Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta kama wani matashi mai suna Umar Ibrahim Gandi Maradun, mai shekaru 22, daga Ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, bisa fitowar sa a wani bidiyo da ya yaɗu a soshiyal midiya, wanda ake ganin ya ƙunshi kalaman da za su iya tunzura rikicin addini.
Rundunar ta bayyana cewa bidiyon ya nuna wani matashi sanye da kayan da ake dangantawa da ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Iƙamatus Sunnah (JIBWIS), yana furta kalaman da ake zargin za su iya barazana ga zaman lafiya da zaman tare tsakanin al’umma.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Talata, Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar ’yan sandan, CSP Ani Iniedu, ya ce rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta tura jami’an leƙen asirin ta domin gano mutanen da ke da hannu a lamarin.
A cewar sanarwar, rundunar ta kuma tattauna da shugabannin JIBWIS na ƙasa da na jiha, inda shugabannin ƙungiyar suka bayyana cewa ba su amince da abin da ake zargin matashin ya aikata ba, sannan suka miƙa shi ga ’yan sanda.
Sanarwar ta ce an kama wanda ake zargin domin gudanar da bincike, inda ta ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Rundunar ta bayyana cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun da ta dace idan bincike ya samar da isassun hujjojin da za su tabbatar da cewa ya aikata laifi a ƙarƙashin dokokin da suka dace.
Rundunar ’yan sandan ta sake jaddada aniyar ta ta kare dukkan ’yan ƙasa ba tare da la’akari da addinin su ba, tare da kiyaye haƙƙin kowane mutum na ’yancin tunani, lamiri da bin addinin da yake so, kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tanada.
Ta yi gargaɗin cewa za ta ɗauki matakin da ya dace bisa doka kan duk wani hali da zai iya tunzura ƙiyayya tsakanin mabiya addinai, haddasa tashin hankali ko barazana ga zaman lafiya.
Haka kuma, rundunar ta buƙaci jama’a da su guji ci gaba da yaɗa bidiyon ko rarraba bayanan da ba a tabbatar da sahihancin su ba, waɗanda za su iya ƙara rura wutar rikicin addini ko kawo cikas ga zaman lafiya.
Sanarwar ta buƙaci jama’a da su kwantar da hankalin su, tare da barin ’yan sanda su kammala binciken su.
Rundunar ta sake tabbatar da aniyar ta ta kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tabbatar da zaman lafiya da doka da oda, da kuma inganta zaman tare a faɗin ƙasar nan.






