• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Bankunan da suka sake ƙarfafa jari za su iya jure girgiza da jijjigar tattalin arziki – CBN

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
April 5, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Hedikwatar CBN tare da Gwamna Olayemi Cardoso

Hedikwatar CBN tare da Gwamna Olayemi Cardoso

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ta tabbatar da cewa bankunan da a yanzu suka sake ƙarfafa jarin su, yanzu sun fi ƙarfi wajen bada kuɗi ga ƙananan da matsakaitan kamfanoni (SMEs), manyan ayyukan gine-ginen ƙasa da kuma ayyukan masana’antu, bayan kammala shirin sake ƙarfafa jarin su.

A cikin wata takarda wadda aka fitar a ranar Asabar, CBN ya ce shirin ya ƙarfafa tushen jarin masu bada rance, tare da ƙara musu ƙarfin tallafa wa Shirin zuba jari na dogon lokaci da manyan ayyuka masu tsada a fannoni kamar makamashi, masana’antu da fasaha.

A cewar babban jami’i mai kula da harkokin banki, bankunan sun haɗa jimillar Naira tiriliyan 4.65 a matsayin sabon jari, inda bankuna 33 suka cika sabbin ƙa’idojin mafi ƙarancin jari.

CBN ta ce bangaren bankunan da aka sake ƙarfafa jarin na su zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta masana’antun ƙasar da kuma faɗaɗa fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.

“Ƙarin jari yana bai wa bankuna damar bada kuɗi ga ayyukan gina ƙasa, makamashi, masana’antu da fasaha waɗanda ke buƙatar dogon lokaci da manyan kuɗaɗe,” inji mai kula da harkokin kuɗi na CBN.

“Bangaren da aka sake ƙarfafa jarin sa zai fi iya tallafa wa sabbin manufofin inganta masana’antu da faɗaɗa fitar da kayayyaki zuwa waje.”

Babban bankin ya ƙara da cewa ƙarfafa ma’aunin kuɗaɗen bankuna zai ba su damar ɗaukar manyan nauyin bayar da kuɗi, tare da inganta kwanciyar hankalin tsarin kuɗi gaba ɗaya.

Da yake ƙarin bayani kan amfanin shirin, Gwamnan CBN ya ce ƙarfafan tsarin ajiyar jari zai ba bankuna damar jure girgizar tattalin arziki, su daidaita da ƙa’idojin duniya, tare da inganta kula da haɗari da kyakkyawan tsarin gudanarwa a duk fannin.

“Ta hanyar gina bankuna da suka dace da buƙatun tattalin arzikin da zai kai darajar tiriliyan ɗaya na dala, bangaren zai iya tallafa wa SMEs, kamfanonin da ke fitar da kaya, da kuma manyan ayyukan gine-ginen ƙasa cikin dorewa,” inji CBN.

“Ana sa ran sake ƙarfafa jarin zai ƙarfafa haɗa kowa cikin harkokin kuɗi tare da faɗaɗa damar samun rance a faɗin ƙasa.”

A cewar babban bankin, shirin ya yi daidai da manyan manufofin kuɗi da na kasafin kuɗi, yana tallafa wa sarrafa yawan kuɗi a kasuwa, isar da manufofin gwamnati, da kuma rage hauhawar farashi.

Mai kula da harkokin ya bayyana shirin a matsayin mafi girman gyaran banki tun bayan haɗakar bankunan Nijeriya na shekarar 2005, yana mai cewa wannan babban mataki ne na gina tsarin kuɗi mai ƙarfi, gasa da kuma mai tallafa wa ci gaba.

CBN ya kuma ce bankunan da har yanzu ba su kai sabbin matakan jari ba suna ci gaba da aiki, kuma suna kan hanyar kammala shirin sake ƙarfafa jarin su.

Da yake magana kan wannan nasara, Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya ce ba za a iya samun ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa ba tare da tsarin kuɗi mai ƙarfi ba.

“Wannan sake ƙarfafa jari yana tabbatar da cewa bankunan Nijeriya za su iya ɗaukar nauyin manyan ma’amaloli da ake buƙata domin bunƙasa tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya,” inji Cardoso.

Gwamnan ya ƙara da cewa shirin ya ƙarfafa juriyar tsarin kuɗi tare da tabbatar da cewa yana cikin shiri mai kyau don tallafa wa ci gaban tattalin arziki da kuma jure matsalolin cikin gida da na waje.

Tags: bankunaCardosoCBNjari
Previous Post

Sojojin Nijeriya sun ceto mutum 31 da aka yi garkuwa da su bayan harin coci

Next Post

Tinubu ya amince a biya bashin Naira tiriliyan 3.3 don gyara wutar lantarki

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Tinubu ya amince a biya bashin Naira tiriliyan 3.3 don gyara wutar lantarki

Tinubu ya amince a biya bashin Naira tiriliyan 3.3 don gyara wutar lantarki

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!