Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da faɗaɗa rundunar Sojin Ƙasa na Nijeriya daga rukunoni (Division) takwas zuwa 12, tare da ɗaukar ƙarin sababbin sojoji 28,000, a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa tsarin tsaron ƙasar da kuma inganta ƙwarewar rundunar wajen gudanar da ayyukan ta.
Sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar a ranar Alhamis ta bakin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ta bayyana cewa manufar wannan mataki ita ce ƙara wa Rundunar Sojin Nijeriya ƙarfin fuskantar sababbin ƙalubalen tsaro da ƙarfafa kariyar ƙasa.
A cewar sanarwar, faɗaɗa rundunar tana daga cikin ci gaba da saka hannun jari da gwamnatin Tinubu take ke yi a fannin soji, wanda ya haɗa da sayo muhimman makamai da kayan aikin soja, inganta walwalar jami’ai da sojoji, da kuma ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen bunƙasa ƙwarewar rundunar da zamanantar da ita.
A ƙarƙashin sabon tsarin, rundunar Sojin Ƙasa na Nijeriya za ta gudanar da ayyukan ta ta hanyar rukunoni 12 a faɗin ƙasar nan. Za a kafa sababbin rukunoni huɗu a Makurdi da Ilorin da Jalingo da kuma Benin City, yayin da za a sake tsara rukunonin da ake da su a yanzu.
Hedikwatar rukunonin za su kasance a Kaduna da Ibadan da Jos da Makurɗi da Fatakwal da Maiduguri da Sakkwato da Ilorin da Jalingo da Legas da Inugu da kuma Birnin Benin, inda kowanne rukuni zai kula da jihohin da aka ware masa a yankin aikin sa.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce sababbin rukunonin za su inganta tsarin jagoranci da bayar da umurni, su ba wa rukunonin yankuna damar yanke shawarar gudanar da ayyuka cikin sauri, su ƙarfafa tsaron kan iyakoki, su inganta kariyar muhimman cibiyoyin ƙasa, su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’addanci da sauran matsalolin tsaron cikin gida, tare da tabbatar da saurin martanin sojoji ga duk wata barazana da ka iya tasowa a faɗin Nijeriya.
Za a aiwatar da sabon tsarin rundunar ne a matakai biyu. Mataki na farko, wanda ya haɗa da kafa Runduna ta 5 a Makurɗi, Runduna ta 9 a Ilorin, da Runduna ta 10 a Jalingo, tare da sake fasalin rukunonin da ake da su, ana sa ran kammala shi nan da watan Satumba 2026.
Mataki na biyu kuwa, wanda ya haɗa da kafa Runduna ta 83 a Birnin Benin da kuma ci gaba da sake fasalin rundunar Sojin Ƙasa, ana sa ran kammala shi nan da watan Disamba 2026.
Shugaba Tinubu ya yaba wa Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Ibrahim Shuaibu, da sauran hafsoshi da sojojin rundunar bisa jajircewar su da ƙwarewar su da kuma sadaukar da kan su wajen kare ikon Nijeriya da cikakken yankin ta.
Har ila yau, ya sake jaddada aniyar gwamnatin sa ta ci gaba da zuba jari a rundunar sojin ƙasar domin tabbatar da cewa tana da isassun kayan aiki, tana da ƙwarin gwiwa, kuma tana da cikakken ƙarfin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.







