Rundunar Sojin Nijeriya ta samu nasarar halaka wasu ’yan ta’adda da dama tare da kuɓutar da mutane 16 da aka yi garkuwa da su, a wasu samamen soji da ta gudanar a jihohin Neja da Kebbi.
Wata sanarwa da Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Birged ta 18, Kyaftin Adebayo Samuel Adewumi, ya fitar a yau ta ce a jiya Laraba ne dakarun sojin suka yi wa wasu ’yan ta’adda kwanton ɓauna a Rijiyan Nagwamatse, da ke Ƙaramar Hukumar Kontagora ta Jihar Neja, inda suka yi nasarar kuɓutar da mutane 16 da ke hannun masu garkuwa da mutane.

Haka kuma, a ranar 3 ga Nuwamba, dakarun sun yi arangama da wasu ’yan ta’adda a kan hanyar da ta taso daga ƙauyen Makuku da ke Ƙaramar Hukumar Sakaba ta Jihar Kebbi, zuwa Tungan Kawo a Ƙaramar Hukumar Rijau ta Jihar Neja.
Bayan musayar wuta, ’yan ta’addan sun arce zuwa cikin daji, yayin da sojojin suka ƙwato wasu makamai da kayayyaki daga hannun su.
Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogin AK-47 guda biyu, bama-baman RPG guda uku, babura 38 da kuma kuɗaɗe sama da naira miliyan 4.7.





