Sojojin Operation Mesa na Birged ta 3, tare da goyon bayan rundunar sojan sama da ’yan sanda, sun ceto mutane bakwai da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙauyen ‘Yankamaye Cikin Gari na Ƙaramar Hukumar Tsanyawa a Jihar Kano.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na Birged ta 3, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya fitar, an bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na dare a ranar 29 ga Nuwamba, 2025, lokacin da rundunar ta samu kiraye-kirayen gaggawa kan harin ’yan bindiga a yankin.
Sanarwar ta ce sojojin sun isa wurin cikin gaggawa, inda suka yi artabu da ’yan bindigar, suka kuma samu nasarar ceto waɗanda aka sace.
Sojojin sun bi sawun ’yan bindigar zuwa hanyar Rimaye, inda suka buɗe masu wuta tare da ƙoƙarin daƙile harin.
Sanarwar ta ce ’yan bindigar sun tsere zuwa yankin Kankiya a Jihar Katsina, kuma jami’an tsaro na ci gaba da bincike domin gano inda suke.
Kwamandan Birged ta 3 ya yaba da ƙwazon sojojin da yadda suka ɗauki mataki cikin gaggawa.
Ya kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da ba jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai da za su taimaka a ayyukan kare rayuka da dukiyoyin jama’a.






