Allah ya yi wa fitacciyar ‘yar siyasar nan kuma mai fafutukar ayyukan jinƙai, sannan jagorar ƙungiyoyin ƙwadago kuma marubuciya, Hajiya Mairo Habib, rasuwa. Ta rasu a Kaduna a yau Asabar bayan ta yi fama da rashin lafiya.
Marigayiyar ta taɓa rike muƙamin Mataimakiyar Shugabar Ƙungiyar Ma’aikatan Masana’antar Masaƙu ta Nijeriya.
Haka kuma ta nemi takarar gwamnan Jihar Kaduna sau biyu, sannan a zaɓen shekarar 2003 ta kasance mataimakiyar ɗan takarar shugaban ƙasa, Fasto Chris Okotie, a ƙarƙashin jam’iyyar Justice Party.
Hajiya Mairo Habib ta kuma yi aiki a matsayin Shugabar Hukumar Gudanarwar Kwalejin Fasahar Kiwon Lafiya ta Kafanchan da ke Jihar Kaduna.
Ta yi karatu a makarantar UMA Mission School, sannan ta samu digiri a fannin Fine Arts daga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya. Daga bisani kuma ta samu takardar shaidar karatun digiri na biyu (Postgraduate Diploma) daga Jami’ar Leeds da ke Birtaniya.
A matsayin ta na ƙwararriyar mai zanen tufafi, ta haɗa fasaha da gwagwarmayar kare haƙƙin ma’aikata da ayyukan jinƙai a tsawon rayuwar ta.
A cikin al’ummar ta ta riƙe sarautun gargajiya da suka haɗa da Sarauniyar Gamji da kuma Garkuwar Unguwar Rimi a Jihar Kaduna.
Hajiya Mairo ce marubuciyar wani fitaccen littafi mai suna ‘Househelps, the Necessary Evils’ wanda ta rubuta kan masu aikatau a gida. An buga shi a 1994.
Marigayiyar ta rasu ta bar mijin ta da ‘ya’ya huɗu.







