Kotun Ƙolin ƙasar Saudiyya ta ba da sanarwa a yammacin yau Talata cewa an ga jinjirin watan da ke nuna farkon watan Ramadan a Saudiyya, wanda ya tabbatar da cewa watan mai alfarma zai fara a gobe Laraba.
Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa sanarwar ta biyo bayan rahotanni daga kwamitocin ganin wata da aka ba izini a faɗin Masarautar, bisa ga koyarwar addinin Musulunci.
Da wannan tabbaci, Musulmi a faɗin Saudiyya za su fara azumi da asubahin ranar Laraba, suna gudanar da watan tara na kalandar Hijira da addu’o’i, nazari na ruhaniya da ayyukan alheri.
Jaridar ta ce shirin ya nuna yadda Saudiyya ke ci gaba da ƙoƙarin inganta ayyuka a Masallatai Masu Tsarki Biyu tare da karɓar adadin masu ibada da ke ƙaruwa a lokacin Ramadan.
Ramadan lokaci ne na ibada ta musamman da ake yin azumi daga ketowar alfijir zuwa faruwar rana, tare da ƙara ibada da tarukan al’umma.
Masallatai a faɗin Masarautar Saudiyya suna shirye-shiryen karɓar masu ibada domin sallar Taraweeh, yayin da hukumomi suka kammala shirye-shiryen tabbatar da gudanar da ayyuka cikin sauƙi a watan mai alfarma.
Hukumomin gwamnatin ƙasar da cibiyoyi masu zaman kan su kuma za su aiwatar da sababbin lokutan aiki da suka dace da jadawalin watan Ramadan.







