Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada aniyar sa ta kawo ƙarshen matsalar tsaro a Nijeriya, tare da bayyana cewa gwamnatin sa na ƙara inganta walwala da albashin jami’an tsaro domin ƙarfafa musu gwiwa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Tinubu ya bayyana hakan ne a jiya Talata yayin gangamin jam’iyyar APC a filin wasa na garin Dutse da ke Jihar Jigawa, inda ya ce gwamnatin sa na ƙarfafa rundunar soji da ’yan sanda, tare da biyan su albashi mafi inganci.
Ya tabbatar da cewa Nijeriya za ta yi nasara a kan makiyan zaman lafiya, haɗin kai da cigaba.
Shugaban ya gabatar da kundin manufofin APC mai taken “From Reforms to Prosperity”, wanda ya ƙunshi nasarorin gwamnatin sa da shirye-shiryen da take da su a fannonin ababen more rayuwa, lafiya, noma da tsaro.

Ya kare matakin cire tallafin man fetur, yana mai cewa kuɗaɗen da aka samu daga wannan mataki sun taimaka wajen gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa.
Ya yi alƙawarin ƙara tallafa wa manoman ƙananan gonaki ta hanyar samar musu da lamuni marasa ruwa, injinan noma da inganta hanyoyin ban-ruwa domin tabbatar da wadatar abinci a ƙasar.
Kafin gudanar da gangamin, Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da cibiyar koyon sana’o’i ta ‘Bola Ahmed Tinubu Multi-Purpose Skills Acquisition Centre’ da ‘Renewed Hope Technical Services Centre’, sannan ya ƙaddamar da hanyar Old Police Station zuwa Fadar Mai Martaba Sarkin Dutse mai tsawon kilomita uku da aka mayar titin tagwaye.
Haka kuma, ya ƙaddamar da taraktoci 400 da sauran kayan aikin gona da gwamnatin jihar ta saya domin bunƙasa noman zamani.

A jawabin sa, Gwamna Umar Namadi ya gode wa Tinubu kan ayyukan raya ƙasa da tallafin da jihar ke samu, ciki har da aikin ‘Greater Hadejia Water Project’, kafa kwalejojin ilimi na tarayya a Dutse da Haɗejiya, shirin NELFUND da kuma tallafin ‘Conditional Cash Transfer’ ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da sauran manyan jagororin APC sun buƙaci al’ummar Jigawa su ci gaba da goyon bayan gwamnatin Tinubu, tare da zaɓen ’yan takarar jam’iyyar a zaɓen 2027.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, na daga cikin manyan jigajigan da suka halarci gangamin, tare da gwamnoni, ministoci da sauran shugabannin siyasa daga sassan ƙasar nan.
Tinubu ya gode wa al’ummar Jigawa bisa goyon baya da biyayyar su ga jam’iyyar APC.







