Dakarun Runduna ta 12 ta Sojojin Nijeriya ƙarƙashin Runduna ta 2 sun kuɓutar da mutum biyu da aka sace bayan gaggawar da suka yi wajen mayar da martani ga wani harin sace mutane a garin Egbe, Ƙaramar Hukumar Yagba ta Yamma a Jihar Kogi.
Muƙaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojoji, Laftanar Hassan Abdullahi, ya bayyana a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a wannan Laraba cewa lamarin ya faru ne a daren ranar 3 ga Yuni, 2026, lokacin da ’yan ta’adda suka kutsa wani gida da ke kusa da Makarantar Solid Rock a Ijalu, Egbe, suka yi garkuwa da mutum biyar daga iyali guda, ciki har da wata mata, jaririn ta da wasu mutum uku.
Ya ce: “Da samun rahoton neman agaji, nan take dakarun suka tashi tare da haɗin gwiwar membobin Kungiyar Masu Tsaron Sa-kai ta Nijeriya (VGN), inda suka fara bin sawun ’yan ta’addan ta hanyar da suka bi wajen tserewa.
“Matsin lambar da jami’an tsaro suka ci gaba da yi ya tilasta wa ’yan ta’addan yin watsi da Misis Adekemi Idowu da jaririn ta mai watanni shida a yankin Oro kafin su tsere zuwa wuraren da ke kewaye.”
Abdullahi ya ce an mayar da waɗanda aka kuɓutar lafiya zuwa gidan su, yayin da dakarun “ke ci gaba da gudanar da tsauraran ayyukan bincike domin ceto sauran mutanen da aka sace tare da kama waɗanda suka aikata laifin.”
Ya ƙara da cewa: “Sojojin Nijeriya na ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, kuma suna kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai cikin lokaci domin tallafa wa ayyukan tsaro da ake gudanarwa.”






