• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Wa’adin ƙarfafa jarin bankuna: Tattalin arziki ya ɗau saiti yayin da bankuna suka kusa tara Naira tiriliyan 6 kafin ƙarshen Maris

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
March 2, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025
Bankin CBN

Bankin CBN

Bayyanannun alamomi da sabubba da dama sun nuna cewa Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya tsunduna tattalin arzikin Nijeriya cikin shekarar 2026 da ƙafar dama, ganin yadda shirin ƙarfafa jarin bankuna a Nijeriya ke ci gaba da ƙara ƙarfi, inda jimillar kuɗin da ake sa ran za a tara zai iya kaiwa kusan naira tiriliyan 6 kafin wa’adin 31 ga Maris, 2026 da CBN ya gindaya.

Majiyoyin harkar banki sun bayyana cewa har yanzu akwai sama da naira tiriliyan 1.5 na yarjejeniyoyin tara jari da ke kan hanya, kuma ana sa ran yawancin su za su kammala kafin cikar wa’adin.

Bincike ya nuna cewa babu wasu sabbin tayin hannun jari da ke jiran amincewa daga hukumomin kasuwar jari, amma bankuna suna amfani da hanyoyin tara jari cikin gaggawa ta hanyar sayar da hannun jari kai tsaye (private placement), jawo sabbin masu zuba jari,

runtubar masu hannun jari a cikin bankunan,

manyan kamfanoni da masu kuɗi masu yawa.

Wasu bankuna na amfani da tsarin buga tandar neman masu zuba jari, domin kammala yarjejeniyoyin su bayan sun samu izinin masu hannun jari da zai ba su damar tara jari ta hanyoyi daban-daban.

Sassauci Ga Bankunan da CBN ke Kula da Su

CBN ya nuna cewa wa’adin 31 ga Maris, 2026 na iya rashin shafar wasu bankuna da ke ƙarƙashin kulawar sa ta musamman. Waɗannan bankuna sun haɗa da:

Polaris Bank,

Union Bank of Nigeria da kuma

Keystone Bank.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana a bayan taron Kwamitin Tsare-tsaren Manufofin Kuɗi (MPC) cewa:

“An tabbatar da kuma amince tara naira tiriliyan 4.05 zuwa ranar 19 ga Fabrairu, 2026.

Daga ciki, naira tiriliyan 2.90 (kashi 71.6%) daga cikin gida ne.

Dala miliyan 706.84 (kimanin naira tiriliyan 1.15, kashi 28.33%) daga ƙasashen waje ne.”

Bankuna 20 sun riga sun cika sabbin sharuɗɗan  jarin.

Bankuna 13 kuma suna matakin ƙarshe na kammala tara jarin.

Ya kuma nuna ƙwarin gwiwa cewa za a kammala shirin cikin wa’adin da aka tsara.

Tsarin Tabbatar da Jari

Sabbin kuɗin da aka tara dole ne su wuce tantancewa kafin a ba da izinin rabon hannun jari da kuma sakin kuɗin ga bankin.

  • Kwamitin tantance jarin ya ƙunshi: Babban Bankin Nijeriya (CBN),
  • Hukumar Tsaro da Sa-ido kan Harkokin Kudade (SEC) da kuma
  • Hukumar Inshorar Kwastomomi da Masu Hannayen Jari a Bankuna (NDIC).

Haka kuma, doka ta 4.1 ta ƙa’idojin kamfanonin harkokin kuɗi ta tanadi cewa duk wanda ya sayi kaso 5% na hannun jari a kasuwa dole ne ya nemi amincewar CBN cikin kwanaki bakwai.

Dalilin Sassauci Ga Wasu Bankuna

Gwamnan ya bayyana cewa bankunan da ke ƙarƙashin kulawar CBN na fuskantar wasu matsalolin shari’a da tsarin gudanarwa, wanda hakan ka iya hana su kasa cikin wa’adin a ranar 31 ga Maris, 2026.

Ya tabbatar da cewa kuɗaɗen masu ajiya a Polaris Bank, Union Bank da Keystone Bank suna cikin tsaro, kuma ayyukan su na ci gaba ƙarƙashin kulawar CBN.

Masana kamar Farfesa Biodun Adedipe da tsohon shugaban Chartered Institute of Bankers of Nigeria (CIBN), Mista Okechukwu Unegbu, sun goyi bayan wannan mataki, suna cewa ya fi sauƙi maimakon a ce a rufe bankunan gaba ɗaya.

Previous Post

Ɗaruruwan jiragen ruwa sun maƙale a Tekun Fasha

Next Post

Ranar Ji ta Duniya 2026: Dalilan da za a iya kauce wa suna ci gaba da haddasa naƙasar ji a tsakanin yara a Nijeriya – Minista

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Ranar Ji ta Duniya 2026: Dalilan da za a iya kauce wa suna ci gaba da haddasa naƙasar ji a tsakanin yara a Nijeriya – Minista

Ranar Ji ta Duniya 2026: Dalilan da za a iya kauce wa suna ci gaba da haddasa naƙasar ji a tsakanin yara a Nijeriya - Minista

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!