Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya ƙaddamar da katafariyar sabuwar hedikwatar kamfanin hadahadar fetur na Northwest Petroleum & Gas Company Limited da ke Victoria Island, Legas, inda ya bayyana ginin a matsayin wani muhimmin cigaba ga ɓangaren man fetur da iskar gas na Nijeriya.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ƙaddamar da hedikwatar a yau yayin wani biki da aka gudanar a Legas, inda ya ce sabon ginin ya nuna irin ƙarfin da kamfanonin cikin gida suke da shi wajen yin gogayya, ƙirƙire-ƙirƙire da kuma samar da ayyuka bisa ƙa’idojin duniya.
Ya ce ginin ya aika da saƙo mai ƙarfi ga masu zuba jari, abokan ciniki da ’yan Nijeriya cewa kamfanin mai na cikin gida yana da shirin ci gaba da kasancewa mai muhimmanci tsawon shekaru masu zuwa, duk da sauye-sauyen da ke faruwa a tsarin makamashi na duniya.
Ya ce: “Mun ji daɗi matuƙa ganin kamfanin cikin gida yana faɗaɗa ayyukan sa da irin wannan ƙwarin gwiwa. Mallakar ’yan Nijeriya dole ne ta kasance tare da ƙarfin ’yan Nijeriya na yin gogayya, ƙirƙire-ƙirƙire da kuma samar da ayyuka.”
Shettima ya danganta sabon jari da ingantaccen aiki da ake samu a ɓangaren man fetur da iskar gas na Nijeriya da sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar, musamman cire tallafin man fetur da sauye-sauyen da aka yi a kasuwar canjin kuɗin waje.
Ya ce sauye-sauyen tattalin arziki na dawo da amincewar masu zuba jari
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce sauye-sauyen sun taimaka wajen magance matsalolin da a baya suke hana zuba jari mai amfani, tare da dawo da amincewar ‘yan kasuwa.
“Daidaita kasuwa yana dawo da amincewar da ‘yan kasuwa ke buƙata domin su zuba jari fiye da abin da zai faru a cikin kwata ta gaba. Dole ne kamfani ya iya yin tsari kafin ya faɗaɗa,” inji shi.
Ya ƙara da cewa samun ƙarin tabbaci kan farashin canjin kuɗi zai taimaka wajen inganta sayen kayayyaki, yanke shawarar zuba jari da kuma ƙara samar da kayayyaki.
Shettima ya tabbatar wa da ‘yan kasuwa cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da samar da yanayin da zai ƙarfafa kasuwanci, bunƙasa fasaha da kuma ɗorewar cigaban tattalin arziki.
Ya jaddada muhimmancin zuba jarin kamfanoni masu zaman kan su wajen samar da ayyukan yi da damar tattalin arziki, yana mai cewa gwamnati ita kaɗai ba za ta iya samar da wadata ba.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya yaba wa Northwest Petroleum & Gas Company Limited saboda gina matsayi mai ƙarfi na kamfanin ɗan Nijeriya a sassa daban-daban na harkar man fetur da iskar gas tun bayan kafuwar sa a shekarar 1998.
A cewar sa, faɗaɗa ayyukan kamfanin zai samar da damarmaki ga matasan Nijeriya, da kuma damar samun horo da ci gaban ƙwarewa, tare da taimakawa wajen gina ƙwarewar da ake buƙata domin ɗorewar masana’antar makamashi ta ƙasar nan.

Ya buƙaci kamfanin da ya tabbatar da cewa amfanin tattalin arzikin ayyukan sa ya wuce hedikwatar sa, ta hanyar ƙara buƙatar ayyukan masu samar da kayayyaki, sufuri, gyare-gyare da sauran hidimomi.
“Babbar cibiyar gudanar da kamfani dole ne ta ƙara inganta aiki, daidaita ayyuka da kuma ƙara samar da ingantaccen aiki a dukkan ayyukan da kuke faɗaɗawa,” inji Shettima.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya taya kwamitin gudanarwa da shugabannin kamfanin, ƙarƙashin jagorancin wanda ya kafa kamfanin kuma Babbar Daraktar sa, wato Misis Winifred Akpani, murnar kammala ginin.
Tun da farko, sai da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana kamfanoni masu zaman kan su a matsayin manyan ginshiƙan cigaban tattalin arziki, tare da sake jaddada aniyar gwamnatin sa ta samar da kyakkyawan yanayi da zai bai wa ‘yan kasuwa damar bunƙasa.
Sanwo-Olu ya yaba wa masu zuba jari masu zaman kan su saboda gudunmawar da suke bayarwa wajen cigaban Legas, musamman a fannonin man fetur da iskar gas, ayyukan kuɗi da gine-gine.
Ya kuma gode wa Mataimakin Shugaban Ƙasa bisa halartar bikin ƙaddamar da ginin, yana mai cewa kasancewar sa a wurin shaida ce ta goyon bayan sa ga cigaban Legas da tattalin arzikin Nijeriya baki ɗaya.
A nata jawabin, Akpani ta ce sabuwar hedikwatar tana wakiltar cigaban da Northwest Petroleum da ya yi, da amincewar sa da makomar Nijeriya da kuma ƙudirin gina kamfani na cikin gida na zamani wanda zai iya gudanar da ayyukan sa bisa manyan ƙa’idoji.
Ta ce: “Wannan gini mai amfani da fasahar zamani alama ce ta jajircewar mu ta dogon lokaci ga makomar Nijeriya. Yana samar da yanayin aiki na zamani da aka tsara domin ƙarfafa haɗin gwiwa, inganta ayyuka, ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire da kuma bai wa ƙwararrun ma’aikatan mu damar yin abin da ya dace wajen tafiyar da kasuwancin mu,” inji ta.
Akpani ta ce makomar masana’antar makamashi za ta ƙara dogara ne kan ƙirƙire-ƙirƙire, fasaha, zuba jari mai ɗaukar nauyi, ƙaƙƙarfan haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar ’yan Nijeriya.
Taron ya samu halartar tsohon Gwamnan Jihar Legas, Akinwunmi Ambode; tsohon Gwamnan Jihar Delta, James Ibori; Daraktar Gudanarwa ta kamfanin Dangote Industries Limited mai kula da harkokin kasuwanci, man fetur da iskar gas, WAEP da takin zamani, Fatima Aliko-Dangote, da sauran manyan ‘yan kasuwa da masu ruwa da tsaki a masana’antu.





