• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Tinubu ya umurci jami’an tsaro su gano ‘yan ta’addar da suka yi kisan gilla a Kasuwar Daji

ALI KANO by ALI KANO
January 4, 2026
in Tsaro
A A
0
Tinubu ya umurci jami’an tsaro su gano ‘yan ta’addar da suka yi kisan gilla a Kasuwar Daji
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umurni Ministan Tsaro, Babban Hafsan Tsaro, Hafsoshin Rundunonin Soja, Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, da Darakta-Janar na DSS da su farauto ’yan ta’addan da ke da alhakin harin Kasuwar Daji tare da tabbatar da an gurfanar da su a gaban shari’a cikin gaggawa.

Idan kin tuna, ‘yan ta’adda sun ɗaure hannayen mutane 37 a baya sannan suka yanka su a Kasuwar Daji kusa da Papiri, a Jihar Neja, yayin da aka kashe wasu biyar a ƙauyen Kaima.

Wata majiya ta ce: “Sun kuma sace mutane da dama, ciki har da yara, wasu daga cikin su ɗalibai ne na Makarantun Katolika masu zaman kan su na Firamare da Sakandaren St. Mary’s da ke Papiri, a Ƙaramar Hukumar Agwara.

A cikin sanarwar da ya rattaba wa hannu a wannan Lahadin, Shugaban Ƙasa ya ce: “Waɗannan ’yan ta’adda sun latsa juriyar ƙasar mu da al’ummar ta. Dole ne su fuskanci cikakken sakamakon laifukan da suka aikata.

“Ko su wanene ko menene manufar su, dole ne a farauto su. Bugu da ƙari, duk wanda ya taimaka musu, ya goyi bayan su, ko ya ba su dama, shi ma za a hukunta shi bisa doka.”

Tinubu ya kuma bayar da umarnin a gaggauta ceto dukkan mutanen da aka sace, tare da ƙarfafa ayyukan tsaro a yankunan da ke cikin haɗari, musamman a kusa da dazuzzuka.

Ya ce: “Wannan lokaci na buƙatar mu nuna jinƙai. Dole ne mu tsaya tare a matsayin al’umma guda, mu fuskanci waɗannan miyagun halittu tare. Idan mun haɗa kai, za mu iya kuma dole ne mu kayar da su, tare da hana su samun mafaka ko’ina.

“Dole ne mu dawo da zaman lafiya ga al’ummomin da aka kai wa hari.

“Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu.”

Tags: 'yan ta'addaBola Ahmed TinubuKasuwar Daji
Previous Post

Sojin sama sun kashe ‘yan bindiga 23 da ke ƙoƙarin tserewa bayan sun kai hari a Kano

Next Post

Sarkin Kano Sanusi ya jinjina wa CBN, ya ce Nijeriya ta tsallake siraɗin rugujewar rattalin arziki

Related Posts

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano
Tsaro

EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano

November 17, 2026
Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi
Tsaro

Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi

November 6, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci bincike kan bidiyon atisayen muzaharar Izala
Tsaro

’Yan sanda sun kama matashin Izala kan bidiyon da ke tunzura rikicin addini

October 27, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

’Yan sanda a Katsina sun tabbatar da kashe Sheikh Yahaya Masussuka da abokin sa

October 26, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka

October 26, 2026
Next Post
Sarkin Kano Sanusi ya jinjina wa CBN, ya ce Nijeriya ta tsallake siraɗin rugujewar rattalin arziki

Sarkin Kano Sanusi ya jinjina wa CBN, ya ce Nijeriya ta tsallake siraɗin rugujewar rattalin arziki

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!