• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Sunday, November 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Daga dala biliyan 3.99 zuwa dala biliyan 34.80: Gundarin adadin ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya ya ninka fiye da sau 7 cikin shekaru biyu – Cardoso

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
March 3, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Hedikwatar CBN tare da Gwamna Olayemi Cardoso

Hedikwatar CBN tare da Gwamna Olayemi Cardoso

Gundarin adadin kuɗaɗen ajiya na waje a Nijeriya ya ƙaru ninka sau bakwai da rabi, tsakanin 2023 zuwa ƙarshen 2025, inda ya kai dala biliyan $34.8 a shekarar da ta gabata.

Wannan adadi, wanda ke nuna ingancin ajiyar kuɗaɗen waje na ƙasa, ya kasance dala biliyan $3.99 kacal a ƙarshen shekarar 2023.

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ne ya bayyana sabon adadin a cikin wata sanarwa.

An ruwaito Cardoso na cewa wannan ci gaba yana nuna gagarumar ƙarfafuwa a mataki da kuma ingancin ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya cikin shekaru uku da suka gabata.

Yayin da yake waiwaye kan abin da ya kira gagarumin ingantaccen tsarin ajiyar kuɗi, Cardoso ya bayyana cewa matsayin adadin kuɗaɗen a shekarar 2025 kaɗai ya zarce jimillar da aka samu a ƙarshen 2023, wanda ya tsaya a dala biliyan $33.22.

Ya ƙara da cewa adadin ya tashi daga dala biliyan $23.11 a ƙarshen 2024 zuwa dala biliyan $34.8 a ƙarshen 2025, yayin da asusun ajiyar kuɗaɗen waje da ke CBN shi kuma ya ƙaru daga dala biliyan $40.19 zuwa dala biliyan $45.71 a wannan lokaci, wanda ke nuna ƙarin dala biliyan $5.52.

Ya bayyana cewa wannan faɗaɗa ya nuna yadda ƙarfin Njeriya ya ƙaru wajen biyan basussukan waje, tallafawa daidaiton farashin canjin kuɗi, da kuma ƙarfafa juriya da daidaiton tattalin arziki baki ɗaya.

Cardoso ya bayyana matsayin ajiyar kuɗin ƙarshen 2025 a matsayin tabbaci mai ƙarfi ga nasarar gyare-gyaren manufofi da daidaita ɓangaren kuɗaɗen waje da bankin ke aiwatarwa.

Haka kuma, ya sake jaddada ƙudirin CBN na ci gaba da riƙe isasshen ajiyar kuɗi, tallafa wa gudanar da kasuwar canjin kuɗi cikin tsari, ƙara amincewa da matsayin tattalin arzikin Nijeriya a waje, da tabbatar da ɗorewar tattalin arziki daidai da dokar da ta kafa bankin.

Ya cewa adadi da jimillar ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya, sun nuna gagarumin ci gaba a ƙarshen 2025, wanda ke nuna ƙarfafa ginshiƙan ɓangaren waje da kuma ɗorewar gyare-gyaren manufofi.

Bayan ya bayyana hakan a taron bayan zaman Kwamitin Tsare-tsaren Kuɗi (MPC), inda ya ce ajiyar kuɗaɗen waje na ƙasa ya kai dala biliyan $50.45 zuwa ranar 16 ga Fabrairu, 2026, Cardoso ya jaddada cewa gundarin adadin ya nuna amfanin ƙara gaskatawa da amincin gudanar da harkokin canjin kuɗi, wanda ke ƙara yarda da masu zuba jari, jawo ƙarin shigowar kuɗaɗen waje da inganta hanyoyin sarrafa ajiyar kuɗi.

Tags: CBNOlayemiCardoso
Previous Post

Ranar Ji ta Duniya 2026: Dalilan da za a iya kauce wa suna ci gaba da haddasa naƙasar ji a tsakanin yara a Nijeriya – Minista

Next Post

Haske daga CBN: Alamomi masu nuna Nijeriya ta shiga 2026 da ƙafar dama

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025

Haske daga CBN: Alamomi masu nuna Nijeriya ta shiga 2026 da ƙafar dama

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!