Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya yi kira ga maniyyata aikin Hajjin bana da su kiyaye ɗabi’u nagari waɗanda za su fito da martabar Nijeriya fili, sannan su kasance jakadu nagari ga ƙasar su yayin gudanar da ibada a Ƙasa Mai Tsarki.
Shettima ya bayyana maniyyata a matsayin wakilan Nijeriya a idon duniya, inda ya buƙace su da su nuna kyakkyawar ɗabi’a ta hanyar bin dokoki da oda na ƙasar Saudiyya.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bayyana hakan ne a yau Lahadi, yayin da yake ƙaddamar da jigilar maniyyata ta farko na shekarar 2026 a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Ya nanata cewa Gwamnatin Tarayya ta jajirce wajen tabbatar da tsaro, tsari, da jin daɗin dukkan mahajjata.
“Ku jakadun Nijeriya ne. Kuna ɗauke da hoton ƙasar mu da mutuncin al’ummar mu. Halayen ku su nuna tarbiya, tawali’u, haƙuri, da gaskiya,” inji shi.
An fara jigilar ne da mahajjata kusan 500 daga Jihar Kogi zuwa Saudiyya, yayin da jimillar maniyyata 50,000 ne ake sa ran za su gudanar da aikin Hajjin na bana daga Nijeriya.
Da yake jawabi a wurin taron, Shettima ya bayyana cewa aikin Hajji wata tabbatacciyar yarjejeniya ce tsakanin gwamnatin Nijeriya da ’yan ƙasa, inda ya ce ya zama wajibi kan gwamnati ta sauke nauyin kula da su, su kuma maniyyata su kare mutuncin ƙasar.
Ya ƙara da cewa: “Aikin mu ne mu tabbatar kowane maniyyaci ya yi wannan tafiya ba tare da wata wahala ko fargaba ba. Nasarar wannan aikin ba ta dogara ne kawai kan yawan jiragen da suka tashi ba, a’a, tana ga jin daɗin mahajjatan mu da kuma kauce wa duk wani naƙasu da za a iya kauce masa.”
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya bayyana aikin Hajji a matsayin wata dama ta musamman da ke buƙatar sadaukarwa ga Allah. Ya buƙaci maniyyatan da su ci gaba da addu’o’i ga Nijeriya, musamman kan zaman lafiya da cigaban tattalin arziki.

Haka zalika, ya nemi a taya Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin sa Shettima da addu’a yayin da suke ƙoƙarin gyara ƙasar nan ta hanyar manufofin su na “Sabunta Fata”.
Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Isma’il Abba Yusuf, ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa hukumar tana nan kan bakan ta na tabbatar da jin daɗin ’yan Nijeriya.
Ya bayyana cewa hukumar tana fuskantar garambawul ƙarƙashin gwamnatin Tinubu don tabbatar da gaskiya da kuma sauya fasalin aikin Hajji a ƙasar nan.
Taron ya samu halartar Ƙaramar Ministar Abuja, Dakta Mariya Mahmoud Bunkure, da wakilin Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, waɗanda duka suka jaddada ƙudirin gwamnati na ganin an kwashe mahajjata lafiya an kuma dawo da su lafiya.







