Gagarumin aikin ci gaba da manyan nasarorin da ake samu ta hanyoyin tsare-tsaren harkoki da manufofin kuɗi a ƙarƙashin Babban Bankin Nijeriya (CBN) bisa jagorancin Gwamna Olayemi Cardoso, sun ƙara haskaka darajar bankin a duniya.
Hakan ya ƙara tabbata ne, yayin da CBN ya lashe kambin kyautar gwarzon Manyan Bankuna na duniya da ake gudanarwa a duk shekara.
A wurin gagarumin taron karramawar wanda aka shirya ranar Laraba, 10 ga Yuni a Landan, a cikin sa yayin jawabin karɓar lambar yabo ta Babban Bankin Shekara a madadin Babban Bankin Nijeriya (CBN), Cardoso ya ce,
“Mun karɓi wannan yabo cikin tawali’u. Ba mu ɗauki wannan kyauta a matsayin mun kai ƙarshen gaci ba, sai dai a matsayin wani ƙarin ƙwarin gwiwa da za ta sa mu ci gaba da gudanar da muhimman ayyukan da ke gaban mu.”
Ko da yake akwai sauran manyan ayyuka a gaba, babu wanda zai iya musanta cewa CBN ƙarƙashin jagorancin Cardoso ya samu gagarumar nasara tun bayan da ya karɓi ragamar babban bankin a lokacin da yake cikin mawuyacin hali da matsaloli masu yawa da girman gaske.
Waɗannan nasarori sun fi ɗaukar hankali musamman a lokacin da duniya ke fama da ruɗani da rashin tabbas, tare da manyan sauye-sauyen siyasa da tattalin arziki a duniya.
Cardoso ya bayyana a wajen taron karramawar cewa wannan nasara ta samo asali ne daga ƙoƙari da sadaukarwar tawagar sa a CBN.
Ya ce: “Ina karɓar wannan lambar yabo ne a madadin Hukumar Gudanarwa, shugabanni da ma’aikatan CBN. Fiye da komai, wannan lambar yabo ta mutanen da suke aiki a wannan hukuma ce, waɗanda ke gudanar da aikin su cikin gaskiya, ƙwarewa da cikakkar sadaukarwa ga hidimar jama’a.”
Da yake ci gaba da jawabi, Cardoso ya yi waiwaye kan tafiyar da ta kai CBN ga samun wannan yabo a duniya tare da jaddada muhimmiyar rawar da manyan bankunan ƙasa ke takawa a tsarin tattalin arziki.
A cewar sa: “Nauyin da aka ɗora wa manyan bankunan ƙasa nauyi ne mai matuƙar muhimmanci da ya ƙunshi kare amincewar jama’a, tabbatar da daidaiton tattalin arziki da samar da yanayin da tattalin arziki da al’umma za su bunƙasa.”
Matsalolin da suka dabaibaye babban bankin a shekarar 2023 da kuma matakan da Cardoso da tawagarsa suka ɗauka domin gyara shekaru na rashin ɗa’a da kauce wa ƙa’idojin gudanar da harkokin kuɗi sun fito fili a rahoton da ya sanar da zaɓen CBN a matsayin Babban Bankin Shekara.
Rahoto naƙalto tsohon gwamnan CBN, kuma Mai Martaba Sarkin Kano a yanzu, Muhammadu Sanusi II yana cewa, “lokacin da Shugaban Ƙasa Bola Tinibu ya hau mulki a watan Mayun 2023, ya gaji tattalin arzikin da ke gab da faɗawa cikin matsananciyar hauhawar farashi da kuma matsalar durƙushewar harkokin gwamnati.
Sanusi ya ce naira ta kasance ta riƙa faɗuwa cikin sauri yayin da hauhawar farashi ke ƙaruwa wata bayan wata, sakamakon rasa ‘yancin cin gashin kan CBN da kuma sassaucin manufofin kuɗi a lokacin gwamnatin da ta gabata. Ya kuma bayyana cewa Nijeriya na dab da faɗawa cikin halin da ƙasashen Venezuela da Zimbabwe suka shiga duk a wancan lokaci.
