• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tarayyar Turai ta bi sahun Hukumar FATF, ta cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da ke da haɗarin safarar kuɗi

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
February 8, 2026
in Labarai
A A
0
Tarayyar Turai ta bi sahun Hukumar FATF, ta cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da ke da haɗarin safarar kuɗi
Shugaban CBN, Olayemi Cardoso

Shugaban CBN, Olayemi Cardoso

Sakamakon gyare-gyaren kasuwar canjin kuɗi da bin ƙa’idojin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ke yi, a yanzu haka Kungiyar Tarayyar Turai (EU), ta cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da ke da haɗarin safarar kuɗi.

Cikin wata sanarwar da Tarayyar Turai (EU) ta fitar a shafin ta na soshiyal midiya, ta bayyana cewa an cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da ke da haɗarin safarar kuɗi da tallafa wa ta’addanci, ta nuna irin gagarumar ribar da gyare-gyaren da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya aiwatar suka haifar.

Wannan mataki ya nuna ƙaruwar bayyana gaskiya da bin ƙa’idoji a ɓangaren ayyukan kuɗi, tare da ingantaccen aiwatar da matakan yaƙi da safarar kuɗi da hana tallafa wa ta’addanci (AML/CFT).

Tunda an tsame sunan Nijeriya daga jerin ƙasashen da EU ke ganin suna da haɗari ana sa ran hakan zai ƙara wanzar da amincewa da haɗin gwiwa daga ƙasashen duniya ga tattalin arzikin cikin gida.

Ɓangaren harkokin kuɗi na Nijeriya ya samu sauye-sauye masu yawa a ‘yan shekarun nan sakamakon gyare-gyare da aka aiwatar. Waɗannan sun haɗa da kasuwannin canjin kuɗi zuwa tsari guda, ƙara tsauraran ƙa’idoji da jagoranci, bayyana gaskiya a harkokin kasuwar musayar kuɗaɗen waje, da kuma ƙarfafa sa-ido kan zirga-zirga da tasarifin kuɗi a cikin tattalin arziki.

Yawancin waɗannan manufofi da gyare-gyare sun haifar da muhimman fa’idoji ga tattalin arziƙin ƙasa.

Babbar nasara daga cikin waɗannan ita ce cire Najeriya daga jerin ƙasashen da EU ke ɗauka a matsayin masu haɗari wajen safarar kuɗi da tallafa wa ta’addanci, tare da Afrika ta Kudu da wasu ƙasashen Afrika huɗu.

Masana harkokin tattalin arziki sun bayyana wannan mataki a matsayin abin da zai ƙara ƙarfafa damar bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya.

Wata sanarwa da Kungiyar Tarayyar Turai ta wallafa a shafin ta ta ce: “Hukumar Tarayyar Turai, bayan tantancewa, ta kammala cewa Nijeriya ta ƙarfafa ingancin tsarin ta na yaƙi da safarar kuɗi da hana tallafa wa ta’addanci, tare da gyara matsalolin fasaha da dabaru da FATF ta bayyana a baya.

Wannan mataki ya yi daidai da shawarwarin da Hukumar FATF ta yanke a tarurrukan ta na watan Yuni da Oktoba na shekarar 2025, inda aka cire wasu ƙasashe daga jerin ‘Ƙasashen da ake sa ido na musamman’, wato waɗanda ake baya-baya da su.

Sanarwar ta ƙara da cewa daga ranar 29 ga Janairu, 2026, za a daina amfani da tsauraran matakan bincike na musamman kan mu’amaloli da suka shafi Nijeriya da sauran ƙasashen da aka cire daga jerin, muddin Majalisar Tarayyar Turai da Majalisar Ministoci sun amince da hakan.

Masana sun lura cewa, kamar yadda aka cire Nijeriya daga jerin FATF, wato ƙasashen da aka ayyana a matsayin ‘grey-list’, haka nan ficewar daga jerin EU na da gagarumin tasiri ga tattalin arziki da harkokin kuɗi.

Kasancewa cikin jerin ƙasashen da ke da haɗari yakan haifar da tsadar gudanar da mu’amaloli, jinkirin biyan kuɗaɗe, taƙaita alaƙar bankuna na ƙasa da ƙasa, da rage jarin waje. An cire Nijeriya daga jerin FATF ‘grey-list’ a watan Oktoban shekarar da ta gabata bayan aiwatar da jerin gyare-gyare don ƙarfafa tsarin AML/CFT.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa amfani da Tsarin Lura da Kasuwar Canjin Kuɗi ta Zamani (EFEMS), sauya tsarin canjin kuɗi zuwa kasuwa mai ‘yanci, da kuma ƙarfafa kulawa da bankuna, duk suna nuna jajircewar CBN wajen aiwatar da gyare-gyare. Ya ce waɗannan sun ƙarfafa ikon Nijeriya na jure girgizar tattalin arziƙi daga sauyin farashin mai da canjin ra’ayin masu tantance darajar kuɗi.

Ya ce: “A shekarar 2026, za mu ƙara haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki, mu ƙarfafa aiki tare da sauran hukumomi da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa, tare da bunƙasa sabbin hanyoyin ƙirƙire-ƙirƙire masu ɗaukar alhaki a tsarin kuɗi. Za mu ci gaba da ba da jagora, kare amincin kasuwannin kuɗin mu, amfani da fasahar zamani don inganta yanke shawara, da gina ƙwarewar ma’aikata domin tsarin kuɗi mai ɗorewa.”

