Nijeriya da ƙasar Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) domin ƙarfafa shirye-shirye da inganta ayyukan gudanar da aikin Hajjin shekarar 2027.
Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a yau Talata a babban ɗakin taro na Super Dome da ke Jiddah, ƙasar Saudiyya.
Shugaban NAHCON, Ambasada Isma’il Abba Yusuf, shi ne ya sanya hannu a madadin Nijeriya, yayin da Mataimakin Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dakta Abdulfattah bin Sulaiman Mashat, ya sanya hannu a madadin ƙasar sa.
Yarjejeniyar ta tanadi tsarin da za a bi wajen daidaita shigar Nijeriya cikin aikin Hajjin 2027, ciki har da adadin kujerun da za a ware wa ƙasar, bin dokoki da ƙa’idojin aikin Hajji na Saudiyya, kiyaye wa’adin gudanar da ayyuka, da kuma haɗin gwiwa wajen samar da muhimman hidimomi kamar masauki, sufuri da kiwon lafiya.
Haka kuma, yarjejeniyar za ta ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen biyu wajen magance matsalolin gudanarwa, sa ido kan ingancin ayyukan da ake samarwa da kuma kare walwalar alhazai ‘yan Nijeriya.
Da yake jawabi a wajen bikin sanya hannu kan yarjejeniyar, Shugaban NAHCON, Ambasada Yusuf, ya yaba wa gwamnatin Saudiyya da Ma’aikatar Hajji da Umrah bisa ci gaba da zuba jari wajen inganta kayayyakin more rayuwa da hidimomin aikin Hajji, da kuma ƙoƙarin inganta tsarin gudanar da aikin da kyakkyawar alaƙar aiki da suke ci gaba da yi da Nijeriya.
Ya sake jaddada aniyar NAHCON ta yin aiki tare da hukumomin Saudiyya domin ci gaba da samun nasarorin da aka samu, ta hanyar ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomi da inganta hidimomin da ake bai wa alhazan Nijeriya.
A nasa jawabin, Dakta Mashat ya bayyana cewa Saudiyya ta samu kashi 93 cikin 100 na gamsuwar alhazai da ayyukan da aka gudanar a lokacin Hajjin 2026, inda ya yaba wa Nijeriya bisa gudunmawar da ta bayar wajen cimma wannan nasara.
Ya kuma yaba wa Nijeriya bisa cika wa’adin da aka gindaya wajen shirye-shiryen Hajjin 2027, tare da ƙarfafa NAHCON da ta ci gaba da wannan ƙoƙari.
Taron sanya hannu kan yarjejeniyar ya samu halartar Jakaden Nijeriya a Saudiyya, Ambasada Yakubu Gambo, da wasu membobin Majalisar Dokoki ta Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Aikin Hajji, Hon. Jafar Mohammed, tare da wasu manyan jami’ai.
Bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar, NAHCON za ta yi aiki tare da hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi, kamfanonin shirya aikin Hajji masu lasisi da hukumomin Saudiyya da abin ya shafa domin daidaita shirye-shiryen gudanar da aikin, ƙarfafa sa ido kan ingancin hidimomi da kuma magance matsalolin da ka iya tasowa kafin fara aikin Hajjin 2027.







