Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana sunayen kamfanonin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje 82 da ya bai wa lasisin amincewa su yi hadahadar canji, daga ranar 27 ga Nuwamba, 2025.
Cikin wata sanarwar da Daraktar Riƙo ta Sashen Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai, Hajiya Hakama Ali, ta sa wa hannu a ranar Litinin, ta gargaɗi jama’a su guji hulɗa da ‘yan canjin da ba su da lasisi daga CBN.
Bankin ya ce an fito da waɗannan sabbin ƙa’idoji ne a ƙarƙashin Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Hadahadar Kuɗi ta 2025, wato Banks and Other Financial Institutions Act (BOFIA), 2020, tare Ƙa’idojin Kula da Masu Harkar Canjin Kuɗaɗen Waje na Nijeriya ta 2024, wato ‘Regulatory and Supervisory Guidelines for Bureaux De Change Operations in Nigeria’ 2024.
CBN ya tabbatar da hakan ne a wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, mai ɗauke da sa hannun Hakama Sidi Ali, Daraktar Riƙo a Sashen Sadarwa ta bankin.
Sanarwar na ɗauke da cewa, kamfanonin canji wato DBC da aka lissafa a shafin yanar gizon CBN kaɗai ne aka amince su fara aiki daga ranar da aka ƙayyade ɗin.
Bankin ya ce zai ci gaba da sabunta jerin BDC ɗin, wato ‘Bureau de Change’ masu sahihin lasisi, domin jama’a su riƙa tantancewa.
Daga nan sai sanarwar ta yi gargaɗin cewa a guji hulɗa da masu musayar kuɗi da ba su da lasisi.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa, “Don kauce wa ruɗani, gudanar da kasuwancin Bureau De Change ba tare da lasisi ba, laifi ne a ƙarƙashin Sashe na 57(1) na BOFIA 2020. Don haka jama’a su kula kuma su bi doka.”
Idan za a iya tunawa, cikin watan Mayun shekarar da ta gabata, CBN ta soke dukkan tsofaffin lasisin nasu canjin kuɗi, tare da umartar cewa su sake neman sabbin lasisi.
An umarce su da su nemi lasisi na ɗaya daga cikin rukuni biyu:
Babban Lasisi: Wannan sai mai babban jari na aƙalla Naira biliyan biliyan biyu, abin da ya yi sama.
Ƙaramin Lasisi: Wannan kuma ana buƙatar babban jari na Naira miliyan500 abin da ya yi sama.
CBN ya ce an ba kowane BDC waadin watanni shida daga ranar sakin ƙa’idojin, domin su cika sharuɗɗan neman lasisi.
A watan Fabrairu 2024, Bankin ya fitar da ƙa’idoji don neman shawarwarin masu ruwa da tsaki.
CBN ya bayyana cewa bayan kammala tattaunawar, ya fitar da ƙa’idojin kula da ayyukan masu canji na 2024, waɗanda duk masu gudanarwa da masu neman kafa BDC a Nijeriya dole ne su tabbatar sun cika kuma suna aiki da su.
CBN ya ce masu babban lasisi za su iya aiki a kowace jiha da da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Sunayen Kamfanonin Canjin Kuɗi 82 Da Babban Bankin Nijeriya (CBN) Ya Bai Wa Lasisi:
BABBAN LASISI (TIER 1)
1. DULA GLOBAL BDC LTD
2. TRURATE GLOBAL BDC LTD
ƘARAMIN LASISI (TIER 2)
1 ABBUFX BDC LTD
2 ACHA GLOBAL BDC LTD
3 ARCTANGENT SWIFT BDC LTD
4 ASCENDANT BDC LTD
5 BARACAI BDC LTD
6 BERGPOINT BDC LTD
7 BRAVO MODEL BDC LTD
8 BRIMESTONE BDC LTD
9 BROWNSTON BDC LTD
10 BUZZWALLET BDC LTD
11 CASHCODE BDC LTD
12 CHATTERED BDC LTD
13 CHRONICLES BDC LTD
14 COOL FOREX BDC LTD
15 CORPORATE EXCHANGE BDC LTD
16 COURTESY CURRENCY BDC LTD
17 DANYARO BDC LTD
18 DASHAD BDC LTD
19 DEVAL BDC LTD
20 DFS BDC LTD
21 EASY CASH BDC LTD
22 ELELEM BDC LTD
23 E-LIOYDS BDC LTD
24 ELOGOZ BDC LTD
25 ENOUF BDC LTD
26 EVER JOJ GOLD BDC LTD
27 EXCEL RIJIYA FOREX BDC LTD
28 FABFOREX BDC LTD
29 FELLOM BDC LTD
30 FINE BDC LTD
31 FOMAT BDC LTD
32 GENELO BDC LTD
33 GENTLE BREEZE BDC LTD
34 GRACEFUL GLORY AND HUMILITY BDC LTD
35 GREENGATE BDC LTD
36 GREENVAULT BDC LTD
37 HAZON CAPITAL BDC LTD
38 HIGH-POINT BDC LTD
39 I & I EXCHANGE BDC LTD
40 IBN MARYAM BDC LTD
41 JOURNEY WELL BDC LTD
42 KEEPERS BDC LTD
43 KHADHOUSE SOLUTIONS BDC LTD
44 KIMMELFX BDC LTD
45 KINGSOFT ATLANTIC BDC LTD
46 M.S. ALHERI BDC LTD
47 MASTERS BDC LTD
48 MCMENA BDC LTD
49 MKOO BDC LT
50 MKS BDC LTD
51 MR J GOLF BDC LTD
52 MUSDIQ BDC LTD
53 MZ FOREX BDC LTD
54 NEJJ BDC LTD LTD
55 NETVALUE BDC LTD
56 NEW WAVE BDC LTD
57 NOTABLE AND KINGSTON BDC LTD
58 PILCROW BDC LTD
59 RAPID BDC LTD
60 RIGHTWAY BDC LTD
61 RWANDA BDC LTD
62 SABLES BDC LTD
63 SAFETRANZ BDC LTD
64 SAMFIK BDC LTD
65 SEVENLOCKS BDC LTD
66 SHAPEARL BDC LTD
67 SIMTEX BDC LTD
68 SOLID WHITE BDC LTD
69 ST. NICHOLAS GLOBAL BDC LTD
70 TOPFIRST UNIQUE MULTICHOICE BDC LTD
71 TOPGATE BDC LTD
72 TRAVELLER’S CHOICE BDC LTD
73 TUCA GLOBAL BDC LTD
74 TURBOVA BDC LTD
75 TURN-UP BDC LTD
76 UNIGO BDC LTD
77 VICTORY AHEAD BDC LTD
78 WHITEWAY WWW BDC LTD
79 YUND GLOBAL LINK BDC LTD
80 ZAMAD FOREX BDC LTD