A cikin shekaru uku kacal, ta hanyar dagewa kan cin gashin kai, bin ƙa’idojin shugabanci nagari, gaskiya da kuma manufofin kuɗi na zamani, Cardoso da tawagar sa sun samu nasarar tsamo tattalin arzikin ƙasar nan daga mawuyacin hali.
A lokacin, tattalin arzikin ya kasance cikin matsin-lamba sakamakon hauhawar farashi, raguwar ajiyar kuɗaɗen waje, rashin bayyana gaskiya a manufofin kuɗi da rahotanni, ɗimbin bashin alfarma da CBN ya riƙa ba gwamnati, wato ‘Ways and Means’, tarin basussukan canjin kuɗi da suka daɗe da kuma babban giɓi tsakanin farashin dala na hukuma da na kasuwar bayan fage.
Ƙarƙashin jagorancin Cardoso, da kuma aiwatar da ingantacciyar manufar rage hauhawar farashi, CBN ya jagoranci wani shiri na rage hauhawar farashi wanda ya sa adadin ya sauka zuwa kusan kashi 15 cikin 100. Haka kuma ajiyar kuɗaɗen waje ta karu zuwa sama da dala biliyan 50, abin da ke ba Nijeriya kariyar shigo da kayayyaki na fiye da watanni goma.
Har ila yau, giɓin da ke tsakanin farashin canjin kuɗi na hukuma da na kasuwar bayan fage ya ragu zuwa kusan kashi 2 cikin 100 daga kashi 60 cikin 100, yayin da aka samu ingantaccen yanayin tattalin arziki, kyakkyawan haɗin kai tsakanin manufofin kuɗi da na gwamnati, sake ƙarfafa ɓangaren bankuna da kuma dawo da amincewar masu zuba jari.
Waɗannan nasarori sun taimaka sosai wajen cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da ke cikin “Grey List”, waɗanda duniya ke yi wa kallon-hadarin-kaji.
Waɗannan nasarori ne suka sa aka bai wa CBN wannan gagarumar karramawa.
Da yake bayyana dalilan zaɓen CBN a matsayin Babban Bankin Shekara, babban editan mujallar, Christopher Jeffrey, ya ce an karrama bankin ne saboda sauye-sauyen manufofin kuɗi da suka maye gurbin tsoffin tsare-tsare tare da haifar da manyan ci gaba a tattalin arzikin Nijeriya.
Ya ƙara da cewa waɗannan sauye-sauye sun bai wa CBN damar aiwatar da tsauraran matakan kuɗi tare da gyaran kasuwar canjin kuɗi. Wata babbar nasara kuma ita ce biyan sama da dala biliyan 7 na basussukan da suka daɗe suna jiran biya.
Mujallar ta kuma bayyana cewa a matsayin wata shaida ta ƙoƙarin inganta tsarin aikin sa, CBN ya aiwatar da gyare-gyare a fannin shugabanci da bayyana gaskiya. Bugu da ƙari, shirin ƙarfafa jarin bankuna, zamanantar da tsarin biyan kuɗi da kuma cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da ɗari-ɗari, tababa ko shakkun mu’amalar kuɗaɗe da su bisa umarnin Hukumar FATF, sun taimaka wajen dawo da amincewar masu zuba jari da jama’a, wanda ya sa CBN ya cancanci wannan karramawa ta duniya.
Yabo da jinjina sun kuma ƙara fitowa daga wasu hukumomi, musamman Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF) wanda ta yaba wa gyare-gyaren da CBN ya yi, yana mai cewa daraktocin IMF sun yi maraba da matakan da aka ɗauka domin ƙara ajiyar kuɗaɗen waje da kuma ƙarfafa amincewa da kasuwa a Nijeriya.
