!