Ziyarar aiki ta tarihi wadda Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kai Birtaniya ta kai wani muhimmin matsayi a ranar Laraba, yayin da shi da Sarki Charles na Uku suka gabatar da ƙwararan jawabai masu jaddada ɗorewar haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu a wata gagarumar liyafar alfarma da aka yi a Fadar Windsor.
Taron walimar, wanda ya samu halartar manyan ‘yan gidan sarautar Birtaniya, ciki har da Sarauniya Camilla, Yarima William, da Catherine Gimbiyar Wales, ya nuna ƙarnuka na tarihi da aka raba tare, alaƙar al’adu, da kuma bunƙasar haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin Nijeriya da Birtaniya.
A jawabin sa, Sarki Charles ya yi maraba da Shugaba Tinubu da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, inda ya yaba da saurin sauyin da Nijeriya ta samu da kuma ƙarin tasirin ta a duniya.
Lokacin da yake tunowa da ziyarce-ziyarcen da ya kai Nijeriya a baya da mu’amalar sa da sarakunan gargajiya, Sarkin ya bayyana ta a matsayin ƙasa mai cike da kuzari da matasa masu himma.

“Ba wai Nijeriya ta sauya kawai ba, a’a ta ma riga ta kai ga nasara,” inji shi, yana mai nuni da cewa yawan al’ummar ƙasar da ya haura miliyan 230, mafi yawan su matasa ne, ya sanya ta zama muhimmiyar ƙasa wajen magance ƙalubalen da ke addabar duniya.
Sarki Charles ya kuma yaba wa ‘yan Nijeriya mazauna Birtaniya, yana mai bayyana irin gudunmawar da suke bayarwa a fannoni kamar kiwon lafiya, kasuwanci, ilimi, wasanni da fasaha. Ya kira su “gadar rai” wadda ta haɗa ƙasashen biyu tare da ƙara armashi ga rayuwar Birtaniya.
Daga kiɗan Afrobeats zuwa finafinan Nollywood da kuma ƙwallon ƙafa na Firimiya Lig, Sarkin ya yi la’akari da irin tasirin al’adun Nijeriya a rayuwar Birtaniya, ya ƙara ɗan barkwanci yayin da ya yi nuni da wani taron “Jollof and Tea” da aka yi a baya-bayan nan inda muhawara kan wace irin jollof ta fi — ta Nijeriya, Ghana ko Senegal — ta ci gaba da kasancewa ba tare da warwarewa ba a diflomasiyance.
Sarkin ya jaddada ƙarfafuwar haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu, yana mai lura da cewa kamfanonin Nijeriya suna ƙara zuba jari a Birtaniya, inda manyan bankuna suke kafa rassan su a Birnin London, sannan kamfanoni suke yin rajista a kasuwar hannun jari ta London Stock Exchange.

Ya bayyana cewa a kwanan nan Nijeriya ta zama babbar kasuwar fitar da kayayyakin Birtaniya a Afrika, yayin da zirga-zirga da yawon buɗe ido tsakanin ƙasashen biyu ke ci gaba da bunƙasa, tare da kashe kuɗi masu yawa daga ɓangarorin biyu.
Sarki Charles ya kuma haskaka haɗin gwiwa a fannin ilimi da fasaha, inda cibiyoyin Birtaniya ke faɗaɗa ayyukan su a Nijeriya, tare da haɗin gwiwar ƙirƙire-ƙirƙire na bai-ɗaya da ke ƙara ƙarfafa.
Yayin da yake murnar cigaban da aka samu tare, Sarkin ya ce an samu rikicewar dangantakar tarihi tsakanin ƙasashen biyu, yana mai yarda cewa wasu ɓangarorin tarihin da suka raba sun bar “alamun raɗaɗi.”
Sai dai ya jaddada muhimmancin koyon darasi daga tarihi domin gina makoma bisa mutunta juna, cigaba da kuma haɗin kai.
Bugu da ƙari, ya jaddada rawar da Nijeriya take takawa a matsayin jagora a Afrika da kuma a cikin Ƙungiyar Kwamanwal, yana mai nuna buƙatar ƙarfafa haɗin gwiwar duniya a wannan zamani da ƙasashen duniya suke ƙara haɗuwa da juna.