IMF ya kuma yaba da gyaran kasuwar canjin kuɗi, wanda ya taimaka wajen gano ainihin farashi da ƙara wadatar kuɗaɗen musaya.
A bara kuma, an naɗa Cardoso a matsayin Gwarzon Gwamnan Babban Bankin Afirka na Shekara a wajen bikin lambar yabo na ‘The Banker Awards’, saboda gyare-gyaren da yake jagoranta.
Masu shirya bikin sun yaba da nasarorin da ya samu da kuma rawar da CBN ke takawa wajen gyara matsalolin kasuwa da mayar da tattalin arzikin Nijeriya kan hanyar ci gaba mai ɗorewa.
A cikin gida kuwa, Cibiyar Bunƙasa Tattalin Arziki da Sauye-sauyen Manufofin Kuɗi (CEGMR) ta yaba wa CBN kan yadda yake tafiyar da manufofin kuɗin ƙasar.
Daraktan cibiyar ya ce: “Manufar kuɗi ba sihiri ba ce, amma daidaito da jajircewa suna haifar da sakamako. Jajircewar CBN wajen bin tsari da amfani da kayan aikin manufofin kuɗi na zamani yanzu yana bayyana a raguwar hauhawar farashi, daidaituwar canjin kuɗi da kuma karuwar ajiyar kuɗaɗen waje.”
Duk da cewa nasarorin ba su da wata shakka, abubuwa biyu sun fito fili daga rahoton mujallar ‘Central Banking’. Na farko shi ne cikakken goyon bayan da Sanusi Lamido Sanusi ya nuna, wanda ba a san shi da yawan yaba wa mutane ba tare da dalili ba.
Na biyu kuwa shi ne jaddadawar Cardoso cewa har yanzu akwai sauran aiki a gaba. Bayan kammala aikin sake ƙarfafa bankuna cikin nasara, Cardoso na mai da hankali wajen tabbatar da cewa ba a lalata ribar da aka samu daga wannan shiri ba.
A ranar da aka gudanar da bikin karɓar lambar yabo a Landan, CBN ta fitar da sabbin ƙa’idoji kan bayar da lasisi da kuma kula da Kamfanonin Rukunin Harkokin Kuɗi (Financial Holding Companies – HoldCos) a Nijeriya.
Takardar da aka fitar ranar 10 ga Yuni, 2026 mai lamba FPR/DIR/PUB/CIR/001/017, wadda Daraktar Sashen Manufofi da Tsare-tsaren Kuɗi, Dokta Rita Sike ta sanya wa hannu, tana ɗauke da taken “Daftarin Sabunta Ƙa’idojin Bayar da Lasisi da Kula da Kamfanonin ‘Financial Holding Companies’ a Nijeriya.”
Takardar ta gabatar da muhimman shawarwari kan ware ayyuka daban-daban (Ring-Fencing Operations), buƙatun jari, tsarin shugabanci da kuma tuntuɓar jama’a, domin ƙara tabbatar da zaman lafiyar ɓangaren bankuna da kare kuɗaɗen masu ajiya.
Sabbin ƙa’idojin sun tanadi cewa lallai dole ‘HoldCos’ su mallaki aƙalla kashi 51 cikin 100 na hannun jari a kowane reshe da ke ƙarƙashin su, tare da ƙarin buƙatun jari domin tabbatar da zaman lafiyar tsarin kuɗi.
Har ila yau, CBN na ci gaba da tabbatar da aiwatarwa da sa ido kan sabon kundin dokokin kasuwar canjin kuɗi domin ƙara gaskiya, faɗaɗa mahalarta kasuwa, tsaurara ƙa’idojin tattara bayanai da kuma ƙarfafa sa-ido a kasuwar EFEM.
Babu shakka ladar aiki tuƙuru da Olayemi Cardoso da tawagar sa suka yi shi ne ƙarin aiki, kuma alamu sun nuna cewa sun ƙudiri aniyar ci gaba da wannan tafiya domin cimma ƙarin nasarori.