Ba da daɗewa ba bayan nada naɗa shi shugabancin CBN, Cardoso ya fara rushe shinge da rashin bayyana gaskiya a tsarin kuɗi da suka jawo saka Nijeriya cikin jerin ƙasashen da EU ta karta wa jan fenti wajen mu’amalar kuɗaɗen.

Daga gyare-gyare a harkokin musayar kuɗaɗe zuwa ƙarfafa sa-ido kan bankunan kasuwanci, CBN ƙarƙashin Cardoso ya yi duk mai yiwuwa don tabbatar da ficewar Nijeriya daga jerin ‘grey-list’.

Daga cikin matakan bin ƙa’idoji akwai tabbatar da cewa bankuna na iya gano ainihin mai mallakar duk wata ma’amala (beneficial owner) tare da tabbatar da sahihancin sa ko akasin haka. Haka kuma, hukumomin kuɗi suna fahimtar tsarin mallaka da iko na abokan hulɗar su, suna sanin manufar dangantakar kasuwanci, tare da ci gaba da sa-ido kan dukkan mu’amaloli a tsawon dangantakar banki.

Shugabar Ƙungiyar Masu Amfani da Bankuna ta Nijeriya (BCAN), Dokta Uju Ogubunka, ta bayyana ficewar Nijeriya daga jerin ƙasashen da EU ke shakkar mu’amalar kuɗaɗe da su cewar wani matsayi ne na samun babban ci gaba.

Ta yaba wa ƙoƙarin CBN wajen cire ƙasar daga ƙalubalen da ake fuskanta.

Ta ce: “Wannan zai buɗe sabbin dama ga bankunan Nijeriya da abokan hulɗar su a mu’amala da cibiyoyin kuɗi na ƙasa da ƙasa. Yana nuna cewa tsarin kuɗin Nijeriya amintacce ne ga biyan kuɗaɗe da sauran mu’amaloli. Abin murna ne ga duk ‘yan Nijeriya.”

Cikin wata sanarwa da CBN ya fitar a lokacin da aka cire Najeriya daga jerin FATF ‘grey-list’, bankin ya ce wannan ya nuna gagarumin ci gaba a tsarin doka, kulawa da aiwatar da hukunci wajen yaƙi da safarar kuɗi, tallafa wa ta’addanci da yaɗuwar makaman hallaka jama’a.

Sanarwar ta lissafo manyan gyare-gyaren da FATF da GIABA suka tantance, ciki har da ƙarfafa kulawa da cibiyoyin kuɗi, faɗaɗa rahoto da sa-ido kan harkokin tura kuɗi, tsarin musayar kuɗaɗen mai tsafta da hada-hadar kuɗaɗe ta zamani wato ‘fintech’, da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin CBN, NFIU, EFCC da hukumomin tsaro.

Sanarwar ta ƙara da cewa ficewar Nijeriya daga jerin ‘grey-list’ zai rage tsadar bin ƙa’idoji, ya sauƙaƙa samun kuɗin waje, da hanzarta mu’amalolin ƙetare ƙasa, wanda zai taimaka wa kasuwanci, iyalai, da bunƙasar tattalin arziki.

Cardoso ya ce kasancewar Nijeriya a jerin ƙasashen da EU ɗora wa karan-tsanar yin hada-hadar kuɗaɗen, ya jawo asarar sama da dala biliyan 30 a jarin da ka iya shigowa ƙasa.

Ya ce, ficewa daga jerin na nuna dawo da amincewar duniya da rage cikas ga bankunan hulɗa.

Rahoton Bankin Duniya na Global Economic Prospects ya ɗaga hasashen bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya a 2026 zuwa kashi 4.4 cikin 100. Rahoton ya ce wannan bunƙasa za ta samu ne sakamakon gyare-gyaren tattalin arziƙi, ingantacciyar manufofin kuɗi, da ƙaruwa a ayyukan hidimomi, noma da masana’antu.

CBN ma ta bayyana cewa shekarar 2026 na ba da dama ta musamman ga daidaita tattalin arziƙi, inda ake sa ran bunƙasa da kashi 4.49 cikin 100 bisa ci gaba da gyare-gyare da sauƙaƙa manufofin kuɗi.

* Ashafa Barkiya ɗan jarida ne mai zaman kan sa, wanda ke nazari kan tattalin arziƙi da matsalolin tsaro

Previous Post

Sojoji sun yi galaba kan ’yan ta’adda tare da ƙwato dabbobi 529 a Katsina

Next Post

IPOB ta soki gargaɗin ɗan majalisar Amurka kan rugujewar Nijeriya, ta ƙi amincewa da cewa haɗin ƙasa ne ke tabbatar da tsaron Kiristoci

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
IPOB ta soki gargaɗin ɗan majalisar Amurka kan rugujewar Nijeriya, ta ƙi amincewa da cewa haɗin ƙasa ne ke tabbatar da tsaron Kiristoci

IPOB ta soki gargaɗin ɗan majalisar Amurka kan rugujewar Nijeriya, ta ƙi amincewa da cewa haɗin ƙasa ne ke tabbatar da tsaron Kiristoci

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!