• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Haske daga CBN: Alamomi masu nuna Nijeriya ta shiga 2026 da ƙafar dama

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
March 5, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025
Bankin CBN

Bankin CBN

1. Alama ta farko ita ce yadda tun bayan karyewar tsadar farashin kayan abinci a tsakiyar 2025, har yau farashin kayan gona bai ƙara yin tashin fin ƙarfin aljihun talaka ba. A cikin watan azumin nan har yau ba a samu tashin kayan abinci a kasuwannin yankunan karkara ba, bisa binciken da wakilin mu ya yi a kasuwannin Giwa Jihar Kaduna, Ɗandume a Jihar Kaduna, Gumau a Jihar Bauchi da wasu kasuwanni da dama, inda har yau tiyar fara ko jar masara bai kai Naira dubu ɗaya. Haka abin yake ga gero da dawa fara ko ja.

2. Yadda malejin tsadar rayuwa ya yi ƙasa zuwa kashi 15.1 ya nuna kayan abinci da kayan masarufi ba su tashi fiye da ƙarfin buƙatun mai ƙaramin ƙarfi ba.

3. Ci gaba da samun daidaiton daraja da tagomashin Naira a kasuwar canjin kuɗaɗen waje na ƙara wa tattalin arziki ƙwarin guiwa tare da samun ƙarin yawan kuɗaɗen waje daga masu sha’awar zuba jari da ‘yan ƙasa mazauna ƙasashen waje.

4. Yadda Asusun Ajiyar Kuɗaɗen Waje a CBN ya cika maƙil da kusan Dala biliyan 50 zuwa cikin watan Fabrairu, ya ƙara nuna samun ci gaba da ake yi, bisa la’akari da cewa wannan gwamnati Dala biliyan 3 da kaɗan kacal ta gada a asusun a ƙarshen Mayu, 2026.

5. Shirin Ƙarfafa Jarin Bankuna da CBN ya tilasta bankunan Nijeriya ya tabbatar da ƙarin ƙarfin tattalin arziki a farkon 2026. Zuwa yanzu bankunan da suka cika sharuɗɗa na da jimillar ƙarfin jari fiye da Naira tiriliyan 4.5, yayin da ake sa ran su kai Naira tiriliyan 6 nan zuwa ƙarshen watan Maris, lokacin da wa’adin da CBN ya ba su zai cika.

6. Rage adadin kuɗin ruwa daga kashi 27% bisa 100% zuwa kashi 26.5 bisa 100%, zai rage tsadar karɓar lamuni daga hannun bankuna.

6. Yadda gundarin adadin ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya ya kai har Dala biliyan 34.80 a ƙarshen 2025, daga Dala biliyan 3.99 a Mayu 2023, ya nuna ƙarfin tattalin arzikin Nijeriya na kan miƙaƙƙar hanyar tabbatar da ƙudirin kaiwa darajar Dala Tiriliyan Ɗaya nan zuwa shekarar 2030.

Tags: bankunaCBNkuɗi
Previous Post

Daga dala biliyan 3.99 zuwa dala biliyan 34.80: Gundarin adadin ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya ya ninka fiye da sau 7 cikin shekaru biyu – Cardoso

Next Post

Garaɓasa: Majalisar Zartarwa ta amince da ba ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da za su yi ritaya giratuti na ƙunshin albashin shekara guda

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Garaɓasa: Majalisar Zartarwa ta amince da ba ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da za su yi ritaya giratuti na ƙunshin albashin shekara guda

Garaɓasa: Majalisar Zartarwa ta amince da ba ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da za su yi ritaya giratuti na ƙunshin albashin shekara guda

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!