Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa na 2023 na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana murabus ɗin sa daga jam’iyyar.
A cikin takardar da ya wallafa a soshiyal midiya yau Lahadi, Kwankwaso ya ce: “Ina mai ba da sanarwar murabus ɗina a hukumance daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), wanda zai fara aiki nan take.
“Ina amfani da wannan dama wajen bayyana matuƙar godiya ta bisa girmamawa da damar da aka ba ni na yin aiki a matsayin Jagoran na jam’iyyar na Ƙasa, tare da zama ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
“A matsayi na na cikakken ɗan jam’iyya mai ƙwazo da gaskiya, wannan ba shawara ce mai sauƙi a gare ni ba.
“Sai dai, la’akari da yadda al’amuran siyasar ƙasa suke tafiya a halin yanzu, wanda ke buƙatar sake tsara dabaru, na ga ya zama dole in danganta kai na da wani sabon dandalin siyasa wanda zai ba da mafi kyawun damar kawo canji mai tasiri a ƙasa.
“Ina miƙa godiya ta musamman ga Shugaban Jam’iyya na Ƙasa, Ajuji Ahmed, da dukkan ‘yan Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa bisa cikakken goyon bayan su a tsawon lokacin da na yi.
“Haka kuma ina gode wa Kwamitin Amintattu (BoT), Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC), da dukkan shugabanni a matakai daban-daban na jam’iyya — daga matakin unguwa har zuwa jiha, da kuma tsofaffin membobin jam’iyyar da duk masu goyon bayan tafiyar Kwankwasiyya bisa jajircewa da sadaukarwar su ga manufar mu ta bai-ɗaya.
“Za mu ci gaba da haɗa gwiwa tare da aiki tare domin gina makoma mafi kyau da wadata ga ƙasar mu mai daraja.”







