Hukumar EFCC a yau Alhamis, 9 ga Afrilu, 2026, ta kama mutane 31 da ake zargi da damfarar intanet a wani samame da ta kai wata makarantar damfara ta intanet (Yahoo academy), wacce ke cikin Becki Estate, Karu, a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
An kama waɗanda ake zargin, waɗanda suka haɗa da shugabanni biyu da kuma masu koyon aikin, ne yayin da suke samun horo kan yadda ake damfarar intanet.
Kayayyakin da aka ƙwato daga hannun su sun haɗa da wayoyin hannu, kwamfutocin tafi-da-gidan-ka guda 18 da sauran na’urori.
Binciken EFCC ya nuna cewa wasu daga cikin masu koyon aikin an jawo su ne tun daga Jihar Binuwai ta hannun masu wannan makaranta da alƙawarin za a ba su aiki. Amma suna isowa wurin, sai aka damƙa masu na’urorin sadarwa, kwamfutoci da manhajoji domin fara horar da su a harkar damfarar yanar gizo.

Domin tabbatar da biyayya da sadaukarwa, masu makarantar sun tsare waɗannan matasan a cikin harabar wurin, suka hana su fita, tare da ƙwace wayoyin su gaba ɗaya, abin da ya katse su daga hulɗa da waje.
Haka kuma, ana ladabtar da su da azaba ta jiki, inda ake yi musu dukan tsiya idan aka ga suna nuna rashin biyayya.
Za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.







