• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, October 1, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Aikin jarida cikin ɗa’a da adalci zai taimaki makomar Arewa, cewar Ministan Yaɗa Labarai

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
July 6, 2026
in Labarai
A A
0
Aikin jarida cikin ɗa’a da adalci zai taimaki makomar Arewa, cewar Ministan Yaɗa Labarai
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana gabatar a wajen Babban Taron Manema Labarai na Arewa (Arewa Media Summit) na farko wanda aka gudanar a Kano a yau Litinin

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana gabatar a wajen Babban Taron Manema Labarai na Arewa (Arewa Media Summit) na farko wanda aka gudanar a Kano a yau Litinin

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana gabatar a wajen Babban Taron Manema Labarai na Arewa (Arewa Media Summit) na farko wanda aka gudanar a Kano ranar Litinin.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga ƙwararrun ‘yan jarida da ke Arewacin Nijeriya da su rungumi aikin jarida mai ɗa’a, adalci da kishin ƙasa, yana mai cewa makomar yankin ba za ta dogara kacokam kan ayyukan raya ƙasa ba, har ma da irin labaran da ake bayarwa game da al’ummar sa da kuma damar da yake da ita.

Ministan ya faɗi haka ne cikin muhimmin jawabin da ya gabatar a wajen Babban Taron Manema Labarai na Arewa (Arewa Media Summit) na farko wanda aka gudanar a Kano ranar Litinin.

Ministan ya ce: “Makomar Arewacin Nijeriya ba za ta dogara kawai kan ingancin hanyoyin mu, gonakin mu ko masana’antun mu ba. Za ta kuma dogara ne kan ingancin tunanin mu da kuma irin labaran da muke bayarwa game da kan mu.”

 

Ya ce kafafen yaɗa labarai suna ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan da ke saisaita ra’ayin jama’a, jawo hannun jari, kare al’adu, ƙarfafa dimokiraɗiyya da kuma inganta haɗin kan ƙasa.

 

A cewar sa, taken taron mai cewa “Government-Citizen Accord: Accountability, Responsibility and Ethical Media Practice” yana tunatar da jama’a cewa dimokiraɗiyya tana aiki ne yadda ya kamata idan gwamnati tana yin abin da ya rataya a wuyan ta, jama’ar ƙasa suna taka rawar su yadda ya dace, sannan kafafen yaɗa labarai suna gudanar da aikin su da kundin tsarin mulki ya rataya musu cikin ƙwarewa, adalci da riƙon amana.

 

“Waɗannan su ne abokan hulɗar da ake buƙata wajen gina Nijeriya mai zaman lafiya, cigaba da haɗin kai,” inji shi.

 

Ministan ya bayyana cewa duk da irin damar da fasahar zamani ta samar wajen sadarwa da bunƙasa tattalin arziki, ta kuma kawo ƙaruwar yaɗuwar labaran ƙarya da bayanan da ake yaɗawa domin ruɗar da jama’a.

 

Idris ya ce: “Sau da yawa, gaskiyar magana ba ta kai saurin yaɗuwa kamar ƙarya ba. Saboda haka, aikin jarida na ƙwararru bai taɓa zama mai muhimmanci kamar yanzu ba. Dole ne aikin jarida na gaskiya ya ci gaba da tsayawa kan ginshiƙan daidaito, adalci, tantance sahihancin bayanai da kuma ɗaukar nauyin abin da ake wallafawa.”

 

Bugu da ƙari, Ministan ya sake jaddada aniyar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kare ‘yancin aikin jarida da kuma ci gaba da kyakkyawar hulɗa da kafafen yaɗa labarai.

 

Ya ce: “Mun ƙudiri aniyar kare ‘yancin aikin jarida a matsayin ginshiƙin dimokiraɗiyya tare da samar da yanayin da zai bai wa ‘yan jarida damar gudanar da aikin su cikin ƙwarewa. Dimokiraɗiyya tana bunƙasa ne idan jama’ar ƙasa suna samun sahihan bayanai, kuma kafafen yaɗa labarai suna gudanar da aikin su na sa ido cikin gaskiya da riƙon amana.”

 

Ministan ya kuma buƙaci ‘yan jarida da su riƙa ba da cikakken hoto game da Arewacin Nijeriya ta hanyar bayyana nasarorin yankin tare da ƙalubalen da yake fuskanta.

