Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya soke lasisin gudanar da ayyukan hadahadar wasu ƙananan bankuna (Microfinance Banks) guda 46 a faɗin ƙasar.
Wannan wani babban mataki ne da CBN ya ɗauka na tabbatar da ɗorewar tsarin kuɗi da kuma kare kuɗaɗen masu ajiya.
Soke lasisin, wanda zai fara aiki daga yau ɗin nan, ranar 1 ga Yuli, 2026, wanda kuma Gwamnan Babban Banki, Olayemi Cardoso ya amince da shi ne bisa ikon da aka bai wa CBN a ƙarƙashin sashe na 12 da na 13 na Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Kuɗi (BOFIA) ta shekarar 2020.
Daga cikin bankunan da abin ya shafa akwai irin su Minji-Se Churchill MFB, Merchant MFB, Janmaa MFB, Busu MFB, Gold MFB, Zain MFB (wanda a baya ake kira Dawakin Tofa MFB), Bompai MFB, Ajwa MFB (wanda a baya ake kira Gezawa), NOW NOW DIGITAL MFB, Crystabel Microfinance Bank, Chanelle MFB, Abia SME MFB, Kamba MFB, Iwade MFB da Winview MFB.
A cewar CBN a ranar Laraba, waɗannan cibiyoyin sun rasa lasisin su ne saboda sun kasa cika ƙa’idojin da ake buƙata domin ci gaba da kasancewa cibiyoyin kuɗi masu lasisi.
CBN ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne sakamakon wasu matsaloli da suka haɗa da rashin isassun kadarori da za su iya biyan basussuka, rufe ayyuka ba tare da amincewa ba, rashin gudanar da aiki da dakatar da harkokin ba da hidimar kuɗi, rashin fara aiki cikin watanni 12 bayan amincewar lasisi, da kuma rashin cika mafi ƙarancin jarin da ake buƙata.
Sanarwar soke lasisin wadda ke cikin sanarwar da Muƙaddashin Daraktan Sashen Hulɗa da Jama’a na CBN, Hajiya Hakama Sidi-Ali, ta fitar, ta ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da yake yi na ƙarfafa sa-ido kan harkar kuɗi, tabbatar da bin dokoki da kuma tabbatar da cewa cibiyoyi masu ƙarfi kaɗai ne za su ci gaba da aiki a tsarin kuɗin ƙasar nan.
CBN ya ce matakin zai kuma taimaka wajen kare masu ajiya tare da ƙarfafa amincewa da harkar banki a Nojeriya, musamman a lokacin da ake ƙara tsaurara bincike da sa-ido kan ƙananan cibiyoyin kuɗi.
Sannan CBN ya sake jaddada cewa yana kan gagarumin aikin sa na tabbatar da ingantaccen tsarin kuɗi mai aminci da ɗorewa, tare da nanata cewa zai ci gaba da amfani da matakan sa-ido da dokoki idan ya zama dole, domin kare amincewar jama’a da kuma tabbatar da daidaiton harkar kuɗi.
Da wannan sabon mataki, CBN ya aika da saƙo mai ƙarfi ga masu gudanar da harkokin kuɗi cewa bin ƙa’idoji, samun isasshen jari da kuma ingantaccen tsarin aiki, ba abubuwa ne da za a yi sakaci da su ba a ƙarƙashin tsarin sa-ido da bibiyar bankuna, manya da ƙananan cibiyoyin hadahadar kuɗi a Nijeriya.







