Tun bayan naɗa Olayemi Cardoso matsayin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) cikin watanni huɗu na ƙarshen 2023, bai tsaya ɓata lokaci ba sai ya duƙufa kan gagarumin aikin saisaita manufofin kuɗi na Nijeriya, domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa wanda ya gada a cikin wani mawuyacin hali. Daga lokacin da Cardoso ya kama aiki zuwa 2026, ya samu nasarorin da za a iya tantance manyan su kusan hamsi, waɗanda kowane ɗayan su ya yi tasiri sosai wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya a fannoni daban-daban.
A baya na lissafa muhimman nasarori har guda 20 da CBN ya samu a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Olayemi Cardoso, cikin 2025. A makon jiya kuma na bayyana wasu muhimman nasarori guda 25 da CBN ya samu a cikin watanni shidan farkon 2026.
A yau kuma zan ɗan taƙaita wajen bayyana kaɗan daga tasirin nasarorin CBN a fannoni daban-daban na bunƙasa tattalin ƙasar nan. Waɗanda nasarori ko tasiri na CBN a fannonin kuwa a zahiri suke, ba wai kawai alƙaluman ƙididdigar bayanai ba ne.
Da farko dai tattalin arzikin Nijeriya ya kai gejin naira tiriliyan 441.5 a shekarar 2025, daga Naira tiriliyan 372.8 da ya kasance a 2024.
Sannan adadin rabon kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi na kowane wata ya ninka sau biyu, inda yanzu ya haura Naira tiriliyan 2, daga ƙasa da Naira tiriliyan 1 da yake a shekarar 2023.
Malejin hauhawar farashin kayayyaki da malejin tsadar rayuwa sun ragu fiye da rabi, daga kashi 34.80 cikin 108 a watan Disamba, 2024 zuwa kashi 15.93 cikin ɗari a watan Mayu, 2026.
Adadin ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya ya haura dala biliyan 50 a shekarar 2026, wanda shi ne mafi yawa girma cikin shekaru 17 da suka gabata.
Haka nan kuma fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba zuwa ƙasashen waje ya kai adadin dala biliyan 6.1 a shekarar 2025, wanda ya nuna ƙarin kashi 11.5 cikin 100 idan aka kwatanta da 2024.
Sai kuma ƙima da darajar ji hannun jari (ASI) ya kai maki 250,000 a shekarar 2026, daga kusan 55,000 a da ya kasance a watan Mayu, 2023. Haka kuma, darajar kasuwar hannayen jari ta ƙaru kusan sau biyar zuwa naira tiriliyan 145.
Jimillar kuɗaɗen harajin gwamnatin tarayya da aka tara ya tashi daga naira tiriliyan 19.9 a shekarar 2023 zuwa naira tiriliyan 28.3 a shekarar 2025.
Jarin da ya shigo Nijeriya daga ƙasashen waje ya ƙaru da kusan kashi 90 cikin ɗari, daga dala biliyan 12.32 a shekarar 2024 zuwa dala biliyan 23.22 a shekarar 2025.
Nijeriya ta samu kashi 40 cikin ɗari na jimillar ƙimar manyan shawarwarin saka hannun jari a fannin haƙo ɗanyen mai a Afirka, tsakanin 2024 da 2025, wanda ya haura dala biliyan 8.
Adadin kuɗin da ake kashewa wajen shigo da fetur daga ƙasashen waje ya ragu daga kusan naira tiriliyan 2.3 a rubu’in farko na 2025 zuwa ƙasa da naira biliyan 90 a rubu’in farko na 2026. Wannan kuwa babbar nasara ce mai tasiri sosai.
Adadin yawan fetur da ake samu, wato ake tacewa a cikin gida yanzu yana kusa da kaiwa lita miliyan 50 a kowace rana, wanda a shekarar 2023 kusan ko adadin cikin bokitin fenti ba a tacewa. Tabbas wannan ci gaba ne sosai ga tattalin arzikin Nijeriya.
Yawan ɗanyen mai da dangin sa da ake samarwa ya ƙaru da ganguna 400,000 a kowace rana tsakanin 2023 da 2025, ciki har da adadin mafi yawan mai da ake haƙowa a yankunan ƙasa cikin shekaru 20.
Jimillar iskar gas da Nijeriya ke samarwa ta ƙaru da fiye da kashi 11 cikin 100 tun daga 2023, inda yanzu ya kai kusan ƙafa biliyan 7.63 na iskar gas a kowace rana.
Ƙaruwar tattalin arziki ya sa an kafa Gidauniyar Tallafa wa Ɗaliban Manyan Makarantu (NELFUND), inda tallafa wa ɗalibai sama da miliyan 1.5 a cibiyoyin ilimi 301, waɗanda ya raba kusan naira biliyan 300 a matsayin kuɗin rancen maida hankali ga karatu da alawus na kula da rayuwa ga ɗalibai masu ɗimbin yawa.
An sauya sama da motoci 100,000 an daga masu amfani da fetur zuwa masu amfani da gas (CNG) ƙarƙashin Shirin Shugaban Ƙasa na CNG, inda aka zuba jari sama da dala biliyan biyu, tare da samar da ayyukan yi ga kusan mutum 100,000.
A shekarar 2025, Nijeriya ta fita daga jerin ƙasashen da FATF ta sa-idon kaffa-kaffa wajen hadahadar kuɗi da ita, wanda hakan ya nuna irin nasarar da CBN ya samu ce wajen yaƙi da haramtacciyar hanyar hadahadar kuɗi daƙile hanyoyin tallafa wa ta’addanci.
Kuɗaɗen shiga daga fannin ma’adinai masu ƙarfi sun ƙaru da fiye da kashi 337 cikin ɗari, wato daga naira biliyan 16 a shekarar 2023 zuwa sama da naira biliyan 70 a shekarar 2025.
Lallai daga jin waɗannan kaɗan daga cikin tasirin da manufofin kuɗi da tsare-tsare na CBN a ƙarƙashin Gwamna Cardoso, bankin ya cancanci a riƙa kambama shi da babbar murya, ta hanyar ci gaba da yi masa taken sa, wato jagoran bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya.






