Ministan Kuɗi da Daidaita Tattalin Arziki, Mista Wale Edun, ya ce Nijeriya tana nan daram a kan hanyar samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaban tattalin arziki duk da ayyukan tsaro da aka gudanar kwanan nan a ƙasar nan.
Edun ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a yau, bayan tambayoyi da aka riƙa yi sakamakon aikin haɗin gwiwar tsaro na musamman da Nijeriya da Amurka suka gudanar a Sakkwato a ranar Kirsimeti.
Ya ce: “Ina so in tabbatar wa masu zuba jari, masana tattalin arziki da abokan hulɗar mu na ƙasa da ƙasa cewa Nijeriya ba ta yaƙi da kan ta, kuma ba ta yaƙi da kowace ƙasa ba.
“Abin da Nijeriya take fuskanta kai tsaye—tare da amintattun abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa—shi ne ta’addanci. Wannan bambanci yana da matuƙar muhimmanci, kuma shi ne ginshiƙi wajen fahimtar kyakkyawan tasirin tattalin arziki na matakan da aka ɗauka kwanan nan.”
A cewar sa, aikin tsaron da aka yi ya kasance “na musamman, bisa sahihan bayanan sirri, kuma an mayar da hankali ne kacokam kan ’yan ta’adda da ke barazana ga rayukan fararen hula, kwanciyar hankalin ƙasa da ayyukan tattalin arziki.”
Ya ƙara da cewa: “Maimakon tayar da kasuwanni ko rage amincewa, irin waɗannan matakai na ƙarfafa tushen zaman lafiya, kare al’ummomin da ke samar da arziki, tare da ƙarfafa yanayin da ake buƙata domin samun cigaba mai ɗorewa.”
Ya kuma ce, “Tsaro da kwanciyar hankalin tattalin arziki ba sa rabuwa; duk wani ƙoƙari na kare ’yan Nijeriya, a zahiri, yana tallafa wa bunƙasar tattalin arziki da jawo zuba jari.”
Edun ya nuna cewa a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Nijeriya ta samu gagarumin cigaba na gaske a ɓangaren tsaro da gyaran tattalin arziki.
Ya ce: “Waɗannan nasarori sun bayyana ƙarara a cikin yadda tattalin arzikin mu yake tafiya.”
Da yake ƙarin bayani, ministan ya ce: “A zangon uku na shekarar 2025, Nijeriya ta samu bunƙasar GDP kashi 3.98 cikin ɗari, bayan samun bunƙasa mai ƙarfi ta kashi 4.23 cikin ɗari a zango na biyu.”
“Muna sa ran samun ƙarin bunƙasa a zango na huɗu na 2025. Hauhawar farashi ta ragu karo na bakwai a jere, kuma yanzu tana ƙasa da kashi 15 cikin ɗari, abin da ke nuna ingantuwar daidaiton farashi da tasirin matakan kuɗi da na kasafin kuɗi da aka daidaita.”
“Kasuwannin kuɗin mu suna nan da ƙarfi. Kasuwannin basussukan cikin gida da na ƙasa da ƙasa suna da kwanciyar hankali kuma suna aiki yadda ya kamata, sakamakon kulawa mai kyau kan harkokin kuɗi.
“A shekarar da ta gabata, Nijeriya ta samu ƙarin darajar kimantawa daga Moody’s, Fitch, da Standard & Poor’s—shaida mai zaman kan ta da ke nuna ƙarfin su gyare-gyaren mu da sahihancin alƙiblar tattalin arzikin mu.”
“Mun kiyaye ladabin kashe kuɗi, mun fifita inganci, tare da kare daidaiton tattalin arziki—abin da ke nuna juriyar ƙasa duk da ƙalubalen da ke zuwa daga waje.”
Edun ya ci gaba da cewa: “Kamar yadda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a jawabin da ya gabatar a makon jiya, babban burin mu a 2026 shi ne ƙarfafa nasarorin 2025, ƙara juriyar tattalin arzikin Nijeriya, tare da ci gaba da gina tattalin arziki mai ɗorewa, mai shigar da kowa, kuma mai bunƙasa.
“Matakan da muke ɗauka a yau—na tsaro, gyare-gyare da ladabin kashe kuɗi—duk suna tafiya daidai da wannan buri.”
Ya ƙara da cewa: “Yayin da kasuwanni za su buɗe a ranar Litinin, 29 ga Disamba, 2025, masu zuba jari za su iya samun tabbacin cewa Nijeriya tana nan mai mayar da hankali, mai tafiya da gyare-gyare, kuma mai jajircewa wajen tabbatar da kwanciyar hankali.
“Tushen tattalin arziki yana ƙara ƙarfi, alƙiblar manufofi a bayyane take, kuma kudirin wannan gwamnati—na kare rayuka, tabbatar da wadata, da bunƙasa tattalin arziki—ba ya ja da baya.”
A ƙarshe, Edun ya jaddada cewa Nijeriya “a buɗe take ga kasuwanci, tana jingine a kan zaman lafiya, kuma tana maida hankali sosai kan gaba.”







