Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci kwamishinonin yaɗa labarai na jihohin da jam’iyyar APC ke mulki da su ƙarfafa haɗin gwiwa tare da daidaita yadda suke isar da saƙonnin gwamnati, domin taimaka wa jama’a su fahimci manufofi da nasarorin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Idris ya yi wannan kira ne a ranar Alhamis a Abuja, yayin wani taro da kwamishinonin, inda ya jaddada cewa ingantacciyar hanyar sadarwa tana da matuƙar muhimmanci wajen gudanar da mulki da hulɗa da jama’a.
Ya ce an tsara Ajandar Sabunta Fata ne domin ƙarfafa tattalin arziki, faɗaɗa damarmaki, inganta ababen more rayuwa da bunƙasa ƙasa.
Ya ƙara da cewa ya zama wajibi ’yan Nijeriya su fahimci manufofin sauye-sauyen gwamnatin, ƙalubalen da ke tattare da su da kuma amfanin da ake sa ran za a samu.
Ya ce: “Ingantacciyar hanyar sadarwa ba zaɓi ba ce kawai. Muhimmin ginshiƙi ne na jagoranci, gudanar da mulki da hulɗa da jama’a.”

Ya buƙaci kwamishinonin da su ƙarfafa hanyoyin sadarwa tsakanin hukumomin Gwamnatin Tarayya da na jihohi, su riƙa musayar sahihan bayanai, tare da amfani da kafafen yaɗa labarai na gargajiya da na zamani wajen isar da saƙonni ga ’yan ƙasa.
Idris ya kuma yi gargaɗi kan yaɗa bayanan ƙarya, yana mai cewa sahihanci, gaskiya da hulɗa da jama’a yadda ya kamata su ne ginshiƙan tabbatar da amincewar jama’a ga gwamnati.
“Babban abin da muke da shi shi ne amincewar jama’a, kuma ba za a iya ci gaba da samun wannan amincewar ba sai ta hanyar sahihanci, tsare gaskiya, daidaito da kuma hulɗa da jama’a yadda ya kamata,” inji shi.
Ministan ya yi kira ga kwamishinonin da su riƙa sauraron ra’ayoyin ’yan ƙasa, fahimtar abubuwan da ke damun su, tare da la’akari da shawarwarin da suke bayarwa wajen tsara dabarun sadarwar gwamnati.
“Sadarwa ingantacciya hanya ce ta musayar saƙonni tsakanin ɓangarori biyu. Dole ne mu kula da abubuwan da ke damun ’yan ƙasa, mu fahimci ra’ayoyin jama’a, tare da tabbatar da cewa shawarwarin su na taimakawa wajen tsara yadda gwamnati ke hulɗa da su,” inji ministan.
Kwamishinonin Yaɗa Labarai 20 daga jihohin da APC ke mulki ne suka halarci taron, inda suka tattauna hanyoyin ƙarfafa sadarwa da daidaita bayanai tsakanin Gwamnatin Tarayya da jihohi, da kuma inganta hulɗa da jama’a.







