• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda CBN ya kori tsoffin shugabannin Bankin Union, bayan gano badaƙala, gidoga da harƙallar wasoson maƙudan kuɗaɗen masu ajiya a bankin

Rahoton Musamman

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
April 7, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Yadda CBN ya kori tsoffin shugabannin Bankin Union, bayan gano badaƙala, gidoga da harƙallar wasoson maƙudan kuɗaɗen masu ajiya a bankin
Bankin Union da CBN

Bankin Union da CBN

Badaƙala, harƙalla, gidoga da ƙaƙudubar maƙudan kuɗaɗe da rashin ingantaccen gudanarwa da suka kai tiriliyoyin naira ne suka haddasa har Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya kori tsofaffin daraktoci da masu bankin ‘Union Bank of Nigeria’ (UBN), tare da naɗa sabon kwamitin gudanarwa da shugabanci daga CBN.

Rahoton binciken ƙwaƙwaf da ya bayyana a ranar Litinin na ɗauke da cikakken bayani kan abin da ya jawo sa hannun CBN tun a watan Janairu 2024 a wannan dadadden bankin kasuwanci.

A cewar rahoton, tsofaffin masu bankin da daraktoci sun shiga harkokin gada-gadar karkatar da rahotannin kuɗi, wawure rancen kuɗaɗen waje ta hanyar damfara, amfani da dabarun kuɗi marasa tsari da kuma cire kuɗin ajiyar kwastomomi ba bisa ƙa’ida ba.

Rahoton ya nuna cewa ‘Titan Trust Bank’, wanda ya kasance hanyar zuba jari ta tsofaffin masu bankin da daraktoci, wanda aka haɗa da Union Bank, yana da bashin dala miliyan 300 da ya ciwo daga Afreximbank, ba tare da kariya daga sauyin farashin canjin kuɗi ba.

Wannan bashin da ba a bayyana ba an ɓoye shi ne aka lafta wa Union Bank, wanda ya haifar da wasu dabarun kuɗi marasa tsari da suka kauce wa doka, domin ɓoye illolin da yake haifarwa ga ayyukan bankin.

An kuma gano cewa tsofaffin daraktoci da masu bankin sun haɗa wannan bashin dala miliyan 300 da wasu kuɗaɗe, har ya kai sama da dala miliyan 490 da aka yi amfani da su wajen sayen hannun jarin Union Bank, yayin da aka ɗora wa bankin nauyin biyan bashin.

Wannan ya zama kamar bankin yana amfani da kuɗin sa wajen sayen kan sa.

Rahoton ya ƙara da cewa ba su yi kariya daga asarar da ke faruwa sakamakon canjin darajar kuɗi ba, kuma ba su rufe kuɗin ruwa da sauran kuɗaɗen da ke tattare da bashin ba, duk da cewa suna ci gaba da amfana da mallakar bankin gaba ɗaya.

To wannan ya haifar da asarar kimanin naira biliyan 396 da kuma kuɗin ruwa da sauran kuɗaɗe sama da naira biliyan 147 zuwa ƙarshen zangon watanni uku na shekarar 2025.

Masu binciken sun kuma gano cewa tsofaffin daraktoci da masu bankin sun karkatar da rancen kuɗaɗen waje da aka karɓa daga bankunan ƙasashen waje, inda aka juya kuɗaɗen da ya kamata a ba kwastomomi, aka yi walle-walle da asarlarƙala ta miliyoyin daloli.

Abin lura shi ne an gudanar da waɗannan mu’amaloli da babban bankin ƙasa a wancan lokacin, ba tare da sanar da shi ainihin manufar rancen ba, yayin da aka ba bankunan waje rahotanni na ƙarya.

Haka kuma, rahoton ya gano karkatar da kuɗaɗen masu ajiya da masu bada bashi na Union Bank na miliyoyin daloli.

Misali, an cire dala miliyan 58 domin biyan wasu basussuka da suka zama katutu daga bashin dala miliyan 300 na Afreximbank da ba a bayyana ba.

Jimillar kuɗin da aka cire ba bisa ƙa’ida ba ya wuce dala miliyan 100, wanda ya jawo ƙarancin kuɗin waje ga bankin.

Wani ƙwararren mai nazarin binciken, wanda ya nemi a sakaya sunan sa saboda muhimmancin rahoton, ya ce sa hannun CBN ya ceci bankin daga yiwuwar rufe shi da kuma illa ga tsarin bankuna gaba ɗaya.

Wannan sa hannu ya bai wa bankin damar ci gaba da aiki cikin sauƙi yayin da sabbin daraktoci ke gyara tafiya da tsarin bankin.

Matakan gyaran da aka ɗauka sun taimaka wa Union Bank ya fara farfaɗowa, ya ƙara samun kaso a kasuwa, tare da biyan basussuka da suka yi katutu. Zuwa ƙarshen zangon uku na 2025, bankin ya riga ya fara dawowa kan turbar daidai cikin hayyaci, kuma masana na sa ran zai iya cika sabon sharadin ƙarfafa jarin naira biliyan 200 domin ci gaba da riƙe lasisin bankin ƙasa.

A wata sanarwa da ta biyo bayan hukuncin kotun Tarayya da ke Lagos a ranar 25 ga Maris 2026, dangane da matakin da ta ɗauka kan Union Bank, CBN ya ce yana nazarin cikakken hukuncin, amma matsayin bankin bai canja ba, wato har yanzu yana ƙarƙashin kulawar CBN.

 

CBN ya ce yana ci gaba da aiki bisa doka da kuma tsare-tsaren sa.

Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa Union Bank na da ƙarfi kuma zai iya cika dukkan wajibai ga kwastomomi, masu ajiya da sauran masu ruwa da tsaki.

CBN ya ƙara da cewa zai ci gaba da sa-ido domin tabbatar da bankin yana aiki cikin tsari mai kyau da aminci, tare da kare amincewar jama’a a tsarin banki.

Tags: badaƙalaCBNsataUnion Bank
Previous Post

Tinubu ya amince a biya bashin Naira tiriliyan 3.3 don gyara wutar lantarki

Next Post

ADC ta yi da zanga-zanga kan ƙin amincewar da INEC ta yi da shugabancin Mark

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
ADC ta yi da zanga-zanga kan ƙin amincewar da INEC ta yi da shugabancin Mark

ADC ta yi da zanga-zanga kan ƙin amincewar da INEC ta yi da shugabancin Mark

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!