A nasa martanin, Shugaba Tinubu ya bayyana wannan lokaci a matsayin babbar karramawa, yana mai lura da cewa shi ne shugaban Nijeriya na farko da ya yi jawabi a liyafar ƙasa a Gidan Fadar Windsor.
Ya yaba wa gudunmawar tarihi da Birtaniya ta bayar wajen kafuwar tsarin dimokiraɗiyya, yana mai ambaton Magna Carta da kuma ayyukan manyan masana masu zurfin tunani irin su Thomas Hobbes, John Locke, da Edmund Burke, waɗanda ra’ayoyin su ke ci gaba da tasiri ga tsarin siyasa a duniya.
Tinubu ya amince cewa tsarin shari’a da hukumomin Nijeriya sun samu tasiri daga al’adun Birtaniya, musamman dokar gama-gari ta Ingila (English common law) da tsarin majalisa, waɗanda aka daidaita su da yanayin Nijeriya na musamman.
Shugaban ya jaddada muhimmancin ‘yan Nijeriya mazauna Birtaniya, yana bayyana su a matsayin ɗaya daga cikin al’ummomi mafi ƙwazo a duniya.
Ya yaba wa ‘yan Nijeriya da ke aiki a Hukumar Kiwon Lafiya ta Ƙasa (National Health Service) a Birtaniya da sauran fannoni daban-daban, yana mai lura da gagarumar gudunmawar da suke bayarwa ga al’ummar Birtaniya.
Tinubu ya kuma yi nuni da fitattun ‘yan asalin Nijeriya a fannin wasanni, ciki har da Maro Itoje, Bukayo Saka, Eberechi Eze, da Anthony Joshua, a matsayin misalan ƙaƙƙarfar dangantakar bil’adama da ta haɗa ƙasashen biyu.
Yayin da yake magana kan ƙalubalen yanki, Tinubu ya jaddada rawar da Nijeriya ke takawa wajen yaƙar ta’addanci a Yammacin Afrika, musamman a yankin Sahel, tare da kira da a ci gaba da haɗin gwiwa da Birtaniya.
Ya bayyana shirin sa na ganawa da Firayim Ministan Birtaniya Keir Starmer domin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da kuma dabarun haɗin kai.
A wani ɓangare mai taɓa zuciya, Tinubu ya nuna godiyar sa ga Birtaniya bisa ba shi mafaka a lokacin mulkin soja a Nijeriya.
Ya tuna yadda hukumomin Birtaniya suka ba shi kariya a wancan lokaci, yana bayyana wannan a matsayin wani muhimmin babi a tafiyar sa a turbar siyasa.
“Wannan haɗin kai ya ci gaba da kasancewa a rubuce cikin ƙwaƙwalwar mu ta bai-ɗaya,” inji shi, yana mai ƙarawa da cewa abin juyayi ne a ce ga shi ya dawo a matsayin zaɓaɓɓen Shugaban Nijeriya na dimokiraɗiyya.
Dukkan shugabannin sun jaddada muhimmancin Ƙungiyar Kwamanwal a matsayin dandalin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe membobi 56, inda Sarki Charles da Tinubu suka yi kira da a ƙarfafa ciniki, daidaiton dokoki, da haɗin tattalin arziki.
Sun haskaka shirye-shirye irin su “Enhanced Trade and Investment Partnership” a matsayin misalai na yadda ƙasashen biyu za su iya buɗe damar cigaba, samar da ayyukan yi, da kuma inganta cigaba mai ɗorewa.
Sarkin ya kuma yaba da ƙoƙarin Nijeriya wajen inganta zaman lafiya da daidaito tsakanin addinai, yana mai nuni da yadda Kiristoci da Musulmi suke rayuwa tare cikin jituwa a ƙasar.
An kammala daren da musayar fatan alheri tsakanin shugabannin biyu gabanin sallar Eid el-Fitr, wanda ke nuna muhimmancin watan Ramadan mai alfarma.
Sarki Charles ya rufe jawabin sa da ɗaga kofin girmamawa ga Nijeriya, yana cewa, “Naija No Dey Carry Last,” yayin da Shugaba Tinubu ya ɗaga nasa kofin domin girmama ɗorewar abokantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu da kuma makoma ta bai-ɗaya da aka gina bisa haɗin kai da mutunta juna.
Wannan ziyara ta ƙasa dai tana nuna wani muhimmin mataki a dangantakar Nijeriya da Birtaniya, tana ƙarfafa haɗin gwiwa da ke ci gaba da bunƙasa a fannoni kamar diflomasiyya, kasuwanci, al’adu, da tsaro a wannan duniya mai ƙara haɗuwa da juna.