 

Ya ce: “Arewacin Nijeriya ya fi abin da ake dangantawa da matsalar tsaro nesa. Yanki ne da ke cike da ‘yan kasuwa, manoma, masu ƙirƙire-ƙirƙire, masu bincike, masu fasaha da matasa da ke sauya al’ummomin su a kowace rana. Waɗannan labarai ma sun cancanci a ba su muhimmanci tare da ƙalubalen da ake fuskanta domin su ba da cikakke kuma ingantaccen hoto game da yankin mu,” inji shi.

 

Da yake bayyana nasarorin da ake samu ƙarƙashin Ajandar Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda), Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya tana zuba jari sosai a fannonin gine-ginen more rayuwa, ilimi, tsaro da sauye-sauyen tattalin arziki domin buɗe sababbin damarmaki a faɗin ƙasar nan.

 

Ya ambaci ayyukan manyan tituna guda huɗu na “Legacy Highway Projects”, kafa Ma’aikatar Bunƙasa Kiwo ta Tarayya, shirin NELFUND na lamunin karatun ɗalibai, da kuma zuba jari a layukan dogo, makamashi da harkokin sufuri a matsayin wasu daga cikin muhimman tsare-tsaren da ke haifar da cigaba, musamman a Arewacin Nijeriya.

 

Ministan ya bayyana manyan nasarori guda biyu da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta samu, wato kafa makarantar koyar da yaɗa labarai (International Media and Information Literacy Institute, IMILI) da kuma ƙaddamar da dandalin Digital Switch Over (FreeTV).

 

Ya ce, “Waɗannan shirye-shirye za su ƙarfafa aikin jarida mai ɗa’a, faɗaɗa damar samun ingantaccen watsa shirye-shirye, samar da ayyukan yi, bunƙasa shirye-shiryen cikin gida da kuma sanya Nijeriya ta zama jagora wajen yaƙi da yaɗa labaran ƙarya da bayanan bogi.”

 

A yayin da yake kira ga masu aikin yaɗa labarai da su taimaka wajen gina kyakkyawar makoma ga yankin, Idris ya ce: “Ku ba da labaran masu ƙirƙire-ƙirƙire. Ku ba da labaran manoman mu. Ku ba da labaran ‘yan kasuwar mu. Ku riƙa ba da labaran da ke ƙarfafa gwiwa ba tare da kauce wa gaskiya ba. Ku riƙa ba da labaran da ke haɗa kan jama’a maimakon rarraba su.”

 

Taron farko na “Arewa Media Summit”, wanda Alhaji Abdulaziz Abdulaziz ya shirya, ya haɗa ‘yan jarida, masu watsa shirye-shirye, masu shirya finafinai, masu ƙirƙirar abubuwan dijital, masana, ƙwararrun harkokin sadarwa, da masu tsara manufofi.

 

Daga cikin manyan baƙi da suka halarci taron akwai Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf; Gwamnan Jihar Yobe da Sakataren Gwamnatin Jihar, Dakta Mohammed Goje, ya wakilta; Gwamnan Jihar Kebbi da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Yakubu Ahmed BK, ya wakilta; Ministan Bunƙasa Kiwo, Idi Mukhtar Maiha; Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga; Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Kafafen Sada Zumunta, Dada Olusegun; Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya; da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kaduna, Ahmed Maiyaƙi, tare da sauran manyan baƙi.

Tags: aikin jaridaArewa Media SummitKanoMohammed IdrisTaron Manema Labarai na Arewa
Previous Post

Yadda nasarorin da CBN ya samar suke ci gaba da tasiri a fannonin tattalin arziki daban-daban daga 2023 zuwa 2026

Next Post

Aikin jarida cikin ɗa’a da adalci zai taimaki makomar Arewa, cewar Ministan Yaɗa Labarai

Related Posts

Nijeriya ta gyara tafiyar ta, yanzu zamanin wadata ya zo – Tinubu
Labarai

Nijeriya ta gyara tafiyar ta, yanzu zamanin wadata ya zo – Tinubu

October 1, 2026
Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya
Kiwon Lafiya

Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya

September 30, 2026
Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Next Post

Aikin jarida cikin ɗa'a da adalci zai taimaki makomar Arewa, cewar Ministan Yaɗa Labarai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!